Mutane suna yawan tambaya, ta yaya mutum zai iya gano baiwarsa har ya sarrafa ta. Wasu a zahirin gaskiya ba su san inda baiwarsu take ba, wasu kuma tun suna ƙanana suka sani. To amma wannan rubutun zai ƙara mana haske ne game da inda baiwar mutum take da yadda zai gano ta, wataƙila rubutu na gaba kuma zai kawo bayanin yadda za a sarrafa ta.
Marubuci:- Muhammad Auwal Ahmad
An yarda Albert Einstein masani ne mai tsantsar fikira da basira, wanda aka ƙara tabbatar da haka bayan sace ƙwaƙwalwarsa da Dr. Thomas Harvey ya yi, sannan ya rarraba ta zuwa ga sauran masana don a yi bincike a kanta. Sakamakon ya nuna cewa Einstein ya fi miliyoyin mutanen duniya da fikirar lissafi da saurin warware wata sarƙaƙiya (problem solving).
Amma shi da kansa Einstein ɗin yake cewa kowa yana da wata baiwa keɓaɓɓiya, amma mutane suna raina kansu ne idan suka kalli wasu. Ya bayar da misali cewa, kifi yana rayuwa a cikin ruwa, shi kuma biri yana rayuwa a tudu — idan aka ce dole sai kifi ya hau bishiya zai ƙare rayuwarsa yana tunanin cewa shi daƙiƙi ne ba zai iya komai ba, ba tare da sanin cewa yana da baiwar linkaya/ninƙaya (swimming) ba.
To haka yawancin mutane suke ɗauka.
Yadda za ka gano baiwarka da kanka: Hanya ta farko
1. Ka nutsu da kyau sannan ka yi duba ga waɗannan ɓangarorin da na kawo a baya da kyau, latsa nan don karantawa, ka ga wanne mutum ne yake matuƙar burge ka a misalan da na kawo.
2. Idan ka samu mai matuƙar burge ka a cikinsu, ka duba a wane ɓangare yake, sannan ka shiga tunani da nazari mai zurfi don sanin cewa shin ka dace da ɓangaren. Idan ba ka ga wanda yake burge ka ba, ka yi bincike a kansa ka gano inda baiwarsa take.
3. Idan ka ji kana son ɓangaren, sai ka yi tunanin shi wanda yake burge ka a ɓangaren wanne abu ya yi, sannan kai kuma yanzu me ya kamata ka yi? Misali idan ƙirƙire-ƙirƙire yake yi, yanzu sai ka yi tunanin yadda kai ma za ka fara kuma me ya kamata ka kirkira?
4. Ina mai tabbatar maka cewa idan a wannan ɓangaren baiwarka take, ba za ka gushe a tunani ba sai ka gano wani abun da ya kamata ka yi.
5. Ka bi shawarar Nikola Tesla da yake cewa a wannan yanayin ka kasance kai ɗaya, ka je gefe inda babu hayaniya babu wanda zai takura maka, wayarka ma ka ajiye ta a gefe.
Yadda za ka gano baiwarka da kanka: Hanya ta biyu
1. Wasu masanan suka ce ka yi tsam da ranka ka gano me ka fi so, me yake burge ka a ɓangarorin da na taɓa kawowa a baya, latsa nan don karantawa, ko kuma wasu daban, shin wanne ɓangare ne yake burge ka?
2. Ka yi yawo a duniya don ganin abubuwan mamaki, ka binciko me ya fi kwanta maka a rai, ina zuciyarka ta fi karkata?
3. Ka fara bincike a ɓangaren da ya fi kwanta maka a rai, sannan ka yi tunanin me ya kamata ka yi?
4. Ka fara aiki da wani abu a zahirance, idan a nan baiwarka take za ka ji kana samun nutsuwa kuma ka fi ganewa da kasancewa a bangaren.
5. Misali, idan baiwar waƙa ce da kai za ka ji ba ka buƙatar sai ka rubuta ta, ko kuma idan lissafi ne za ka ji kana so kai ma ka kawo wani sabon abu.
DUBA WANNAN: Karanta Ire-iren Baiwar Ɗan Adam 14 Masu Ban Mamaki
Muhimman Bayanai guda 7
1. Duk wanda yake da baiwa a wani ɓangare to zai so ɓangaren sosai, kuma zai ji yana burge shi ko kuma waɗanda suke a ɓangaren. Ke nan, wannan hanya ce mai sauƙi ta gane inda kake da baiwa a wajen.
2. Idan ka gano inda baiwarka take kada ka ɓata lokaci wajen yin shawara, kawai ka kutsa ka fara sarrafa ta.
3. Ka tuntubi masu irin baiwarka tare da nuna musu kai ma kana son ɓangaren, su ma za su ji suna sonka, wataƙila akwai shawarwarin da za su ba ka.
4. Wasu lokutan za ka ji kana son abu amma yana ba ka wahala, to a irin wannan yanayin ka sake duba wani ɓangaren ka kwatanta su ka ga wanne ka fi so? Inda ka fi so ɗin shi ne baiwarka, komai wahalarsa.
5. Idan ɓangaren da kake so yana ba ka wahala, ka tuntuɓi masana a ɓangaren wataƙila akwai ingantattun shawarwarin da za su ba ka.
6. Ka yi sani cewa akwai ɗan-na-gada, akwai kuma ɗan-na-koya wato masu naci. Ko ba ka da baiwa a ɓangaren matuƙar ka nace sai ka fi wanda yake da baiwa a wajen.
7. Ka yi haƙuri ka nace, idan tsarin farko bai yi maka aiki ba, ka sake ƙirƙiro wani sabon tsarin, tsayawa a wuri ɗaya hatsari ne in ji kifi.
Fatan alheri!
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.