Darussan rayuwa 10 waɗanda ba za a koyar da kai a makaranta ba, amma rayuwa za ta sanar da kai.
1. Rayuwa ba gasa ba ce.
Kowa ka gani a rayuwa yana da nasa tafarkin da ƙaddarar wacce ta sha bamban da na sauran mutane. Don haka ka bar haɗa kanka da wani, kowa a rayuwa yana da rabonsa.
2. Lafiyarka ta fi komai muhimmanci.
Ba za a karantar da kai wannan a makaranta ba, amma rayuwa za ta karantar da kai da zafi. Ba ka da wata kadara ko mallaki da ya wuce lafiyarka.
Idan rashin lafiya ya kama ka, duk wani abu da kake yi a baya ba za ka iya yin sa ba, don haka ka kula da lafiyarka yadda ya kamata domin lafiyar mutum ita ce jarinsa.
3. Farin ciki daga zuciya yake.
Yawan dukiya, shahara da ɗaukaka, ko jin daɗi duka ba su ke samar da farin ciki ba. Idan kana da wadatar zuci za ka samu farin ciki da kwanciyar hankali wani kuwa duk abin da yake so a rayuwa yana da shi amma duk da haka cikin damuwa yake kwana.
4. Ba kowanne zance a ke tankawa ba.
Idan ka ce za ka tsaya ka jefi duk wani kare da yake haushi a kan hanyarka ba za ka taɓa isa inda kake so ka je ba. Don haka, ba duk abin da aka faɗa ko aka aikata maka za ka tankawa ba.
Wani lokacin shiru shi ne abu mafi dacewa ga wanda yake neman ka da rigima ko faɗa.
5. Ba za ka iya burge kowa ba a rayuwa.
Duk abin da za ka yi wa mutane, sai wasu sun ji haushinka ko sun tsane ka. Ka yi iya ƙoƙarinka don ka zauna da mutane lafiya, amma ka sani duk abin da za ka yi, ba za ka iya burge kowa ba.
Don haka kada ka yi mamaki don wani ya tsane ka ba tare da dalili ba, saboda wasu mutanen a haka ɗabi'arsu take.
6. Lokaci ya fi komai tsada a rayuwa.
Komai yana da lokaci a rayuwa, don haka ka yi komai a lokacinsa. Duk abin da ya kucce/kuɓce maka za ka iya dawo da shi amma banda lokaci. Idan lokaci ya wuce ya wuce kenan har abada.
7. Abokai na gaskiya suna da wuyar samu.
Mutane da yawa sukan gina abokantaka ne akan amfanuwa ko saboda abin duniya.
Idan Allah Ya azurta ka da aboki ko Ya azurta ki da ƙawa mai kyawun hali kuma wanda yake son ka da alheri, ka riƙe sa da kyau. Abokai na gaskiya suna da wahalar samu.
8. Tafiya ta fi mahimmanci bisa ga masauki.
Idan ka cika damuwa da sakamakon da kake nema, za ka iya rasa darussa masu muhimmanci da akan koya a cikin hanya.
Kafin isa ga masauki ko burin da kake nema, akwai doguwar tafiya wacce take ɗauke da tarin darussa kuma muhimmancinta daidai yake da na wannan burin da kake nema.
9. Gazawa ɓangare ne na nasara.
Duk wani mutumin da ya yi nasara ya taɓa faɗuwa a wani mataki na rayuwarsa.
Faɗuwa dama ce da take ƙarfafa azamarka da juriyarka kuma ta karantar da kai abubuwa masu yawa da ba za ka sani ba idan da nasara ta zo gare ka kaitsaye.
10. Tunaninka shi ne kamanninka.
Abin da ka yarda da shi game da kanka da kuma duniyar da ke kewaye da kai su ke hukunta zahirin rayuwarka. Don haka domin canza rayuwarka, dole sai ka fara canza tunaninka.
Waɗannan darussa ne masu muhimmanci amma masu hankali kaɗai kan gane.
Allah Ya ganar da mu!
Tushe/Asali: Hausa Motivation