Kasuwanci duniyar makafi ce, masu idanuwa ne kaɗai suke nasara.
Marubuci: Bello Galadanchi
1. Shiri ba komai ba ne.
Aiwatar da abin da ka shirya shi ne komai.
2. Shawara ba komai ba ce.
Shirin gudanar da shawarar da za ta aiwatar da shirinka shi ne komai.
Saboda haka mataki mafi muhimmanci shi ne shiri.
Shiri ne zai sa ka fahimci komai.
Ga misali ɗaya. Idan wani ya ba ka kyautar iPhone 6 guda dubu uku, ta ya za ka yi kasuwanci da su?
Wasu za su ajiye su ne kawai.
Wasu kuma za su fahimci falalar binciken duk masu sayar da wayar, kuma su fahimci yadda ya fi dacewa a yi wa wayoyin farashi, da talla. Wannan ya ƙunshi shawarar ko za a buɗe shago ne a sayar da su daga ciki, ko a gida za a sayar online, ko a Facebook ko groups a WhatsApp za a tallata. A taƙaice, ta ya za a fi samun riba mafi tsoka da kuma ƙarin kwastomomi.
Wannan shiri ne, kuma idan kuka lura, za ku ga cewa ba shiri ba ne, kawai bincike ne da tattaro bayanai masu muhimmanci wato samun idanu ne a cikin duhu.
Nasara a kasuwanci ba ta da tabbatacciyar hanya.
Ka shiga da shirin cewa komai zai iya zama ƙalubale mai saka ciwon kai.