Zan furta miki kalmar so a gare ki a duk yanayin da nake ciki. Zan ƙaunace ki a duk yanayin da kike ciki, ba zan guje ki ba.
Marubuci:- Prince E
Hmm ke kaɗai ce jallin jal gimbiya shugabar gimbiyoyi, babu wacce ta isa ta kama farcen ƙafarki bare ke kanki. A wajena ke ce zaɓina.
A duk tsanani ko wuya, zan zauna da ke koda a lambun ƙaya ne.
Ina son ki so irin na ɗa da uwa.
Ina son ki so wanda bai da algus a ciki.
Ki riƙe mini alƙawari ya gwarzuwar sadaukiyar masoyiyata. Jarumar babban birnin alƙaryar zuciyata.
Ina son ki, so na gaskiya wanda ba
yaudara a ciki.
Ba na son maƙiyinki, koda kuwa ya
taimake ni a rayuwa.
Ki riƙe ni tamkar yadda na riƙe ki.
Ba na son maƙiyinki, koda
kuwa ya kashe maƙiyina.
Tsananin son ki yana neman zautar da ni, na kan rasa kaina a duk lokacin da tunaninki ya turnuƙe ni.
Na kan ji komai ya wadatu gare ni idan na ji kyakykyawar muryarki.