Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan domin su gaisa da baƙonsa, ga mamakinsa sai ya ga ƙofar ɗakinsa a buɗe, babu baƙo babu alamunsa, amma kuma ga dabbobinsa nan da kuma hajarsa ta mai.
Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in Kashi Na 7
Hoto: Zu 09/iStock Photo
Yana nan tsaye yana mamakin inda baƙonsa ya shiga, sai ga kuyangarsa Murjanatu ta fito, ta durƙusa ta gaishe shi.
Ya tambaye ta, ko ta ji motsin baƙonsa? Domin tagar ɗakinta na kallon farfajiyar gidan ne, duk wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu za ta iya ji daga cikin ɗakinta. Ta ce da Ali Baba, "Maigida zo ka duba da idonka, ka ƙara yi wa Allah godiya, da ya kuɓutar da kai." Ta ja shi har zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya buɗe ɗaya da kansa ya ga abin mamaki.
Ali Baba ya buɗe jakar mai ɗaya, sai ya ga mutum a ciki, riƙe da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro, Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su da tafasasshen mai." Ta kwashe labarin abin da ya faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa gidansu lamba, da kuma yadda ta zo ɗibar mai a cikin hajar baƙo, ta gane mutane ne a ciki, da yadda ta ƙona su da mai, da kuma yadda ta ga shugaban ɓarayi ya buɗe gida cikin dare ya arce, da ya gano cewa an kashe masa mutane.
Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata albishir da wata kyauta mai tsoka, amma bai faɗa mata ko mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani bawansa mai suna Abdallah.
Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya faɗa masa abin da ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke cikin gidan su gina ƙaton rami mai faɗi da zurfi, wanda zai iya ɗaukar ɓarayin nan duka, su rufe su ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawansa Abdallah suka gina ƙaton rami, Allah ya taimake su akwai danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha wata wahala ba wurin haƙa ramin.
Suka riƙa cicciɓo gawar ɓarayin nan, ɗaya bayan ɗaya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da ƙasa suka rufe. Ali Baba ya gargaɗi bawan nan, duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje. Jakan ɓarayin nan kuwa, sai Ali Baba ya riƙa ɗibar biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba, har suka ƙare.
Shugaban ɓarayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali Baba, sai ya koma maɓoyarsu a cikin daji. Ba da jimawa ba, kaɗaici da kuma tsoro suka lulluɓe shi, ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kaɗai a cikin daji ba. Saboda haka sai ya ɗebi wani abu daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani baƙon alhaji, ya koma cikin gari.
Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi masa iso gun Sarki, ya ce shi baƙo ne, sunansa Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki. Sarki ya sa dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma yanzu babban ɗansa ne, saurayi ɗan kimanin shekaru ashirin da uku, a ciki.
Koja Husaini ya tare cikin sabon gidansa, lokaci-lokaci kuma ya kan koma maɓoyarsu ya ɗebo wani abu daga cikin dukiyarsu, wadda yanzu ta zama mallakarsa shi kaɗai. Amma ya kan yi taka-tsan-tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja hankalin mutane su fara zarginsa. Kullum zuciyarsa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya kashe Ali Baba.
Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da maƙocinsa, ɗan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su yi ta hira a tsakaninsu.
Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa ɗansa ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na zaune a ƙofar gidansa, ƙarƙashin wata bishiya, yana hutawa. Da ganinsa, nan take Koja Husaini ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan ɗansa, bai ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da ana kallonsa.
Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya yi tafiyarsa. Ba a daɗe ba kuma sai ga ɗansa ya fito, da ya ga Koja Husaini zaune a ƙofar gidansa, sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro, wanda ya zama tamkar abokinsa a halin yanzu, ɗan Ali Baba ne, babban maƙiyinsa a duniya. Don haka sai ya raya a zuciyarsa, bari ya ja shi a jika, wata ƙila ta sanadiyarsa zai cimma burinsa na kashe Ali Baba.
Tun daga wannan rana sai alaƙar Koja Husaini da Ɗan Ali Baba ta ɗauki sabon salo. Koyaushe Koja Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Ɗan Ali Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaƙu da juna suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.
Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida, watau iyalansa da barorinsa kawai. Da Ɗan Ali Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban abokinsa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja Husaini ya yi matuƙar farin ciki a ransa, damar da yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar ƙoƙarin sa ya keɓe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan iyalansa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata sharɓeɓiyar wuƙa ya sulle ta a cikin rigarsa, suka tafi.
Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Ɗan Ali Baba ya gabatar da abokinsa ga mahaifinsa, sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba; Ali Baba da matarsa, Ɗan Ali Baba da abokinsa Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan ciye-ciye da shaye-shaye.
Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganinsa, nan take ƙwaƙwalwarta, mai kama da kwamfuta, ta gane shi. Shugaban ɓarayn nan ne ya sake dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba, ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin hanyar da za ta yi maganin wannan ɓarawo.
Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa bakinsa da abin da aka tanadar. Tuni kuma Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe wannan ɓarawo. Ta raɗa wa bawan nan Abdallah, ya ɗauko dundufarsa ya fara kiɗa ita kuma za ta yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk lokacin da yake buƙatar nishadi. Abdallah ya jawo dundufarsa ta kiɗa, ya fara kaɗawa a hankali, dama kuma gwanin kiɗa ne, ita kuma Murjanatu ta tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.
Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin maza, ta kan riƙe wata 'yar ƙaramar wuƙa a hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo gaban mutum ta ɗaga wuƙar nan kamar za ta daka masa ita a zuciya, sai ta juya wuƙar ta daka masa mariƙin wuƙar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi. Duk ƙasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta Koja Husaini ya san da haka.
Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa, sai ta ɗauko 'yar ƙaramar wuƙa ta riƙe a hannunta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin ranta. Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kiɗa, Abdallah, ta ɗaga wuƙar kamar za ta daɓa masa ita, sai ta daɓa masa ƙotarta, aka yi tafi. Ta wuce wurin Ɗan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban ɓarayi, ta ɗaga wuƙar nan, ta tattara iyakar ƙarfinta a hannunta mai wuƙar ta kirɓa masa ita a ƙahon zuciya. Nan take ɓarawo ya faɗi ƙasa yana shure-shure har ya mutu.
Ko da Ali Baba da ɗansa suka ga wannan ɗanyen aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili ba, sai suka taso mata, hankalinsu a tashe, suka far mata da faɗa, don me za ta kashe baƙon da suka gayyato, laifin me ya yi mata. Murjanatu ta dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane ne wannan baƙo, sannan ta ce musu, "Duk da yake ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida ba, amma na tabbata manufarsa ba ta alheri ce ba."
Da suka duba jikin shugaban ɓarayi, sai suka samu sharɓeɓiyar wuƙa sulle a cikin rigarsa. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu ta kuɓutar da rayuwar Ali Baba daga halaka. Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin da ya ɓoye mata a cikin zuciyarsa, wanda kuma ya taɓa furta mata.
Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na 'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma idan kin yarda ina so ki amince da ɗana ya zama mijinki." Sannan ya juya wurin ɗansa ya ce da shi, "Ya kai ɗana, na san da cewa ba za ka ƙi amincewa da zaɓina ba, ka amince na aura maka Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami galaba a kaina, dama ya yi ƙoƙarin yin abota da kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da buƙatarsa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kuɓutarmu gaba daya."
Murjanatu da Ɗan Ali Baba suka amince da junansu. Bayan 'yan kwanaki aka ɗaura musu aure, aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amma ya 'yanta ta kuma ya aurar da ita ga ɗansa, da ma yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu wanda ya san abin da ya faru.
Ali Baba bai ƙara komawa maɓoyar 'yan fashin nan ba, domin yana gudun ya haɗu da sauran ɓarayin nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da aka shekara ya ga babu wata barazana da ɓarayin nan suka ƙara yi masa, ran nan sai ya shirya ya faki idon mutane ya ɗare saman dokinsa, ya nufi dajin. Ya ɗebo dukiyar ya aza kan dokinsa ya hawo ya dawo.
Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga lokaci zuwa lokaci, yana ɗebo dukiyar da ɓarayin nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk lokacin da ya je ya kan yi sauri ya ɗiba ya dawo don tsoron kada sauran ɓarayin biyu su tarar da shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci gaba da kasuwancinsa a kasuwa, don haka babu wanda ya san sirrunsu. Ya zamana babu mai arziki duk faɗin ƙasar kamar Ali Baba.
Ya yi zamansa shi da iyalinsa cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba su.
ƘARSHE
Ga waɗanda ba su samu damar karantawa ba tun daga farko ba, to su kwantar da hankalin su, su latsa nan don komawa ga shafin farko na labarin ko kuma nan....
DUBA WANNAN: Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (1)
Alhamdulillah! Wannan shi ne ƙarshen hikayar Ali Baba da Ɓarayi Arba'in, wacce muka kwashe tsawon makonni bakwai muna kawo muku.
Idan Allah ya kai mu litanin mai zuwa, za mu zaƙulo muku wata hikayar mai daɗi da kuma ilmantarwa, wacce ma ta fi wannan.
Allah ya kai mu.
Tushe/Asali: Waziri Aku