Tuesday, 1 October 2024

Karanta Ainihin Tarihin Rayuwar Ibn Taimiyya

Tura Wannan Zuwa Ga

Cikakken sunan Ibn Taimiyyah shi ne ' Taqiy al-Din 'Abu al-Abbas 'Ahmad ibn 'Abd al-Hallim ibn 'Abd as-Salam ibn ' Abdullah ibn al-Khiḍr ibn Muḥammad ibn al-Khiyr ibāllīr- ibn al-Khiḥr Ḥarrānī : أحمد بن عبد الحليم بن عبد السلام بن عبد الله بن الخضر بن محمد بن الخضر بن إبراهيم ب اللهن علي بن علي بن بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن علي بن عبد السلام .


Ainihin Tarihin Rayuwar Ibn Taimiyya
Hoto: Asharis assemble


MarubuciSaliadeen Sicey


Sunan Ibn Taimiyyah ( ابن تيمية ) ba a saba ganinsa ba ya samo asali ne daga wata mace daga cikin iyalansa saɓanin namiji, wanda al'ada ce ta da a lokacin kuma har yanzu. Laƙabin " Taimiyya " ya fito ne daga kakarsa wacce ake kira Taimiyyah. Ta kasance mai nasiha kuma an yi masa laƙabi da " Ibn Taimiyyah ". Taimiyya ta kasance fitacciyar mace, shahararriyar mai ilimi da taƙawa da sunan Ibn Taimiyya da yawa daga zuriyarta maza ne suka karɓa.


Ibn Taimiyyah, sunan haihuwa Taqī ad-Dīn ʾAḥmad ibn 'Abd al-Hallim ibn 'Abd al-Salam al-Numayrī al-Harrani, malamin Sunna ne, muhaddith, alkali, Salafist kuma masanin siyasa.


Ahmad ɗan Abdulhalimu ɗan Abdussalami ɗan Abdullahi ɗan Haliru ɗan Muhammadu ɗan Haliru ɗan Aliyu ɗan Abdullahi. Ya shahara da sunan Ibnu Taimiyyah saboda kakarsa da ake kira Taimiyyah. Ana kuma ce ma sa “Majduddini”. Sannan ana ce ma sa “Numairi” saboda shi dan kabilar Banu Numairi ne.


Sannan ana ce ma sa kuma “Harrani” saboda Harrana ne garin da aka haife shi. ( Yanzu Garin Yana Cikin Ƙasar Turkey 🇹🇷).  


Sannan ana ce ma sa “Dimashki” saboda a garin Dimashka ( Damascus Syria 🇸🇾 ) ne ya girma, ya yi karatu. 


ASALINSA


Ibnu Taimiyyah ɗan asalin ƙasar Turkiyya ne. Don an haife shi a garin Harrana wadda take arewa maso gabashin ƙasar ta Turkiyyah.


Haihuwa


An haife shi ne a ranar litinin 10 ga watan Rabi’ul Awwal 661H Wanda Ya zo dai-dai da 22 Janairu 1263, Amma bayan shekaru shida sai iyayensa suka yi hijira daga ƙasar zuwa ƙasar Siriya inda suka sauka a babban birnin Dimashka, hedikwatar Sham.


Dalilin hijirar tasu kuwa shi ne kaucema fitinar ‘yan Tattar waɗanda suka auka ma garuruwan musulmi suka yawaita ɓarna da zubar da jinin bayin Allah. Game da mahaifansa kuwa, shi ɗan gidan malamai ne domin ya sami kansa a tsakanin iyaye da kakanni da ‘yan’uwa ma’abota karatu. A lokacin da za su yi hijira kuwa babu abin da ya wahalar da su kamar littafai da ke tare da su masu ɗimbin yawa, ga shi kuma suna gudun maƙiya.


Al-harran garin da aka Haifi Shaihil Islam Ibn Taimiyya
Hoto: Wikipedia

Ba domin kiyayewar Allah ba ma ba za su tsira da rayukansu zuwa Sham ( Syria 🇸🇾) ba. Isarsu ƙasar Sham ke da wuya mahaifin Ibnu Taimiyyah Shihabuddini ya fara koyarwa da wa’azi a babban masallacin Jum’ah na Dimashka wanda ake kira Al-Jami’ul A’azam masallaci mafi girma. 


Daman shi fitaccen malamin furu’a ne a mazahabar Hambaliyya. Nan take aka shugabantar da shi ga babbar makarantar hadisinnan da aka sani Darul Hadis As-Sukkariyyah, aka kuma ba shi gida a cikin makarantar in da nan ne Ɗansa Ibnu Taimiyyah ya girma. Kafin haka, kakan Ibnu Taimiyyah Majduddini sanannen malami ne da ya yi wallafe-wallafe a fannin hadisi da Usulul Fiqhi  shi ne mawallafin littafin nan na Muntakal Akhbar wanda Imamus Shaukani ya yi wa sharhi a cikin Naulul Audar. Haka ma baffansa Fakhruddini, malami ne fitacce da ya wallafa babban littafin Tafsirin Alqur’ani. 


Shi ne kuma wanda ya gaji Ibnul Jauzi a kujerarsa ta karantarwa da babban mumbarinsa na Bagadaza.


Kuma IbnuTaimiyyah ya yi karatu a wurinsa.


Mahaifa


Harran gunduma ce a gundumar lardin Şanlıurfa a ƙasar Turkiyya. Yanki ne mai faɗin kilomita 96 kuma yana da yawan mazauna 96,072 a lissafin shekarar (2022). Garin Ya na da kusan kilomita 40 (mil 25) kudu maso gabas da Urfa da kilomita 20 (mil 12) daga mashigar kan iyakar Siriya ta Akçakale.


Mahaifar Ibn Taimiyya
Hoto: Onedio

An kafa birnin Harran a wani lokaci tsakanin ƙarni na 25 zuwa 20 kafin haihuwar Annabi isa (AS) (BC), mai yiwuwa ya kafu a matsayin birnin 'yn kasuwa na Sumerian. A tsawon tarihin farko birnin Harran ya girma cikin sauri zuwa babbar cibiyar al'adu, kasuwanci da addini ta Mesopotamiya. Kuma ya sha zama babban birnin lardi sau da yawa a matsayi na biyu mafi muhimmanci ga babban birnin Assuriyawa na Assur da kanta. A lokacin rugujewar Daular Assuriya, Harran ya ɗan yi aiki a matsayin babban birnin ƙarshe na Daular Neo-Assyrian (612-609 BC).


Harran
Hoto: Holy land photos

Daular Mongol ta mamaye birnin a shekara ta 1260 kuma ta lalata kusan dukkan birnin, mutane sun bar garin har shekara zuwa ta 1271. Duk da cewa an bar Harran a matsayin sansanin soja a ƙarƙashin wasu gwamnatoci a baya, amma a cikin ƙarni na biyar da suka wuce an yi amfani da shi azaman wurin zama na wucin gadi ta wurin makiyaya na gida. Al'ummomi Harran sun koma cikin ƙauye na dindindin a cikin shekarun 1840s, amma kwanan nan Harran ya girma zuwa birni na dindindin ta hanyar ci gaban ban ruwa na aikin gona na cikin gida. Harran gundumar Turkawa ce har zuwa 1946, bayan da aka mayar da ita zuwa wani yanki na gundumar Akçakale. Ta dawo da matsayinta na gunduma a cikin shekarar 1987.


Birnin Harran
Hoto: Pinterest

A yau, babban wurin yawon buɗe ido ne na cikin gida. Garin ya shahara musamman da kiwon ƙudan zuma waɗanda ke da alaƙa da gine-ginen da suka riga suka kasance a Harran a zamanin Mesopotamiya ta dā.


Tashinsa da Iliminsa 


Ibnu Taimiyyah ya tashi a gidan ilimi kamar yadda muka gani. Ya kammala hardar Alƙur’ani tun a lokacin ƙuruciya. Sannan ya kula da sanin ilimomin Fiƙihu da Hadisi da Tafsiri da Arabiyyah.


 Tarihin Ibn Taimiyya
Hoto: Usman Abdullah Malik

Ya soma karantarwa da fatawa da rubuta littafai da tattaunawa da malamai Munazara tun bai wuce shekaru 20 Ba. Koda ya cika shekaru 30 an fara yi masa laƙabin Mujtahidi kuma “Mairaya Sunnah”. Yana da matuƙar wuya a iya siffanta baiwar da Allah ya yi wa Ibnu Taimiyyah ta fuskar ilimi. Masu ba da labarinsa na ganin kasawarsu wajen bayyana irin hikimomin da ke tattare da shi ta wannan haujin. An lisafta malaman da ya gurfana a gabansu don ɗaukar karatu aka tarar sun zarce malamai 200.


Akwai kuma littafan da ya karanta su sau da yawa a wurare daban-daban kamar Musnad na Imamu Ahmad. 


Game da nasa littafai shi kuma, Ibnu Taimiyyah ya wallafa sama da littafai hamsin a fannona daban-daban na addini, banda jananan wallafe-wallafensa da aka tara cikin Majmu’ul Fatawa mai sifili talatin da bakwai. 


Ya ishi mai karatu misali abin al’ajabi cewa, duk da yake Ibnu Taimiyyah bai wallafa Tafsirin Alƙur’ani ba, amma malamai daga bisani sun wallafa shi daga cikin littafansa. Ma’ana an tattara wuraren da ya yi sharhi akan ayoyin Alƙur’ani daga ciki littafansa a tsakankanin maganganunsa da kafa hujjojinsa, sai ga shi an samu kusan kammalallen Tafsiri mai Mujalladi huɗu. 


Mujaddadi Ibnu Taimiyyah muna iya cewa, Allah gwanin sarki ya tashi Ibnu Taimiyyah ne a wani lokaci da buƙatar irinsa ta yawaita. Don kuwa a wancan lokaci al’umma tana fama da matsaloli da rikici da tashin hankula na ciki da na waje. Daga cikin gida musulmi na fama da rabuwar kai, da yawaitar ƙungiyoyi da yaɗuwar bidi’ah da raunin ilimin furu’a.


Ga kuma lalacin da ya zo a cikin jama’a da zaluncin sarakuna da kwaɗayin malamai. Tsibbace-tsibbace da bokanci da duba sun zama gama-gari a cikin al’umma. Daga waje kuma ‘yan mishan sun kai ma musulmi farmaki, ‘yan Shi’ah masu kiran kansu Fadimawa sun haɗa kai da su. Sannan ga Tattar sun shelanta mummunan yaƙi da musulunci da musulmi a duk in da suke a wancan lokaci. 


Shaihun musulunci ya fuskanci duka waɗannan matsaloli da nufin magance su. Ya kuma samu taimakon Allah matuƙa a wajen cimma wannan burin nasa.


Mutum ne da aka suffanta shi da kaifin basira da ƙarfin ƙwaƙwalwa, har wasu ma na ganin bai taɓa sanin abu ya manta da shi ba. Yana da ƙarfin tuna ayoyin Alkur’ani da nassoshin hadissai da maganganun malamai na kowane fanni. Don haka ya kasance mai kaifin hujja wadda take yanke wuyan abokin gaba nan take.


Ga shi kuma jarumi da ba ya tsoron ko-ta-kwana. Don haka ba ya da ja da baya ga abin da ya sa gaba. Sannan yana da kwarjini a idon jama’a da kyawawan ɗabi’u da suka daɗa soyar da shi ga mutane. Ga shi mutum mai kishin gaskiya da ƙoƙarin yaɗa ta. Haɗa da halinsa na gudun duniya da rashin kula da jin daɗinta. Irin wannan malami Allah ya ɗora shi a kan kyakkyawar hanya irin ta Annabawa wane irin canji kake tsammanin al’umma ba za ta ci moriyarsa ba ta hanyarsa? 


Ɗan Taimiyyah nan take ya rurrusa aƙidun da suka zame ma musulunci tsutsar goro ta hanyar rubuce-rubucensa da wa’azozinsa da karantarwarsa. Ya kece raini a wajen wargaza aƙidun Yahudawa da na ‘Yan mishan. Ya yi faɗa da ƙungiyoyi mabiyan son zuciya irin mulhidai da zindiƙai da ‘yan Shi’ah da waɗanda suka wuce wuri a Sufanci.


Ya yi kira ga koma ma littafin Allah da Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba tare da ta’assubanci ga wani mutum ko ƙungiya ko mazhaba ba. 


Sa’annan ya kira sarakuna da talakawa zuwa ga yaƙar kafirai waɗanda suka keta hurumin musulmi, musamman dai Tattar. Ya kuma fita ya yi yaƙi a matsayin ɗaya daga cikin sojoji. Tare da haka kuma Ibnu Taimiyyah ya kafa wata makaranta da Allah ya yawaita almajiranta tun daga wancan zamani har zuwa yau, kuma tana ci gaba da bunƙasa har a naɗe ƙasa.


Wannan makaranta tasa tana mutunta magabatan Sahabbai da Tabi’ai da waɗanda suka biyo bayansu, da shugabannin mazhabobi, tana kuma la’akari da ra’ayoyinsu da fatawoyinsu baki ɗaya. Tana kuma rinjayar da nassi ingantacce idan ya zo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan maganar kowa kome darajarsa. 


Wannan makaranta dai tana da ɗaruruwan littafai da dubban malamai a cikinta. Dukkaninsu suna jingina kansu ga Sunnah da bin magabata ba ga shi Ibnu Taimiyyah ɗin ba. Jarabawar da Ibnu Taimiyyah ya gamu da ita yana da wuya Allah ya ɗaukaka wani bawansa ba tare da ya gamu da wata jaraba ba a rayuwarsa. Wannan ita ce sunnar Allah ga Annabawa da malamai mutanen kirki.


Shehun musulunci ya gamu da jarabce-jarabce da dama a sakamakon jihadinsa na makami da na alƙalami waɗanda suka dagula ma sa jin daɗin rayuwa. 


Zan faɗi wasu daga cikinsu a takaice kamar yadda suka zo a tarihinsa daga littattafai da dama.


A shekarar 696H ya gamu da ƙyashi daga abokan tafiya, malamai, waɗanda suka ɗauki littafinsa Al-Fatwal Hamawiyyah suka kai ƙararsa da shi a wurin mahukunta. Sun bi duk hanyoyin da suke iyawa wajen murza maganarsa da ba ta irin ma’anar da suke so su jingina ma sa. A wannan lokaci sarki Saifuddin Jagan ya goyi bayan Ibnu Taimiyyah, ya kuma husata da waɗanda suka kafa adawa da shi. Don haka wannan jarrabawa ba ta daɗe ba ta gushe.


A shekarar 705H lokacin da farin jinin Ibnu Taimiyyah ya gama bayyana, bayan an ga rawar da ya taka a yaƙin da aka yi da Tattar, har kuma ya samu kusanci da hukuma abin da ya ba shi damar sa a kawar da wasu ɓarnace-ɓarnace. Nan take sai ƙurjin hassada ya sake tashi a zukatan wasu malamai daga cikin sufaye.


Sai wani malami da ake kira Nasrul Mambiji da wani malami bamalike ana ce ma sa Ibnu Makhluf suka tafi hedikwatar masarauta da ke ƙasar Masar ( Egypt 🇪🇬 ) su ka kai ƙarar Ibnu Taimiyyah suna tuhumar sa da gurɓata aƙidun jama’a.


Suka kafa hujja da littafinsa na Al-Akidatul Wasiziyyah. A nan ma sarki ya ba da umurni aka zaunar da shi tare da manyan malamai in da aka karance littafin nasa, daga ƙarshe kuma aka barrantar da shi daga saɓa ma magabata.


Sai ma a wannan karon ya samu takardar yabo daga Sarkin Musulmi. Wata ɗaya bayan faruwar wannan, sai waɗannan malaman suka sa sarki ya rubuta ma sa wata takarda ana neman sa da zuwa Misra ( Egypt 🇪🇬) don ya bayyana a gaban sarki. A wannan karon da tuhumar yana neman sarauta! 


An dai zaunar da shi a gaban Ibnu Makhluf don ya yanke ma sa hukunci, abin da ɗan Taimiyyan ya ƙi yarda da shi, kasancewar shi ne abokin mai husumar da ya kai ƙararsa.


Shehul Islami sai da ya share wata goma sha biyu cif a gidan kurkuku  kafin a nemi ya fita, in da shi kuma ya ƙi fita ya ce, sai an bayyana ma sa laifinsa. Daga ƙarshe ya fita daga kurkukun bayan ya cika watanni goma sha biyar da sati biyu da kwana ɗaya bisa ga nacewar wani basaraken garinsu.


Wata bakwai bayan fitowarsa sai aka sake mayar da shi a cikin watan Shawwal na 707H saboda ya ci gaba da zama a Masar mutane na amfana da shi. A wannan karon sai ya kasance mutane suna tururuwa a gidan kaso don gaishe shi da yin fatawa a wurinsa, abin da ya daɗa cinna wutar gaba a tsakaninsa da waɗanda ke bibiyarsa da baƙar aniya. 


Bayan fitowarsa ma, ɗan Taimiyyah bai fasa abin da yake yi na karantarwa da fallasa miyagun aƙidu ba. Wannan ya sa aka ɗauke shi daga Alkahira zuwa Iskandariyya da nufin ya haɗu da ‘yan dabar garin su kashe shi.


Ana haka ne sai aka samu canjin gwamnati lokacin da sarki Muhammad ɗan Kalawun ya sake koma ma kujerar sarauta sai ya mayar da Shehul Islami zuwa hedikwatar ta Masar. Daga nan kuma suka fita a shekarar 712H da nufin yaƙar kafiran Tattar, sai Allah ya mayar da maƙiyan garuruwansu ba tare da an yi yaƙi ba. Don haka, sai Ibnu Taimiyyah ya koma gida Sham, in da ya haɗu da tarba wanda ba a taɓa ganin irinta ba!


Bayan ya yi shekara bakwai da sati bakwai a ƙasar Masar tun wancan kiran da aka yi masa, ko bayan komawarsa gida Shehul Islami ya ci gaba da samun matsaloli da malamai masu ƙaramin sani da taurin kai. Kamar yadda suka yi caa akansa wai don ya ce, in mutum ya yi rantsuwar saki kaffara kawai zai yi, aurensa na nan.


Haka ma don cewar da ya yi saki uku na komawa ɗaya idan an yi su zama guda. Waɗannan malamai ba su samu sukuni ba sai da suka sa aka hana shi fatawa a shekarar 719H. 


A shekara ta 720H aka sake iza ƙeyar babban malamin zuwa gidan kaso in da ya share wata biyar da kwana goma sha takwas. 


A shekara ta 726H wasu Alƙalai sun tsoma bakinsu a cikin rikicin Ibnu Taimiyyah da maƙiyansa, in da aka wallafa wata fatawa ta ƙarya aka jingina ta gare shi, wai ya haramta ziyarar kabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da na sauran Annabawa, alhalin shi kuwa ya rarrabe tsakanin ziyararsu ne ita kaɗai da kuma haɗa ta da yin tafiyayya. Ya labarta saɓanin magabata a kanta, sannan ya nuna karkata ga hanawa idan ya kasance an yi tafiyayya saboda ita. Ya kuma bayyana hujjojinsa na ingantattun hadissai. 


Wannan rikicin ma dai sai da ya sake mayar da wannan bawan Allah a gidan maza, in da ya samu damar da ya yawaita wallafe-wallafe gami da bautar Allah Ta’ala. 


A shekara ta 728H aka fitar da duk littafan da ke tare da shi da alkalumma da tawadar da aka samu a wurinsa, saboda wani malami da ake kira Ikhna’i ya kai karar sa, don ya yi ma sa raddi, kuma wai ya jahiltar da shi.


A nan ya zama dole Ibnu Taimiyyah ya haƙura ya duƙufa ga zikiri da sallah da karatun Alkur’ani da yake waɗannan suna a kansa tun zamanin ƙuruciya. 


RASUWARSA 


Ya fara rashin lafiya a farkon Satumba 1328.


Allah ya karɓi ransa a gidan kurkuku na birnin Dimashka ( Damascus Syria 🇸🇾 ) yana da shekaru 67 waɗanda suke cike da karantarwa da haƙuri da jihadi. Ya rasu kafin wayewar garin litinin 20 ga watan Zul Qi’ida 728H. Wanda Yazo dai-dai da 26 Satumba 1328. 


Da wannan labari ya isa ga jama'a, sai aka yi ta nuna goyon bayansa ga jama'a. Bayan da hukumomi suka ba da izini, an ba da rahoton cewa dubban mutane sun zo don nuna girmamawa. Sai suka taru a cikin Kagara suka yi jerin gwano har zuwa masallacin Umayyawa. An gudanar da sallar jana’izar a cikin kagara wanda malami Muhammad Tammam ya yi, kuma an yi na biyu a masallacin. An yi sallar jana’iza ta uku kuma ta ƙarshe ta ɗan’uwan Ibn Taimiyyah, Zainul-Din. An binne shi a Damascus, a Maqbara Sufiyya ("maƙabartar Sufaye"). An binne ɗan uwansa Sharafuddin a maƙabartar da ke gabansa.


An ruwaito cewa maza dubu ɗari biyu da mata dubu goma sha biyar zuwa goma sha shida ne suka halarci sallar jana'izarsa. Ibn Kathir ya ce a tarihin Musulunci, jana'izar Ahmad bn Hanbal ne kaɗai ya samu halartar kamar Wannan taron. 


IYALI 


Bai yi aure ba ballantana ya bar zuri’a. Bai kuma taɓa furta kalma ɗaya da take nuna rashin sha’awarsa ga auren ba. 


To, ko me ya hana shi cin moriyar

wannan Sunnah?


Sanin gaibu sai Allah.


Ɗalibai 


Da yawa daga cikin ɗaliban Ibn Taimiyya sun zama malamai a nasu ɓangaren.  Ɗalibansa sun fito ne daga wurare daban-daban kuma sun kasance a makarantu daban-daban (mahabbai).  Shahararrun ɗalibansa su ne Ibn Qayyim Al-Jawziyya da Ibn Kathir. Sauran ɗalibansa sun haɗa da: 


1, Al-Dhahabi

2, Al-Mizzi

3, Ibn Abdil-Hadi

4, Ibn Muflih

5, ’Imad al-Din Aḥmad al-Wasiti

6, Najm al-Din al-Tufi

7, Al Ba'labakki

8, Al Bazzar

9, Ibn Qadi al-Jabal

10, Ibn Fadlillah al-Amri

11, Muhammad Ibn Al-Manj

12, Ibn Abdus-Salam al-Batti

13, Ibn al-wardi

14, Umar al-Harrani

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user