An haifi Jackie Chan a Hongkong a ran 7 ga watan Afril na shekarar 1954 (Yanzu Yanada Shekaru 70). Ɗan wasan kwaikwayo, darekta, marubuci, furodusa, mai fasaha. Iyayensa, Charles Chan da Lee-lee Chan sun raɗa masa sunan Chan Kong-sang, wato sunansa na yanka, wanda ke da ma'anar "an haife shi a Hongkong". Lokacin da aka haife shi, Jackie na da nauyin pound 12, shi ya sa ba yadda za a yi sai a yi wa mahaifiyarsa tiyata.
Marubuci: Saliadeen Sicey
A lokacin da yake ƙarami, mahaifinsa ya kan tashe shi da sassafe, kuma tare za su yi wasan Kung fu. Sabo da a ganin mahaifinsa, wasan Kungfu na iya taimakawa wajen raya halayensa da kuma koya masa haƙuri da ƙarfi da kuma bajimta.
A lokacin da yake da shekaru 7 da haihuwa, mahaifinsa, Charles Chan ya kama aikin kuku da ofishin jakadancin Amurka a Australia, amma yana ganin cewa, ya fi kyau Jackie ya koyi wani abu a Hongkong, shi ya sa ya bar shi a Hongkong, don ya shiga kwalejin koyon wasan kwaikwayon ƙasar Sin, inda Jackie ya yi shekaru 10 yana koyon wasan Kungfu da kundumbala da waƙa da kuma wasan kwaikwayo.
A lokacin da yake da shekaru 17 da haihuwa, Jackie ya gama karatu a kwalejin koyon wasan kwaikwayo ta ƙasar Sin. Amma a lokacin, wasannin kwaikwayo na ƙasar Sin ba su samu karɓuwa sosai ba, shi ya sa Jackie da abokan karatunsa sun sha wahalar samun aikin yi, sai dai kawai suka kama ayyukan ƙwadago da kasada. A lokacin, Hongkong na fitar da ɗimbin fina-finai a kowace shekara, kuma kullum ana buƙatar samari masu aikin kasada, ga shi kuma Jackie ya kasance mutum mai kuzari da ƙarfi da kuma hikima, shi ya sa ba da jimawa ba sai ya yi suna sabo da rashin tsoronsa a wajen ayyukan kasada.
Daga bisani, Jackie ya yi shekaru da dama yana aikin kasada. Amma ayyukan fina-finai sun fara taɓarɓarewa a Hongkong, shi ya sa ba yadda zai yi sai ya ƙaura zuwa Australia domin zama tare da iyayensa. A lokacin da yake Australia, Jackie ya taɓa aiki cikin wani ɗakin cin abinci da kuma wurin gine-gine, kuma a can wurin ne ya sami sunan "Jackie". Wani ma'aikacin wurin ya sa masa wannan suna sabo da bai iya faɗar ainihin sunansa ba, wato "Kong-sang" sosai ba, kuma ya fara kiransa da "little Jack", wanda daga baya ya zama "Jackie".
Amma Jackie bai sami jin daɗi ba a Australia. Ayyukan gine-gine na da wahala, kuma halin bai kyautata ba sai bayan da wani mutum mai suna Willie Chan ya buga masa waya. Willie Chan yana ayyukan fina-finai a Hongkong, kuma a lokacin, yana neman wani da ya taka rawa cikin wani fim da wani shahararren darektan fim na Hongkong ke yi.
Ayyukan kasada da Jackie ya taɓa yi sun burge Willie sosai. Ba da jimawa ba, Jackie ya kama hanyar komawa Hongkong. Amma duk da haka, fina-finan da Jackie ya yi ba su sami nasara sosai ba, kuma dalili shi ne Jackie bai yi amfani da basirar da Allah ya ba shi yadda ya kamata ba. Har zuwa lokacin da ya nuna ra'ayoyinsa cikin fina-finai, wato haɗa abubuwa masu ban dariya a cikin fina-finai na Kungfu, sai ya zama wani babban tauraron fim.
Fim mai taken "Snake in Eagle's Shadow" ya zama babbar nasara ta farko da ya samu, daga baya, akwai "Drunken Master" da "Fearless Hyena", waɗanda dukansu suka sami farin jini sosai, waɗanda kuma suka sa Jackie ya samu karɓuwa sosai a nahiyar Asiya. Amma duk da nasarorin da ya samu a Asiya, Jackie bai yi fice sosai ba a farkon zuwansa a Hollywood. Shi ya sa ya bar Amurka, kuma ya maida hankalinsa a kan yin fina-finai a Hongkong.
Bayan kimanin shekaru 10, Jackie ya sake zuwa Hollywood, inda ya fitar da fim mai suna "Rumble in the Bronx", wanda ya tabbatar da matsayinsa a zukatan masu kallon fim na Amurka. Daga baya, Rush Hour da Shanghai Noon dukansu sun saka Jackie cikin jerin sunayen taurari na Hollywood.
A cikin 1982, Chan ya auri Joan Lin, 'yar wasan kwaikwayo ta Taiwan. Sun haifi ɗansu da ya zama mawaƙi kuma ɗan wasan kwaikwayo Jaycee Chan. Jackie Chan kuma yana da 'yar da aka haifa a ranar 18 ga Janairun 1999 sakamakon ƙarin aure da Elaine Ng Yi-Lei. Chan ya yarda cewa "ya aikata laifin da yawancin maza a duniya suke aikatawa". Duk da haka, Elaine ta yanke shawarar cewa za ta kula da 'yarta ba tare da Chan ba.
A shekara ta 2004, masanin fina-finai Andrew Willis ya bayyana cewa Chan wataƙila shi ne "tauraron fina-finai da aka fi sani a duniya." A cikin 2015, Mujallar Forbes ya ƙiyasta ƙimar kudin sa ta kai dala miliyan 350, kuma a cikin 2016, shi ne ɗan wasan kwaikwayo na biyu mafi girma a duniya. Kuma ya fito a fina-finai sama da 150.
Ban da fina-finai, a cikin 'yan shekarun baya, Jackie yana ta ƙara maida hankali a kan harkokin jin daɗin al'umma. Ya kasance jakadan UNICEF da kuma UNAIDS, kuma ya yi lokuta da yawa yana tare da yara da kuma waɗanda ke buƙatar taimakon sauran jama'a.
Chan ɗan addinin Buddah ne, amma baya son magana aka imaninsa.