Idan mutum zai ci abinci sai ya ce;
بِسْمِ اللهِ.
Bismi l-lahi.
Da sunan Allah.
Idan ya manta to sai ya ce (yayin da ya tuna)
بِسْمِ اللهِ فِي أَوَّلِهِ وَآخِرِهِ.
Bismi l-lahi fi awwalihi wa akhirihi.
Da sunan Allah a farkonsa da ƙarshensa.
Wanda Allah ya azurta shi da abinci ya ci, to ya ce;
اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَأَطْعِمْنا خَيْراً مِنْهُ.
Allahumma barik lana feehi wa-at'imna khayran minh.
Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinsa, kuma Ka ciyar da mu wanda ya fi shi alheri.
Wanda kuma Allah ya azurta shi da madara ya sha, to ya ce;
اللّهُمَّ بارِكْ لَنَا فِيهِ وَزِدْنا مِنْهُ.
Allahumma barik lana feehi wazidna minh.
Ya Allah! Ka sanya mana albarka a cikinta, kuma Ka ƙara mana ita (madarar).