A tsammanin ta bai isa ya zo wurin ba a wannan lokacin, domin su a abin hawa suke, shi kuwa a ƙasa yake. Tana zuwa ta same shi ya haɗa kai da gwiwa yana ta kiran sunanta, "Laila! Ya Laila!! Ya Laila!!!" Ta ƙaraso wurinsa tana mai cewa, "Ya Majnunun Soyayya ga Lailarka ta iso!!". Duwatsun kusa da na nesa suka ɗauki muryarta tana amo.
Marubuci:- Auwal Ilyas Adam
Nan da nan ya zabura zuwa gare ta, yana mai cewa, "Shin da gaske ne Laila ke ce anan?" Ta amsa "Ni ce!" Ya miƙa mata hannu ta riƙe sai suka ji kururuwar mahaifanta suna nemanta domin a ci-gaba da tafiya. Ta juya da hanzari, ya ce, "Haba Laila kada ki tafi ki bar ni da begenki!" Ta ce, "Kar ka damu, idan na dawo za mu haɗu anan."
"Yaushe za ki dawo?" Ya tambaye ta. Ta ce, "Ban san lokacin ba, amma da zarar mun taho zan aika maka." Da haka ta tafi ta bar shi anan. Majnun ya ce a ransa, "idan ta dawo wa za ta aika ya faɗa min? A ina ɗan saƙon zai same ni? Kawai bari na zauna anan ɗin har sai ta dawo." Ya share wuri ya zauna ba shi da wani abinci sai ganyen bishiyar da ke wajen yana shan ruwan da ke ɓuɓɓugowa daga ƙarƙashin dutse. A kullum zancensa shi ne kiran sunan Laila da addu'ar ta dawo ta same shi. A haka har tsiron bishiya ya fito daga 'ya'yan itacen da yake jefarwa, ganyenta ya nannaɗe masa jiki ya zama tamkar bishiyar a jikinsa ta tsiro.
A can garin da su iyayen Laila suka je da ita kuwa, sai wani attajiri ya fito yana son ta da aure. Nan take ya ba wa iyayen raƙuma ɗari gami da wasu kyautuka masu yawa. Da Laila ta ga alamar lallai za a aurar da ita gare shi sai ciwo ya kama ta. Ta yi ta fama, iyayen suka yi nufin komawa gida domin magani alabarshi idan ta warware sai a yi auren. A hanyar su ta dawowa suka sauka a wannan zangon. Duk da tana fama da jinya Laila ta taso zuwa wurin da suka yi alƙawari da Majnun. Ta kusa isa kenan ta gamu da wani mutum ya ce mata, "Yarinya kada ki je wurin nan da kika nufa. Akwai wata fatalwa mai kamar bishiya da ta bayyana."
Kullum tana kiran sunan "Laila, Laila." Da ta ji haka sai ta tabbatar Majnun ne bai tafi ba. Ta ƙarasa wurin da gudu. Yana ganinta ya yi zumbur ya miƙe tsaye yana mai farin ciki, yana cewa "Laila kin cika alƙawari? Laila ke ce kuwa? Laila za ki aure ni??"
Kasancewar ya jima sosai a zaune ba ya miƙewa, sai jiri ya ɗebe shi, a lokaci guda kuma zuciyarsa ta buga saboda tsanannin farin ciki. Kansa ya gwaru da dutse ya faɗi sumamme.
Laila na ganin irin wannan sadaukantarwa ta kasa haƙurcewa, zuciyarta ta raurawa, ƙirjinta ya yi matuƙar ƙunci. Nan take numfashinta ya ɗauke ta faɗi a wajen sumammiya ita ma.
Kays Majnun shi ne ya fara farfaɗowa daga sumar da suka yi gabaɗayansu, ya yunƙura da zummar isa inda Lailan take amma sai ya kasa yunƙurawar saboda ba kuzari a tare da shi, cikin wata murya ma'abociyar raurawa ya ƙwalawa Laila kira "Laila...!" shirun da ya biyo baya shi ne ya tilasta masa fara jan jiki a kwancen, a hankali yana jan jiki har ya ƙarasa inda Lailar take a kwance a sume.
Cikin ruɗewa da firgici Majnun ya ringa kiran sunan Laila ganin ba ta ko alamar motsi, ya ce "Kada ki tafi ki bar Majnuninki a cikin azabtacciyar rayuwar da gwara mutuwa da ita, kin sani cewa Majnun da son ki yake rayuwa Laila..." ya ƙarashe kalaman nasa da wasu daɗaɗan baitoci:
Rabuwa da ke ba daɗi na ji a jikina.
Kar ki bar ni Lailata domin kuwa ke ce jin daɗina...'
Farin ciki ne mara misaltuwa ya bayyana ƙarara a fuskar Majnun dai-dai lokacin da ya ga Laila ta motsa.
A dai-dai lokacin da Lailar ta motsa har ma ta samu ta zauna, kuma a lokacin ne iyayen Lailar suka ƙaraso wajen da suke, iyayen Lailar suka ruɗe ganin yadda suka ga 'yarsu a wani mawuyacin hali.
Suka ɗauki 'yarsu da zummar tafiya da ita wani garin daban wanda yake da nisa daga wannan nahiyar, ''Laila..." Majnun ya ƙwala mata kira da ƙarfi ganin har sun fara yin nisa daga wajen da suka bar shi a kwancen, ƙwala mata kiran da ya yi shi ne ya yi sanadiyar ƙara dakusar da ɗan ragowar kuzarin da ke tare da shi, don haka yana gama ƙwala mata kiran sai ya kuma kifewa a ƙasa sumamme.
DUBA WANNAN: Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (4)
Laila tana ganin hakan sai ta ruɗe, ta kufce daga hannun iyayenta ta rugo izuwa gare shi.
Za mu ci-gaba Insha Allah.