Masoyan kafafen sada zumunta, duk wanda ya fahimci canjin ra'ayi daga wurin abokin soyayyar da suka ƙulla da nufin aure, to matakin farko ya warware abotar da suka ƙulla (unfriend), idan duk da haka bai samu nutsuwa a zuciyarsa ba, ya toshe kafar saduwarsu (block).
Marubuci:- Abuna'Ila Saminu
Kada ka taɓa bari yaudara ta saka maka damuwar da za ta shafi lafiyarka, ka fahimci cewa; babu wani ɗan adam ɗin da idan babu shi ba za ka rayu ba, kai kaɗai mahaifiyarka ta haife ka, a duniyar nan kuka haɗu bayan ka gama haɗa hankalinka, na mene ne za ka cusa wa zuciyarka damuwa don ka rasa abin da wataƙila hakan ne ya fi zama alkhairi ga kowannen ku?
Ko tagwaye kuka zo duniya da mutum, dole ne da akwai ranar da za ku rabu, koda kuwa kuna cikin ƙoshin lafiya da lafiyayyen hankalinku, ballantana wanda kafar sada zumunta ce sanadin haɗuwarku.
Wannan fa ina magana ne da waɗanda suka ƙulla soyayyar tasu da nufin raya sunnar Manzo (S.A.W), ba masu kullawa da nufin shashanci ba.