Sunday 22 September 2024

Sana'o'i 7 Da Za Ku Samu Kudade Sosai Da Su

Tura Wannan Zuwa Ga

Babu shakka, ko masu sana’o’i da kuɗi a halin yanzu hankulansu ba su kwanta ba, kuma kullum zuba idanu suke domin ganin inda kasuwanci ya nufa, da inda aka fi samun alheri, da kuma inda duniya ta dosa baki ɗaya.


Sana'o'i 7 Da Za Ku Samu Kudade Sosai Da Su
Hoto: LinkedIn 

MarubuciBello Galadanchi


Ganin irin halin da masu ƙaramin ƙarfi suka samu kawunansu a ciki yasa na tattaro waɗannan sana’o’in domin mai sha’awa. 


1. SHIGO DA KAYAN ƘASASHEN WAJE DA FITAR DA KAYAN NOMA: Allah Ya albarkaci ƙasashen mu da amfanin gona, a dai-dai lokacin da wasu ƙasashen waje suke buƙatar su.


Za ka iya kawo kayan wuta kamar komfuta, da wayoyin hannu, da kayan sola, da kayan sakawa, da takalma, yayin da kai kuma kake fitar da amfanin gona kamar gyaɗa, wake, shinkafa, doya, man gyaɗa da zogale. 


2. SARRAFA KAYAN ABINCI: Idan kana so ka samu kuɗi, to ka sarrafa kayan abinci kamar gyaɗa, masara, fulawa, kayan ƙamshi, man gyaɗa sannan ka kai kasuwa. 


Akwai riba mai albarka a kayan abinci. 


3. SAYE DA SAYAR DA KAYAN DA AKA YI AMFANI DA SU: Idan aka yi la’akari da halin tattalin arziki da ƙasa ta samu kanta a ciki, za a ga cewa mutane a shirye suke su sayi kayan da aka yi amfani da su idan har ba za su iya sayen sabo ba. Waɗannan kaya kuwa sun kama daga komfuta, wayar hannu, kayan lantarki, motoci, kayan sakawa, kayan gyaran gida da sauransu. 


4. HARKAR MAI GADI DA TSARO: Idan har za ka/ki iya, to mai zai hana ki samu yara masu jini a jiki da ke sha’awar aikin gadi, ki ɗinka musu inifom mai kyau da takalma da huluna, sannan ki samu shago ko wata ‘yar ma’aikata ki tallata su? Akwai ƙalubalen tsaro sosai a al'ummar mu a halin yanzu, saboda haka sana’ar kamfanin gadi na samun arziki a dai-dai wannan lokaci.


5. ƊINKI: Sosai kuwa, har yanzu teloli kuɗi suke samu mai yawa idan har suka iya riƙe kwastoma. To mai zai hana ka fara shagon da yake ɗinkawa, sannan ya sarar da shi ga dillalai? Jama’a sun riga sun fara wannan sana’a kuma kuɗi suke samu.

 

6. BADA SHAWARWARI AKAN NEMAN ILIMI: Saboda matsaloli da muke fuskanta a ɓangaren neman ilimi, mutane da yawa na sha’awar zuwa ƙasashen da suka ci-gaba domin neman ilimi. Idan har ka fahimci yadda ake neman makarantun ƙasashen waje, to ka fara wannan sana’a mana. A shirye mutane suke su biya ka domin ka taimaka musu. 


7. KAMFANIN SAMAR DA AIKI: Akwai mutane masu yawa sosai da ke fuskantar ƙalubalen neman aiki, kuma a dai-dai wannan lokaci, akwai kamfanoni da yawa da ke neman ma’aikatan da suka cancanta domin cike guraben aiki. Za ka iya zama “mai dalilin aiki” ta hanyar haɗa mai neman aiki, da kamfanin dake neman ma’aikata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user