Wednesday 16 October 2024

Kalaman Soyayya Gauraye Da Turanci Da Hausa Masu Dadi

Tura Wannan Zuwa Ga

Salam Alaiki, beautiful, mai ƙaunata, mai ƙamshin apple, darajarki ta fi ta pineapple, ballantana ki sa kaya mai launin purple, ai dole ne a ce miki wonderful, na ranste ko a cikin school kin fi ƙarfin a ba ki kyautar bicycle. To ki ji tsoron Allah merciful, ki gujewa hawa motor cycle, tunda dai Allah ya ba mu tricycle, idan kin ji tsoron Allah merciful, to sai ki zauna peaceful, sai ki shiga aljanna successful.


Kalaman Soyayya Gauraye Da Turanci Da Hausa Masu Daɗi 
Hoto: Dreamstime

Marubuci:- Prince E

Ke ce wacce zuciyata ta natsu cikin alƙaryar son ta.


Ba ni da wani abin tinƙaho a duniyar masoya face ke saraauniyar zuciyata, ma'abociyar kyau da kwalliya.


Ke ce mafi kusanci ga zuciyata.


Ke kaɗai ce wacce zuciyata ta yarda kuma ta aminta da kyawawan ɗabi'unta.


Furen soyayyarki ya fi kowanne fure saurin yaɗuwa a cikin zuciyata.


Na kai ƙololuwa cikin sararin samaniyar ƙaunarki, babu wani abu wanda ya kasance yana da saurin tasiri a cikin zuciyata face daga gare ki yake.


Ke ce wacce kalamanta ke sanyaya min zuciyata.


Ke ce wacce murmushinta yake jefa ni cikin shauƙi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user