Kafin mutum ya yanke shawarar yin aure ya kamata ya bi matakai guda uku.
1. Ya yi istikharah wato neman zaɓi daga wajen Allah , ya yi sallah raka'a biyu, kamar yadda ya zo a hadisin Jabir ɗan Abdullahi daga riwayar Bukhari 1166, bayan ya yi sallama (wasu malamai suna ganin za a iya yin wannan addu'a kafin sallama, kamar shekhul Islam Ibn Taimiyya ) sai ya ƙaranta wannan addu'a ta neman zaɓi daga Allah.
Marubuci: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
2. Ya nemi shawara daga masana addini da ɗabi'u da halayya, da gogayya da harkokin aure, domin su ba shi shawara bayan sun saurare shi sun ji irin tasa buƙatar, wanda yake shawara ba zai yi nadama ba.
3. Dole mai neman aure mace ko namiji su cire son zuciya idan su na neman aure na gari, duk da shari'a ba ta yarda mutum ya auri matar da ba ya so ba, amma mafi yawan mata na gari ba su fiye kyau da yawa ba, don haka idan an sami mace mai kyau amma ba ta da tarbiyya, da mai addini da tarbiyya amma tana da ƙarancin kyau sai ka ga an raba hankalin mai neman aure.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ana auran mace saboda abu huɗu, saboda kyawunta ko kuɗinta ko matsayin ta ko addininta, ka rabauta da mai addini, idan ka ƙi hannun ka ya yi turɓaya. Bukhari 5090. Daga Abu Hurairah (R.A)
Waɗannan abubuwa guda huɗu su ne mafi yawan masu neman aure suka fi buƙata ga mace, amma ana samun wata ta haɗa dukkan waɗannan siffofin, wata kuma ta samu uku daga ciki, wata ta samu biyu wata siffa ɗaya kawai take da ita daga cikin waɗannan siffofin.
Wacce ta fi ita ce wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin;
1). Mai kyau, mai kuɗi, mai matsayi, mai addini dukkan huɗun tana da shi.
2). Mai addini da kyau.
3). Mai matsayi da kuɗi amma babu kyau babu addini.
4). Mai addini amma babu kuɗi.
5). Kyakkyawa amma babu tarbiyya ta addini.
6). Mace tana da siffofi guda biyu na fili kamar kyau da muni ko baƙi da fari ko tsawo da gajarta, a kwai kuma siffofi na ɓoye kamar kirki da haƙuri da tarbiyya da juriya da iya zaman aure.
Mafi yawan mutane sun fi son mace mai kyau, wannan kuwa ba laifi ba ne, amma idan mutum ya auri mace saboda kyawun ta kawai, lokacin da kyawun ya tafi, sai ka ga mace tana samun canji daga mijinta, saboda abinda ake son ta saboda shi ya tafi ko ya ƙare, kuma mace mai kyau kawai babu tarbiyya sun fi wahalar da mazan su da halakar da su, domin za su dinga yin abinda bai kamata ba. A wasu lokuta domin su faranta musu ko da hakan ya saɓawa Allah da Manzon sa.
Kowa a cikin masu neman aure daga cikin maza ko mata akwai siffofin na fili da yake sha'awa daga matar da yake so ya aura, ko daga mijin da take so ta aura, kamar fara ko baƙa ko doguwa ko gajeriya, mai ƙiba ko siririya, kyakkyawa ko mummuna, amma shi kyau da muni ya dangana ne da abin da mutum yake so, domin mummuna a wajen wani kyakkyawa ce, kuma kyakkyawa a wajen wani mummuna ce.
Ya tabbata a hadisi daga Maa'ƙalu ɗan yasar ya ce : wani mutum ya zo wajen Manzon Allah (S.A.W), sai ya ce : Na samu wata mata zan aura tana da matsayi kuma mai kyau ce, na iya auran ta? sai ya ce masa a'a, bayan lokaci sai ya dawo ya kuma yin wannan tambaya ya ƙara ce masa a'a, a karo na uku sai ya ce masa : Ku auri mai iya soyayya, mai haihuwa, domin zan yawaici al'umma da ku. Abu Dauda 2050. Nasaiy 3227. Silsila Na Albaniy. 2373.
Wannan hadisi ya zo da ƙarin siffofi guda biyu su ne soyayya da haihuwa, yaya za a yi zaman soyayya, kuma a haifi 'ya'ya a yi musu kyakkyawan reno, don haka muna iya ƙara waɗannan siffofi akan na farko su zama siffofi shida.
Akwai wani hadisi ya zo daga Abdullahi ɗan Amri, ya ce : Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Duniya wani jin daɗi ce, mafi jin daɗin duniya shi ne samun mace ta gari, Muslim ya ruwaito.
Sai aka fassara mace ta gari a wata riwayar da Tirmiziy ya ruwaito da siffofi guda biyar, wacce idan ka kalle ta za ta faranta maka rai, idan ka ba ta umarni za ta yi maka biyayya, idan ka yi mata rantsuwa ko kashedi ba za ta saɓa maka ba, idan ba kanan ko ka yi tafiya za ta kiyaye maka dukiyar ka da mutuncin ta.
Idan muka kalli waɗannan hadisai guda uku za mu ga sun zo da siffofi guda goma sha ɗaya kenan.
Su ne:
1). Mai Addini.
2). Mai kuɗi.
3). Mai kyau.
4). Mai matsayi.
5). Mai soyayya.
6). Mai haihuwa
7). Mai faranta rai.
8). Mai biyayya.
9). Mai ɗaukar tsawa da kashedi.
10). Mai kiyaye dukiya.
11). Mai kiyaye mutuncin ta.
Daga waɗanan hadisai na Manzon Allah (S.A.W) muka samo waɗanan siffofin na irin matar da ya kamata mutum ya nema, amma da wuya a sami wacce ta haɗa dukkan waɗannan siffofin.
Mace mai tarbiyya dai ita ce abin nema, idan ka samu mai tarbiyya ka gama more aure.