Sunday 1 September 2024

Shawarwari 10 Da Za Su Ginawa Samari Kyakkyawar Makoma

Tura Wannan Zuwa Ga

1. Ɗan shekara talatin (30) ba yaro ba ne, idan kana tsammanin har yanzu kai yaro ne to ka daina, kai saurayi ne da ya gama zangon farko na samartaka; kana mataki na biyu ne yanzu!


 Kyakkyawar Makoma
Hoto: Freerangestock

Marubuci:- Mu'awiyah Ja'afar Hussain


2. Ko ka san cewa ka kusa cika shekaru ashirin (20) da balaga? Idan haka ne, yana nufin kana da lada ko zunubi na kusan shekaru ashirin a rayuwarka.


3. Me ka cim ma a tsawon shekaru ashirin ɗin nan! Ko ka san: 


a. Ilimi: za ka iya kai wa kowanne matakin ilimi a wannan shekarun; boko da addini, haddar ilimummuka da fahimtarsu, ƙwarewa a fannin da kake so!


b. Sana'a, za ka iya ƙwarewa a duk sana'ar da ka sa a gaba, kuma ka haifar da canji mai yawa ta hanyar ƙirƙira da amfanar da wasu cikin al'umma.


c. Manufa: a shekarun nan duk manufar da ka sa a gaba za ka iya cim mata, kuma ka yi fice cikinta tare da gogewa.


4. Ko ka san za ka iya zama uba ko kaka  a wannan lokacin! , idan ka yi aure kana da shekara sha huɗu, ka haihu kana sha biyar, zuwa yanzu 'yarka za ta iya kai wa sha biyar, kuma ta yi aure tana sha huɗu har ta haifa maka jika?


5. A shekarun nan za ka iya gina al'ummarka da abun da Allah ya ba ka na kowacce ƙwarewa da kake da ita, kuma ka kawo canji a kanka da al'ummarka.


6. To ka yi latti, kuma ba ka yi latti ba; ka yi latti idan ba ka ribaci lokacinka ba, ba ka yi latti ba idan ka duba kana da sauran jini a jika.


7. Ko ka san yanzu ne kake cikin ganiyar ƙarfinka da kwarjininka? Idan haka ne, me ka shiryawa rayuwa mai zuwa? Mai kake tunani na jiya da yau da gobe?


8. Ko ka san a yanzu ya kamata ka yi nadamar abun da ya wuce, kuma ka yi tunanin gaba, sannan yanzu da kake karatun nan ya kamata tunaninka ya canza?


9. Ko ka san irinku al'umma take nufi da samari su ne ƙashin bayan al'umma? To shin kai ƙashin ginawa ne ko rushewa?


10. To ka yi wa kanka karatun ta natsu, ka gyara, ka fuskanta, ka yi nadama, ka zauna da na gaba don kada ka faɗa kuskurensu, ka duba na baya don kada ka maimaita me ka aiwatar a lokacin da kake kamarsu!


Allah ya sa mu dace.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user