Thursday, 31 October 2024

Hatsarin Bayyanawa Budurwa Sirrin Komai

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk lokacin da mace ta gama sanin sirrinka kaf raini ne abu na gaba da ke shiga tsakaninku, ba mace ba har ga maza haka ɗabi'ar Ɗan Adam take.


Hatsarin Bayyanawa Budurwa Sirrin Komai
Hoto: Mensxp

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Saurayi ne zai fara soyayya da yarinya kafin wata ɗaya ya cika kowanne sirrinsa sai ta sani, komai na rayuwarsa sai ya gaya mata, wani ma hatta jarinsa da dukkan wani tsari na rayuwarsa sai ya buɗe baki ya gaya mata.


Haba malam ba fa matarka ba ce ko matarka ce ba komai da komai ya kamata ta sani ba, kai ba ka san hakan yana sakawa hatta maƙiyanka su yi galaba a kanka ba ta hanyar fitar da bayananka da sirrikanka da kake yi ga wata baƙuwa wadda ba lallai ta zama matarka ba ma.


Samari da dama su suke ba wa 'yammata damar rainasu da yaudararsu.


Malam mutum kamar wanda aka sakawa hannu zance ratatatata ba ƙafiya, wani saurayin hatta kalar ɗan ƙaramin wandon da yake sakawa sai budurwarsa ta sani, wai kai ba ka la'akari da cewa wannan budurwartaka za ta iya zama babbar maƙiyiyarka har a iya farautar rayuwarka da ita ko kuma nan gaba idan Allah ya ɗaukaka ka, ka zama wani babban mutum a samu wasu bayanan cutar da kai daga wajenta.


Mutum mai son cimma manyan burika a rayuwa bayyana sirrinsa gaba ɗaya ba abinda ya kamata da shi ba ne ba wai ga mace ba kawai hatta ga 'yan uwansa na uwa ɗaya uba ɗaya.


Ka yi ƙoƙari ka dinga taƙaita sanar da budurwarka bayananka, nan gaba za ka min godiya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user