Friday, 11 October 2024

Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (4)

Tura Wannan Zuwa Ga

Lokacin da Laila ta kufce/kuɓce daga hannun mahaifiyarta kaitsaye sai ta ruga izuwa rabin ranta wato Kays Majnun kenan wanda yake kwance a sume sakamakon ƙunci da rashin ƙarfin jiki da ke addabarsa.


Ainihin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila
Hoto: Hamidsamejo

Marubuci:- Auwal Ilyas Adam


Tana isa gare shi sai ta durƙushe tana kuka gami da ambaton sunansa cikin wata murya mai ɗauke da sautin tausayi, shiru Majnun bai ko motsa ba balle ta sa ran zai amsa mata kiran nata, cikin shashsheƙar kuka Laila ta fara rerawa masoyinta wasu baitoci irin na masoya:


"Idaniyata tana ta zubar da ruwan hawaye.


Tafiyata ta zama tamkar ta masu maye.


Ga idanuwana a buɗe har gari ya waye.


Zuciyata ta soye.


Ka taso na gan ka rabin raina........."


Ganin har yanzu masoyin nata bai farfaɗoba sai zuciyarta ta karye, jikinta ya yi sanyi nan take ta faɗi a wajen da kalmar Majnun a bakinta.


A haka iyayen Lailar suka ƙaraso wajen da suke, suka ɗauke ta suka tafi da ita, suka bar Majnun kwance a sume a wajen.


Wata iska ce mai ƙarfin gaske ta ringa kaɗawa a ilahirin dajin da Majnun yake kwance, jim kaɗan da fara iskar kuma sai yanayin garin gabadaya ya canza kala, wanda hakan yake nuna cewa ruwan sama na gaf da sauka. Ruwan saman da ya fara sauka da ƙarfin gaske shi ne ya zamo silar farfaɗowar Majnun daga dogon suman da ya yi, yana farfaɗowa ya fara da kiran Laila!


Da rarrafe da jan jiki Majnun ya samu ya koma jikin bishiyar da yake ƙarƙashin ta dan dai ya tsira daga dukan ruwan saman, wasu zafafan hawaye ne suke sintiri daga ƙwayar idanunsa zuwa kan kumatunsa, gabadaya duniyar ta yi masa zafi gami da duhu, shin a ina zai ga Lailarsa ne? Me ya sa mutane suke masa kallon mahaukaci saboda kawai ya zurfafa a begen masoyiyarsa, me ya sa iyayen Laila ba sa jin tausayinsa ne? 


A haka ya kasance yana ta kuka da sambatu na rashin sanin ina zai ga Lailarsa har ruwan saman ya ɗauke, yana nan zaune sai ga wasu Fatake za su wuce sai suka ga Majnun kamar wani tsohon mahaukaci saboda gabaɗayansa ya canza kamar ba mutum ba. Fataken suka tsaya domin taimaka masa, Majnun ya kwashe labarinsa kaf shi da masoyiyarsa ya labartawa waɗannan fataken, koda fataken nan suka ji wannan labarin nasu sai suka cika da mamaki gami da tausayi, da yawa daga cikinsu suka ringa kuka saboda tsabar tausaya masa.


Majnun ya nemi fataken da su ba shi aron alƙalami da takarda zai rubutawa masoyiyarsa wasiƙa ya ba su su tafi da ita ko Allah zai sa su samu labarinta.


Suka amince da hakan kuma suka ba shi abin rubutu da takarda, ya karɓa ya fara rubutawa masoyiyarsa wasiƙa kamar haka:


"Zuwa ga wacca jin daɗin raina ya rataya a cikin ƙwayar idanunta, ki sani cewa Majnun ɗinki ba zai iya rayuwa ba idan ba da ke ba, zuciyata ta kurumce ba ta ji kuma ba ta gani matuƙar dai ni da ke za mu ci gaba da rayuwa a ware, ina mai baƙin cikin sanar da ke cewa ruhina yana gaf da barin gangar jikina mutuƙar dai na ɗau lokaci ban gan ki a kusa da ni ba Laila! Ki sani ya ke wadda farin cikina yake kai kawo a tare da ke ba zan gusa daga inda kika bar ni ba har sai ajalina ya riskeni a wajen". 


Bayan Majnun ya gama rubuta wasiƙar sai ya matsa can ƙasan wasiƙar ya rubuta wasu baitoci masu tsuma zuciyar duk wanda ya ji su:


"Yaushe ne za mu gana na ji sautin muryarki?


Zuciya sai tai ta kuka idan na duba ban gan ki ba.


A rayuwa idan babu ke ban san ni yaya zan yi ba.


Ina son jin kalamanki, ki ambata su gare ni ko zan samu haiba.


Ina ta kukan rashinki, ki tausaya min ki zo ki duba.


Ni da ke nake alfahari, Laila ki taho gare ni na bar ƙuncin zuciya......"


Fatake suka yi sallama da Majnun, fuskokinsu cike da tausayinsa, kuma suka yi masa alƙawarin Insha'Allahu za su sada wasiƙarsa ga masoyiyar tasa.


Bayan iyayen Laila sun tafi da ita, da suka isa masaukinsu sai aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo, tana farfaɗowa ta fara kuka gami da ambaton sunan Majnun, hankalin iyayenta ya tashi ganin ita ma ta fara bayyana duk wasu alamomi da Majnun ɗin yake nunawa a kanta, wato alamun hauka.


Iyayen Laila suka yanke shawara a kan su nufi can wajen ƙasar Bagadada domin yin ƙaura gabadaya daga yankin da 'yarsu za ta kuma ganin Majnun.


Nan da nan suka haɗa kayansu sai Bagadada, yayinda ita kuma Laila take kwance cikin matsananciyar rashin lafiya.


Kwanci tashi Fataken nan masu ɗauke da wasiƙar Majnun zuwa ga masoyiyarsa suka iso wani wuri wanda nan ne mahadar Fatake, daga wannan mahaɗar zuwa cikin ƙasar Habasha tafiya ce ta rabin kwana, wannan ne ya sa duk waɗanda suka zo da zummar shiga ƙasar Habasha sai sun tsaya a wannan mahaɗar domin kinkintsawa.


Jikin Laila sai ƙara tsananta yake, hakan ne yasa tafiyar tasu ba ta sauri, a hakan su ma suka samu suka iso wannan mahaɗar, a wannan mahaɗar suka yada zango kuma suka duƙufa nemawa 'yarsu magani, suka bada cigiya a wannan mahaɗar ko akwai mai maganin da zai iya warkar da 'yarsu, suka alƙawarta dukiya mai tarin yawa ga duk wanda ya yi nasarar warkar da ita, a shelar da aka yi sai karaf a kunnuwan waɗannan Fataken, wato waɗannan waɗanda suka ba wa Majnun magani, don haka jin an ce za a bada dukiya mai yawa sai suka je suka ce za su gwada warkar da Laila ɗin, yayin da aka kai su inda Lailar take sai aka labarta musu dalilin rashin lafiyartata.


Suna jin haka sai suka gane cewa lallai ita ce wadda Majnun ya labarta musu ita.


Fataken suka nemi da a bar su daga su sai ita a ɗakin domin a cewarsu akwai ma shafar jinni/aljanu a tare da ita, bayan an bar su daga su sai ita, sai suka labarta mata labarin masoyinta Majnun, nan da nan sai ta tashi zaune jin an ambaci Majnun ɗinta, bayan ta gama karanta wasiƙar da Majnun ya aiko mata da ita sai ta fashe da kuka, kuka mai ratsa zuciyar mai sauraro, anan Fataken suka rarrasheta da ƙyar sannan suka kwatanta mata nahiya da kuma wurin da suka baro masoyin nata.


Lokacin da iyayen Laila suka dawo ɗakin sai suka tarar da 'yarsu har ma ta tashi zaune kuma ga fara'a a fuskarta, nan take iyayenta suka nuna farin cikinsu sannan suka kawo dukiya mai tarin yawa suka ba wa Fataken nan kamar yadda suka alƙawarta.


Bayan kwana biyu da samun lafiyar Laila sai iyayenta suka yanke shawarar haɗa kayansu domin shiga cikin ƙasar Habasha, a lokacin da suka gama shirinsu kaf domin fara tafiyar, a lokacin ne kuma Laila ta sulale da taimakon wani mutum da ya sata a hanya kana ya samo mata doki ta bar nahiyar da nufin isa ga masoyinta, masoyinta na gaske wanda take da tabbacin har abada ba za a samu masoyi kamarsa ba.


DUBA CI-GABAN ANAN: Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (5)


Kwanci tashi, ta yada zango anan ta yada zango a can har ta shigo nahiyar da Majnun ɗinta yake, don haka sai ta ƙara ƙaimi domin ta kai ga rabin ran nata, gabaɗaya kamanninta ya sauya, tayi futu-futu da ita, kuma ta rame da ma kuma gashi ba ta daɗe da farfaɗowa daga rashin lafiya ba.


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user