Amincin Allah ya tabbata ga mamallakiyar kyawu na kwatance, wadda miliyoyin mutane suke faɗuwa wajen kallon tsadaddiyar fuskarta, Allah ya sa komai na tafiya daidai a ɓangarenki, ban taɓa faɗa miki wata magana mai muhimmanchi ba wadda ta shafi tarayya ta da ke ba sai yau, ita ce yadda nake tsananin kishin ki.
Marubuci:- Abba Rabi'u
Ina sanar da ke da murya maɗaukakiya cewa ina kishin ki fiye da kishin miji a kan matarsa.
Ki sani ina kallon sauran mata ne a mazaunin maza saboda tsananin son ki da ya yi mini yawa, ke ma ina so ki yi koyi da ni akan hakan.
Kash ina ma a ce zan iya ciro zuciyata da na buɗe miki ita ki ga tsantsar ƙaunarki da ke a cikin ta.
Da a ce ni Mawaƙi ne da na rera ƙasaitattun baitocin bege zuwa gare ki. Ki kasance lafiya.