Tuesday, 29 October 2024

Karanta Ire-iren Baiwar Ɗan Adam 14 Masu Ban Mamaki

Tura Wannan Zuwa Ga

Kowa yana da wata baiwa da Allah ya yi masa wani ya san da ita, wani kuma har yanzu bai gano ta ba. Ita fiƙira ko baiwa tana da fifiko a wurare da dama, amma duk wacce Allah ya ba ka sai ka yi masa godiya.


Ire-iren Baiwar Ɗan Adam 14 Masu Ban Mamaki
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Muhammad Auwal Ahmad


Gano baiwar da Allah ya yi maka na nufin ka yi amfani da ita wajen aiwatar da wasu abubuwa masu kyau, waɗanda za su taimaka maka su kuma taimaka wa al'umma. Amma ba ta nufin ɓata kanka, kuma ba ta nufin yi wa wani mugunta ko makamancin haka.


Ba komai ba ne yake sa masana janyo mutane a jika su koya musu abubuwa da dama sai don gano baiwar da Allah ya yi musu, sannan sai su ɗaura su bisa wannan turbar don morar su a duniya. 


Akwai mutanen da suke da baiwar zane, ko lissafi, ko iya wasu abubuwa masu ban mamaki. Wani da ka gan shi ba za ka yi tunanin shi ke da wata baiwa ta yin wani abu ba. Wasu kuwa su kan iya yin wasu abubuwa da ya wuce da tunani ko shekarunsu ko makamancin haka, kai da ka gani sai ka yi shakku akan lamuran. 


Rabe-Raben Baiwa ko Fikira. Da farko ya kamata mu san cewa baiwa ko fikira ko basira ta rabu kashi-kashi, kamar haka:


1. Mathematical-Logical Intelligence: baiwar lissafi, warware sarƙaƙiya, tunanin gano sababbin dabarun lissafi da sauransu. Misali: Albert Einstein, Nikola Tesla, Mark Zuckerberg.


2. Linguistic Intelligence: baiwar rubutu, zance, zube, zanen-baka, sarrafa kalmomi, iya magana da sauransu. Misali: William Shakespeare, Abubakar Imam, Abubakar Tafawa Ɓalewa, Wole Soyinka.


3. Spatial-Visual Intelligence: baiwar abubuwan da suka shafi sararin samaniya, ƙirƙire-ƙirƙiren zane, zanen gidaje, injiniyanci, haɗe-haɗen hotuna, tuƙin jirgin sama, gane taswira da sauransu. Misali: Leonardo Da Vinci, Jelani Aliyu.


4. Musical Intelligence: baiwar waƙe-waƙe, kiɗe-kiɗe, rubuce-rubucen waƙa/kiɗa. Misali: Michael Jackson, Nura M. Inuwa, Mamman Shata.


5. Bodily-kinaesthetic Intelligence: baiwa a kan abubuwan da suka shafi wasanni, motsa jiki, rawa, dambe, tsere da sauransu. Misali: Cristiano Ronaldo, John Cena.


6. Intra-personal Intelligence: baiwar gane halayyar mutane, falsafa, fahimtar shauƙinsu da na wasu da sauransu. Misali: Sigmund Freud, Sadhguru, Plato.


7. Naturalist Intelligence: baiwa a kan fahimtar tsarukan halittu. Misali: Charles Darwin.


8. Inter-personal Intelligence: baiwa a kan fahimtar wasu da tunaninsu, da sauƙin mu'amala da mutane; kamar 'yan jaridu, 'yan siyasa, 'yan wasan kwaikwayo, 'yan kasuwa ko lauyoyi. Misali: Mahatma Gandhi, Bill Clinton, Ali Nuhu, Nasiru Salisu Zango.


9. Teaching-Pedagogical Intelligence: baiwar koyarwa da fahimtar da wani abubuwa cikin sauki


Wannan rabe-raben da ke sama bisa ga nazariyyar Gardner Howard ne, wani masanin halayyar Ɗan-Adam. Amma akwai wasu duk da shi bai yi amanna da su ba, amma yanzu sun zama ruwan dare. Ga su kamar haka:


10. Digital Intelligence: baiwar amfani da yanar gizo cikin sauƙi, sarrafa hanyoyin shiga da iya amfani da ƙirƙire-ƙirƙiren yanar gizo, kamar masu tashoshin YouTube, shafukan yanar gizo, ko iya sarrafa waya/na'ura da yanar gizo.


11. Programming Intelligence: baiwar iya tsare-tsaren na'ura, ƙirƙire-ƙirƙiren manhajoji, shafukan yanar gizo da sauransu. Amma wasu suka ce wannan baiwar tana ƙarƙashin Mathematical-Logical Intelligence wanda ya zo a lamba ta ɗaya.


12. Engineering Intelligence: baiwar ƙirƙire-ƙirƙiren abubuwa don sauƙaƙa al'amuran yau-da-gobe. Amma wasu suka ce wannan baiwar tana ƙarƙashin Spatial-Visual Intelligence wanda shi ma ya zo a lamba 3.


13. Humour Intelligence: baiwar barkwanci, ƙirƙire-ƙirƙiren labaran barkwanci.


14. Cooking Intelligence: baiwar dafa abinci, sarrafa hanyoyin da abinci zai yi daɗi da sauransu.


Bayan waɗannan akwai wasu ɓoyayyun fikirori ko baiwa da mutun yake da su amma wataƙila masana ba su gama gano su ba.


DUBA WANNAN: Hanyoyi 10 Na Sanin Yadda Za Ku Gano Baiwar Ku Da Kanku


Shawarata a nan ita ce: ka nemi sanin baiwarka kuma ka yi aiki da ita, sannan idan kana da wata hanya da za ka taimaka wa wani don gano baiwarsa to ka taimaka, sannan ka ɗaura shi a hanyar da zai ci ribarta idan kana da dama.


Yanzu ka yi tunani, wacce baiwa Allah Ya ba ka, ko kuma yaronka ko ɗan'uwanka? Ka shirya yadda za ka sarrafa ta sannan ka yi aiki da ita cikin hikima yadda za ka taimaki kanka ka taimaki al'ummar duniya.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user