Ina son ki abar ƙaunata. Na kasance a cikin matsi, na kasa bacci yayin da dare ya tsala, ba ni da komai sai tunanin ki, har wani lokacin gari kan waye ba tare da na rintsa ba.
Saƙon Saurayi Me Ratsa Zuciya Ga Budurwa
Hoto: Candy/Pinterest
Marubuci:- Abba Rabi'u
Na san wannan yana faruwa ne saboda irin tsantsar soyayyar da nake miki a zuciyata.
Shin ko ke ma haka ne?
Tattausan lafazin ki abin kwatantawa ne.
Komai naki daban da na sauran 'yammata.
Da zan kwana ina misalta kyawun halittarki, ba zan iya kai wa ƙarshe ba, koda kuwa zan wanzu ina yi har ƙarshen rayuwata.
Hmm bari dai na tsaya a nan kada ki ce na cika zuba kamar kanyar da ba daɗi................