Saturday 14 September 2024

Karanta Zafafan Kalaman Hikimomin Magabata Na Musamman Masu Dadin Gaske

Tura Wannan Zuwa Ga
Ba kowanne wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowanne mai ilimi ne yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin da kake cikin sa sai ya zama kana da haske a kan haske. Idan kuma kana da wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka ƙara sani, sannan ne wayewarka za ta amfane ka.

Zafafan Kalaman Hikimomin Magabata Na Musamman Masu Dadin Gaske
Hoto: LinkedIn

Marubuci: Dr. Mansur Sokoto


Sarakunan da su ka yi mulkin duniya duk sun tafi ba su san wutar lantarki ba. Ba su sha ruwan firijin ba, balle su kunna fanka ko AC. Ba su hau keke ba, ballantana motoci da jirage. Ba su san abin da ake kira tarho ba ballantana wayar tafi-da-gidanka.


Duk hasken gidajensu a wancan lokaci bai wuce na kyandur da fitila mai amfani da kalanzir ba.

A yau kai sarki ne amma ba ka gamsu da abin da ka samu ba. Idan kana da mota ta maƙwabcinka kake kallo. Idan kana da gida na wani babban mutum kake kallo. Oh! Allah sarki. Ɗan Adam da buri yake mutuwa.

Sufanci na gaskiya ababe biyar ne: 1. Riƙo da Alkur'ani da Sunna 2. Kauce ma cin haram 3. Yin tuba ga Allah 4. Rashin cuta ma mutane 5. Bai wa kowa haƙƙinsa. - Sahl bin Abdillah At Tustaree.

Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa wata rana ruwan sama ne zai nuna maka. Shuka alheri ka wuce a can gaba za ka tsince shi.

Hattara da hawaye guda uku: Hawayen iyaye, da hawayen maraya, da hawayen wanda ka zalunta. Kowanen su hawayensa na iya nutsar da kai a cikin tekun bala'i.

Ɗan Adam na girma ne a matakai biyar: Zai fitar da haƙora idan ya kai shekaru bakwai, idan ya ƙara bakwai zai balaga, bayan wasu bakwai tsawonsa zai kammala, idan ya ƙara bakwai ya samu cikar hankali. Bayan haka sai kunne ya girmi kaka (Ma'ana rayuwa za ta karantar da shi abubuwa da dama daga nan har mutuwa ta zo masa). - Al Imam As Thauree.

Hattara da mabuɗai guda uku:
Fushi, mabuɗin azaba.
Tsoro, mabuɗin fitina.
Kwaɗayi, mabuɗin wahala.

Mala'iku su na da hankali ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa ba su da hankali. Ɗan Adam ne Allah ya haɗa masa guda biyun. Idan hankalinka ya rinjayi sha'awarka ka bi sawun mala'iku. Idan sha'awarka ta zarce hankalinka ka shiga sahun dabbobi.

Matakan tsira biyar ne: Sanin Allah, Ƙaunar Allah, Tsoron Allah, Yarda da Allah, sai kuma gudun duniya. - Yahya bin Mu'adh.

Idan an yi maka ƙazafi ka tuna iyalin shugabanmu ma'aiki Sallallahu Alaihi wa Sallam. Kwana hamsin tana cikin sunu da takaici sai da Allah maɗaukaki ya wanke ta.

Allah ya yi mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki ɗaya. Ko ka san dalili? Mahaliccinmu ya fi son mu yi kallo, mu saurara fiye da yadda mu ke magana.

Idan na ƙwarai da mugu su ka haɗu kowa ma yana iya gane bambanci. Amma a tsakanin na ƙwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi, wannan sai ma su hankali ne su ke iya rarrabewa.

Ababe biyar su suka dace da biyar: A samu yaro yana a makaranta, Saurayi wajen neman abinci, Dattijo a masallaci, Mace a gidan aure, Mugu a kurkuku. - Al Hakeem At Tirmidhi.

Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai ya wadata. Ba a sanin gaskiyar ɗan siyasa sai ya kai ga muƙami.

Idan kana jin kaɗaici ka tuna Annabi Adam Alaihis Salam. Ya zauna a duniya shi kaɗai ba kowa.

Idan ka sha wuya a wajen wa'azi da karantarwa ka tuna Annabi Nuhu Alaihis Salam. Shekarunsa dubu ba hamsin yana wa'azi.

Idan 'yan uwanka sun cuce ka ka tuna Annabi Yusuf Alaihis Salam. A cikin rijiya su ka jefa shi.

Idan matsalolin rayuwa sun dabaibaye ka, ka tuna Annabi Yunus Alaihis Salam. Kifi ne ya haɗiye shi amma ya samu kuɓuta a dalilin ambaton Allah.

Matsaloli da wahalhalun rayuwa ba su ne ƙarshen Ɗan Adam ba. Manya ma sun gamu da matsaloli kala-kala.

Abin damuwa shi ne matsalarka ta zama sanadin rabuwar ka da Allah mahaliccinka.

Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. 

Idan ka wadatu daga mutum za ka zama tsaran sa.

Idan kuwa ka buƙatu zuwa ga mutum, to dole sai ka zamo bawansa.

Kyawun hankali ya riƙa tunani.

Kyawun harshe ya riƙa faɗin gaskiya. 

Kyawun Budurwa kunya. 

Kyawun Yaro biyayya.

Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauƙi daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.

Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata ɗaya ba ta isar sa. 

Amma wanda kyakkyawan hali yake so ɗaya ma sai ta ishe shi.

Alheri yana tattare ne a ababe biyar: Wadatar zuci da neman halal da tsoron Allah da kamun kai da barin cuta ma mutane. - Al Imam As Shafi'ie.

Idan ciwo ya addabe ka ka tuna Annabi Ayyub Alaihis Salam. Har sai da ya ji ƙamshin mutuwa a kan cuta.

Masana sun ce, lafiyar Ɗan Adam tana cikin samun ababe guda bakwai:

1. Samun isasshen hasken rana yana bugun jikinka.

2. Yawan shan ruwa (da rana).

3. Wadataccen bacci (da dare).

4. Shaƙar tatacciyar iska.

5. Shan Farar Zuma.

6. Tafiyar minti 30 a kullum da ƙafa.

7. Cin lafiyayyen abinci.

Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori. Wannan shi ne halin mutanen kirki!.

Akwai miliyoyin halittun Ubangiji waɗanda ba su da aljihu, ba asusun ajiya a gida ko a banki amma ba su daina cin arziki ba. Kwantar da hankalinka, arzikinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi Halaliya, don ba ka wuce arzikinka, kuma saurin nema ba ya kawo samu.

Idan mahaifinka na tsanar ka a kan riƙon addini ka tuna Annabi Ibrahim Alaihis Salam. A kan haka ne ya sha wuya a hannun mahaifinsa.

A Hotel ake rubuta "Idan mun burge ka ka faɗa ma duniya. Idan mun ɓata ranka ka faɗa mana". Wannan shi ne yadda ya kamata ka yi hulɗa da kowane Musulmi ɗan uwanka.

Abu ɗaya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa, shi ne kyawun hali. Ka zama mai kyawun hali ba sai ka faɗi ba mutane da kansu za su yabe ka.

Da dare kowa ya na rufe ƙofarsa ne don tsoron mutane. A lokacin ne kuma Allah ya ke buɗe ƙofofinsa don karɓar mutane. Ko kana ƙwanƙwasa ƙofarsa ta hanyar salloli da zikiri da addu'o'i da tilawa a wannan lokaci?

Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka ba to ka yi sadaka daga cikin haƙoranka. Murmushi ga fuskar ɗan uwanka shi ma sadaka ne.

Kada jin daɗin wani ya tsone ma ido, ba ka san abin da ya rasa ba kafin Allah ya ba shi wannan ni'ima da yake cikinta. Kada damuwarka ta tada hankalinka, ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Haƙuri maganin zaman duniya.

Idan ka makara a wajen aiki kana jin kunyar shugabanka. Idan ka makara zuwa masallaci ko kana jin kunyar Allah?

Idan yaro ya yi wayo kyawunsa a sa shi makaranta. Idan ya girma kyawunsa a gan shi a masallaci. Mace ita kuma kimarta idan ta girma tana a gidan mijinta.

Kamilin mutum shi ne wanda ya tara ababe guda uku: Ga kyauta ga daɗin zama ga kuma yawan ibada.

Karatu akwai wuya, ilimi akwai daɗi. Nema akwai wuya, arziki akwai daɗi. Zama da Jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take, yaro ɓata hankalin dare ka yi suna!

Na samu wannan a cikin wani ɗan nazari da nake yi na ga ya dace kada na yi maku rowar sa.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user