Saturday, 7 September 2024

Zafafan Shawarwari 10 Ga Matasa Don Gina Kyakkyawar Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya kai matashi mai shekaru sha takwas (18) zuwa ashirin da biyar (25), saurara ka ji ni!


 Shawarwari 10 Ga Matasa Don Gina Kyakkyawar Rayuwa
Hoto: Javatpoint


Marubuci:- Mu'awiyah Ja'afar Hussain


1. Sunanka matashi, ko ka san me matasantaka take nufi? Lokaci ne na fara nuna farkon ƙarfi da farin cikar gaɓoɓi, sannan farkon shiga matakin samartaka.


2. Ba shakka za ka ga ana yawan rubuta 18+ a kafafe da mujallu da jaridu; to hakan na nufin kai ne abun farauta a wannan lamarin, kai ake so a canzawa rayuwa! Ka san me ya sa? Saboda ku ne manyan gobe, idan har aka samo ku to an samu gada zuwa ga manyan gobe, kuma an samu gadar lalata na ƙasa da ku.


3. Na san zuwa yanzu ka gama sakandare, wataƙila ka shiga jami'a ko kwaleji, to fa ka sani cewa yanzu fa kai ba karabiti ba ne, ka yi firamare, sakandare, yanzu kana mataki na gaba. 


Me kake so ka zama nan da shekaru goma?


4. A yanzu ne sha'awa take fizgarka, kana gani kana daidai da kowa, to ka nutsu ka ji ni; shin yarinyar nan da kake nema za ka iya aurenta?  Shekarunta nawa? Kusan sa'arka ce ko? Kana da ƙanwa kamar ta ko? Shin za ka yarda abokinka ya zo zance wajen wannan ƙanwar taka? Shin ta kai aure kuwa?


To na san amsarka ita ce a'a, to kada ka ɓatawa kanka lokaci.


5. Yayunka na gida da na unguwa da suka haura shekaru 25, na san kun yi wasan yarinta da su, kana ganin kanku ɗaya, to amma dai ka san ba sa'anninka ba ne, to ya rayuwarsu take? Shin kana ganin sun yi abun da ya dace lokacin da suke kamarka? Kada ka ba ni amsa, yi tunani akai.


6. Yauwa, ka duba tsofaffin unguwarku, shin suna da ilimin addini da na boko? Idan suna da shi to tun suna irinka suka nema, idan kuma ba su da shi to tun suna irinka ba su nema ba. Kenan kai kana cikin lokacinka, kuma ba zai jira ka ba.


7. Abokan nan naka, na san ka san akwai waɗanda suke neman mata, neman kuɗi, neman ilimi, amma rayuwar wa ta fi burgeka?  To tun yanzu ka canza tunani.


8. Shekaru uku zuwa biyar baya dai ka san ɗawainiyar ka na kan iyayenka ne ko? Yanzu ma akwai wasu ɗawainiyoyin da suka ɗauke maka ko? To ka sani yanzu suka fara neman taimakonka, nan gaba ba za su maka komai ba, don haka tun wuri ka saba da dogaro da kanka, ka fara taimakonsu.


9. Ka san a cikin matasa akwai dattijai kuwa? Su ne suka kame kansu, suka maida hankali wajen ci-gaban su da al'ummarsu, suka lizimci manyansu don samun hikima da fahimtar gwagwarmayar rayuwa!


Ko ka san shekarun baya ku ne 'yan aike a unguwa? To yanzu babu mai aikenku. Ku ne masu aiken, ku ne masu tarbiyyantar da ƙannanku na unguwarku.


10. Daga ƙarshe, ku ne adireshin danginku, ku ne adireshin unguwarku. Ku ne adireshin addininku, ku ne adireshin al'ummarku; da zaran kun yi ba daidai ba, to kuna wakiltar abun da aka ambata ne, idan kun yi daidai, kuna alamta cewa ku wakilai nagari ne.


Allah ka shiryamu da matsanmu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user