Monday 7 October 2024

Karanta Gajerun Sakonnin Yabon Sassan Jikin Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Idanuwanta tamkar an sato taurari guda biyu a sama an sanya mata su.


Saƙonnin Yabon Sassan Jikin Masoyiya
Hoto: Photo done

Marubuci:- Prince E


Hancin ta a tsaye yake kamar eriyar/ƙeriyar rediyo.


Laɓɓan bakinta masu taushi kamar furen turaren zubardaj.


Lafuzzan bakinta da halayenta masu tashi kamar gajimare.


Yatsun hannuwanta kamar tsintsiya, dogaye sirara kamar an feƙe da shafana/shafino.


Ga ta da murmushi mai jan hankali mai shiga jiki har zuciyar mai kallon ta, tamkar sanyin safiyar asubahi.


Tafiyar ta cikin lumana babu baragada/sauri kamar mai tausayin ƙasa.


Ga ta kyakkyawa irin wacce kowanne saurayi ke mafarkin mallaka.


Allh Sarki ƙanwata, har yau ba a ƙirƙiri haruffan da za su iya bayyana ainihin kyawunki a rubuce ba.


Matsayinta a cikin mata tamkar zinariya ce a cikin ɓaƙaƙen ƙarfe da dangoginsa.


Ke ce na nuna ƙanwata.


Ina ma hannayena za su iya taimaka mini na tashi sama, da na yi amfani da su na keta giza-gizai na taho wurinki.


Kina raina ƙanwata, ƙaunar da nake miki ta fi wacce makaho yake yi wa idanuwa.


Zuciyata idan tana tunaninki tamkar ta tsago ƙirjina ta taho nemanki da kanta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user