Friday 11 October 2024

Gajeren Sakon Budurwa Na Soyayya Ga Saurayin Ta

Tura Wannan Zuwa Ga

Ina son ka tamkar yadda ba zan iya bayyana maka ba. Ina sonka tamkar yadda ba za ka iya ƙirga adadin ruwan sama ba.


Saƙon Budurwa Na Soyayya Ga Saurayin Ta
Hoto: Dr. Jim Collins

Marubuci:- Abba Rabi'u


Ɗawainiya nake da son ka a cikin zuciyata, da sannu za ka fahimci ni masoyiyarka ce ta haƙiƙa.


Kada ka zubar da hawayenka, yayin da wani ya ɓata maka rai, tuna da wacce kake so, kake kuma ƙauna, sai zuciyarka ta yi fari.


Na zana zanen fulawar so a tafin hannuna na yi nufin nuna maka domin ka fahimci yanayin matsayin da son ka ya yi a cikin zuciyata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user