Tuesday 15 October 2024

Ka Lura Da Abokan Ka Ko Aminan Ka

Tura Wannan Zuwa Ga

Tara abokai a wannan zamanin abu ne mai matuƙar sauƙi, kowa zai iya zama abokin ka amma ba lallai ba ne kowa kuma ya zama aminin ka.


Tara abokai
Hoto: Vancomm

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Ka yi nazari kafin ka yanke shawarar zaɓar amini, aminintaka tana da amfani sosai amma kuma tana da matuƙar haɗari a wannan zamanin da muke ciki.


Wanda ka aminta da shi , da shi za'a haɗa hannu wajen cin amanar ka, zai nuna maka shi masoyin ka ne na haƙiƙa, da ma kaɗan yake jira domin cimma manufar shi a kanka, da zaran ya biya buƙatar shi za ka neme shi ka rasa, tamkar ba ku taɓa kasancewa a tare ba, ko haɗuwa ku yi da shi sai ka ga yana kame-kame domin a lokacin ba ka da wani sauran amfani a gare shi.


A mafi yawancin lokuta idan hali ya zo ɗaya to aminantaka ta kan zo cikin sauƙi.


Ka zaɓi amini nagari ba amini na banza ba, ba lallai ba ne kowa ya zama mutumin kirki, haka ma ba lallai ba ne kuma kowa ya zama mutumin banza.


Allah ya zaɓa mana abokai nagari, ya kuma sanya su zama alkhairi a gare mu duniya da lahira Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user