Don kawai kuna soyayya da yarinya irin ta saurayi da budurwa ba shi ke nuna cewa hakan ya ishe ku zaman aure ba.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Ba Soyayya kawai ya kamata ka mayar da hankalin dubawa ba kafin aure ya kamata ka duba;
1. Zurfin aljihunka.
2. Zurfin kasuwancinka.
3. Zurfin albashinka.
4. Zurfin tunaninka.
Idan da hali ma ya kamata ku je wajen masana kimiyyar halayyar Ɗan Adam (Psychology) domin su karanci hallayyarku, su ba ku shawara yadda za ku zauna da juna idan kuma halinku ba na iya zama da juna ba ne, sai ku haƙurcewa juna gudun tashin tashina da rigingimu da rashin kwanciyar hankali.
SOYAYYA KAWAI BA ZA TA WADATAR BA
Ka tambayi wanda ya shekara uku ko huɗu zuwa sama da yin aure zai gaya maka wannan kalmar, akwai buƙatun rayuwa da suke dakushe so a daina jin ɗuriyarsa bayan aure, kamar dai Allah bai taɓa halittarsa a zuciyar ma'auratan ba. Don haka kafin ka yi aure ya kamata ka auna nawa kake samu? Nawa ne abinda buƙatun gida za su iya ci? Nawa ne zan ajiye a matsayin na buƙatun gaggawa? Kafin na yi aure ƙannina nawa ne mata ko maza da nauyinsu ke kaina? Nawa zan ajiye a matsayin hidimarsu?
Abin da kake mantawa shi ne waɗannan ƙananun buƙatun da kake gani ba komai ba ne su ne suke zama "Virus" ɗin da suke haɗiye soyayya su kashe ta murus ka ji amarya ta shaƙi kwalar ango tana faɗin "Me ka taɓa yi min?" Ko ango ya kallawa amarya mari har ɗan kwalinta ya yi hijira daga kanta.
Matan Arewa sai da tanadi kasancewar al'ada da addini sun hana su ayyuka da wasu sana'o'in.
Don haka ka gane cewa a zaman aure so kawai ba zai wadatar ba.