Wednesday 9 October 2024

Karanta Kammalallen Tarihin Rayuwar Annabi Sulaiman (A.S)

Tura Wannan Zuwa Ga

Annabi Sulaiman (A.S) (Da Larabci: سُلَیمان ) ɗan Dawuda ne (A.S) kuma ɗaya daga cikin manyan annabawan Banu Isra'ila. Ya roƙi Allah Mulkin da ba wanda zai yi kamar sa a bayansa. Allah ya biya masa buƙatarsa ​​kuma baya ga mutane, ya sanya aljanu, aljanu, iska da tsuntsaye a ƙarƙashin ikonsa. An gina wajen ibadar Sulemanu a lokacinsa kuma bisa ga umarninsa.


Kammalallen Tarihin Rayuwar Annabi Sulaiman (A.S)
Hoto: Nurmuhammad

MarubuciSaliadeen Sicey


Sulaiman ɗan Dawud, Dawud shi ne Sarkin Isra'ila mai hikima kuma Annabin Allah (S.W.T). Sulaiman ya koyi ilimi mai zurfi a wurin mahaifinsa kuma ya kan shiga wajen mahaifinsa a lokacin sauraren ƙararrraki, Ya kasance mai kallo kuma ya koya daga wurinsa kuma a wasu lokuta yana ba da gudummawa A wajen zartar da hukunci.


Zuri'a


Sulaiman (A.S) ɗan Dauda ne (A.S) kuma ya fito ne daga zuriyar Yahuda ɗan Annabi Yakub (A.S). Annabi Sulaiman (A.S) yana da farar fuska da ƙaton jiki. An haife shi da kaciya.


Annabi Sulaiman (A.S) shi ne magajin mahaifinsa bayan wafatinsa yana da shekara ashirin da biyu ko goma sha uku.


Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Dãwũda da Sulaimãn ilmi, kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya fĩfĩta mu a kan mãsu yawa daga bãyinSa mũminai."


Kuma Sulaiman ya gaji (ilimin) Dawuda. Ya ce: "Ya ku mutãne! An sanar da mu harshen tsuntsãye, kuma an bã mu dukan kõme. Lalle ne wannan, haƙĩƙa falala ce bayyananniya.


Kuma rundunarsa, daga aljannu da mutãne da tsuntsãye, aka tattara a wurin Sulaimãn, kuma aka jẽre su gabã ɗaya. (Karanta suratul An-namli 27:15-17).


Annabci da Mulki


Annabi Sulaiman (A.S) yana daga cikin manyan annabawan Banu Isra'ila kuma ya zama sarkinsu. 


Akwai ra'ayoyi da yawa game da zoben Sulemanu kamar yadda hadisi ya zo, Imam al-Mahdi (A.S) zai karɓa. Akwai kuma labarun camfe-camfe game da wannan zobe.


A zamanin Sulemanu (A.S), gungun mutane suna yin sihiri. Ya ba da umarnin a tattara dukan rubuce-rubucensu a ajiye a wuri na musamman. Bayan wafatin Suleman (A.S) sai wasu suka fitar da su suka fara koyarwa da wa'azin sihiri. Annabi Sulaiman (A.S) ya yi mulki tsawon shekaru arba'in. 


Iko da Mulki


Annabi Sulaiman (A.S) ya roƙi Allah da mulkin da babu wanda zai kama bayansa. Allah ya biya masa buƙatarsa ​​kuma ya sanya iska a ƙarƙashin ikonsa wadda ta yi nisa a cikin yini guda. Mutane da tsuntsaye da aljanu sun zama ƙarƙashin ikonsa. Yana ɗaure wasu aljanu marasa biyayya. Aljanu sun yi masa aiki kuma ya sami hanyar shiga ma'adinan zinariya.


Wajen Ibadar Sulemanu (A.S)


A bisa nassin Attaura, Allah ya yi wa Annabi Dauda (A.S) busharar gina wajen ibada mafi girma kuma mafi muhimmanci ga Yahudawa, “Gama sa’ad da kuka mutu aka binne ku tare da kakanninku, zan ta da ɗaya daga cikin zuriyarku. Zuriyarka, ni kuwa in sa mulkinsa ya yi ƙarfi, shi ne zai gina wajen ibada domin sunana, Zan kuwa tabbatar da gadon sarautarsa ​​har abada. Daga baya musulmi ne suka kira wannan wurin masallacin al-Aqsa (Kudus).


Halayen Maɗaukaki


Bayan mulki da iko mai girma, Allah ya bai wa Annabi Sulaiman (A.S) wasu gata;


Ayoyi da hadisai daban-daban sun ruwaito siffofi da yawa ga Annabi Sulaiman (A.S). Alkur'ani ya faɗe shi da bawan kirki mai yawan ambaton Allah kuma Allah ya ba shi ilimi. A cewar Kur’ani, Annabi Sulaiman (A.S) ya fahimci harshen dabbobi. 


A cewar wasu bayanin labarin Radd al-Shams ya faru ne ga Annabi Sulaiman (A.S). 


Littattafai na Misalai da Waƙoƙi an jingina su gare shi kuma duka biyun suna cikin littattafan Yahudawa masu tsarki.


Annabi Sulaiman (A.S) ya kuma yi hukunci. A cikin Alkur’ani an ambaci hukunce-hukuncensa. 


An ambaci sunan Sulaiman (A.S) sau goma sha bakwai a cikin Alkur'ani. Kur’ani ya ambaci labarai daban-daban game da Annabi Sulaiman (A.S), wanda ya fi shahara a cikinsu shi ne labarin Sarauniyar Sheba (Bilkisu Mai Gadon Zinare) Har ila yau, akwai labaru daban-daban game da shi a cikin hadisai, da yawa daga cikinsu masu bincike sun ce ba gaskiya ba ne da kuma ƙarin gishiri. 


Har ila yau, Kur'ani ya yi bayani ga kuskure na Sulaiman (A.S), bayan haka ya tuba. Allah kuma ya kira Sulaiman (A.S) 'Awwab' , wanda a zahiri yana nufin wanda ya sake komawa baya. Wannan yana nuni ne ga masu yawaita tuba zuwa ga Allah, kuma yana daga cikin mafi soyuwa a gare shi, wanda yake ba da lada mai yawa;


Kamar yadda Tafsir bn Kathir ya ce, a wata rana Sulaiman (A.S) yana kallon dawakan da suka ƙware sosai da nagartaccen kiwo, sai ya shagala da su, sai ya rasa lokacin sallar la'asar. Ya yi nadamar sha'awar kyawawan abubuwan duniya har ya manta da sallah ya rasa ambaton Allah. Sannan ya roƙi Allah gafara sannan kuma ya nemi yardar Allah.


Allah Ta’ala ya saukar da cewa: “ Kuma ga Dawuda Mun bai wa Sulaiman. Madalla da bãwa! Lalle shĩ, ya kasance mai yawan tũba."


Wata rana Suleman ya tara rundunarsa, ta bataliyoyin mutane, da aljanu, da tsuntsaye, da dabbobi daban-daban. Zai kai su ƙasar Askalon.


Suna wucewa ta cikin wani kwari, sai tururuwa ta ga rundunar da ke gabatowa, sai ta yi magana don ta gargaɗi sauran tururuwai: “Ku gudu zuwa gidajenku! Ga Annabi Sulaiman nan da rundunar sa. Annabi Suleman da jin wannan magana ta tururuwa sai ya yi murmushi. Ya yi murna da tururuwa ta san shi Annabi ne da ba zai cutar da halittun Allah da gangan ba. Ya godewa Allah da ya tseratar da rayukan tururuwai.


Allah Ta’ala ya ce: “ Kuma aka taru a gaban Sulaiman da rundunoninsa na aljannu da mutane da tsuntsaye, sai aka jera su gaba ɗaya. Har a lõkacin da suka je wa wani rami na tururuwa, wata tururuwa ta ce: "Yã kũ tururuwai! Ku gudu ku shiga rami ga Annabi Sulaiman nan da rundunar sa kada ya tattake ku."


Sai (Sulaimãnu) ya yi murmushi, yanã mai jin ni'ima da maganarta, kuma ya ce: "Ya Ubangiji! ayyuka na ƙwarai da za su faranta maka, kuma ka shigar da ni da rahamarKa a cikin bayinka salihai”. (Karanta suratul An-namli 27:17-19 Alƙur'ani).


A Urushalima, (Kudus) a kan wani ƙaton dutse, Sulemanu ya gina wajen ibada mai kyau don ya jawo mutane su bauta wa Allah. A yau ana kiran wannan ginin da sunan "The Dome of the Rock." Daga nan ne kuma wasu gungun mabiya da yawa suka bi sahun Sulaiman wajen gudanar da aikin hajji a Masallacin Harami na Makkah. 


Bayan sun kammala aikin hajji ne suka tafi ƙasar Yaman suka isa birnin San'a. Birnin ya burge Annabi Sulemanu ta ɓangaren dabarar su ta yadda suka bi da hanyar ruwa a dukan garuruwansu. Ya yi sha'awar gina irin wannan tsarin hanyar ruwan a ƙasarsa amma bai da isassun magudanan ruwa.


Sai Ya tashi ya ce a nemo Masa tsuntsun hoopoe (Al Hudahuda) wanda zai iya gano ruwa a ƙarƙashin ƙasa. Ya aika da sigina a ko'ina cikin jama'ar sa don a kira shi, amma ba a gan shi ba. A fusa ce ya bayyana cewa in dai tsuntsun ba shi da wani ƙwaƙƙwaran dalili na rashin zuwansa, zai hukunta shi hukunci mai tsanani.


Daga ƙarshe dai Al-Huda-huda ya zo wurin Annabi Suleman (A.S) ya na mai duƙar da kansa ƙasa cikin girmamawa, yana mai faɗin dalilin jinkirin sa ya ce "Na gano wani abu da ba ku sani ba, na je birnin Sheba (Sab'a) na dawo Muku da wani muhimman labari.


Annabi Sulemanu ya ce yana son ya sani, kuma ya huce fushinsa. Tsuntsun ya ci gaba da cewa: A “Sab’a Akwai wata katafariyar sarauniya mai suna Bilkis (Bilqis) da ke mulkinta, wadda ke da arziki mai yawan gaske, ciki har da wani ƙaton gadon zinare mai kyau, amma duk da wannan dukiya, Shaiɗan ya shiga zuciyarta da zukatan mutanenta. Ita ce take tafiyar da tunaninsu gaba ɗaya, na yi mamaki da na ga suna bautar rana ba Allah Ta’ala ba”.


Don Annabi Sulaiman Ya gaskata da wannan zance sai Sulemanu ya aiki Al Huda-huda da wasiƙa zuwa ga sarauniya Ya umurci tsuntsun da ya kasance a ɓoye kuma ya lura da komai.


Al Huda-huda yana tashi fir sai birnin Sab'a, sai fadar Bilkisu, yana shiga sai ya ajiye wasiƙar a gaban sarauniya ya tashi ya ɓuya. Cike da zumuɗi ta buɗe ta karanta: "Lalle daga Sulaiman yake, kuma haƙiƙa! Yana cewa: "Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin kai; muminai na gaskiya su ne waɗanda suka miƙa wuya.” (Ch 27: 30-31 Quran).


Sarauniyar ta shiga cikin damuwa sosai, ta yi sauri ta kira masu ba ta shawara. Don su mai da martani game da wannan ƙalubale, domin su ji cewa akwai wanda yake ƙalubalantarsu, kuma yana nuna musu zai yaƙe su sha kaye, Amma ya roƙe su, su yi biyayya ga sharaɗinsa.


Sai suka gaya mata cewa shawara kawai za su ba ta amma haƙƙinta ne ta ba da umarni a ɗauki mataki. Ta ce kuna so ku fuskanci barazanar mamayar Sulemanu da yaƙi? Don haka ta gaya musu: “Sulhu da abota sun fi kyau kuma sun fi hikima; yaƙi kawai ya kan jawo wulaƙanci, yana bautar da mutane, yana lalata nagarta. kyauta da sulhu kuwa za ta sa ta sami damar gano ko waye Sulaiman da jarumtakarsa, idan Annabi ne za ta fahimta idan kuma mai neman mulki ne za ta gane.


Shi kenan sarauniya Bilkis ta shirya mutanen ta da kayan dukiyoyi masu tarin yawa ta aika su zuwa wajen Annabi Sulaiman, domin su kai masa a matsayin gaisuwa domin ta jarraba cewa Annabi ne ko mai neman mulki da dukiya ne.


Tawagar Annabi Suleman sun je sun leƙo asirin labarin zuwan manzannin Bilkis da kyautar da aka aiko da ita kuma sun gaya wa Annabi Sulaiman, nan take ya ba da umarnin tara rundunar mayaƙa da tarin dukiyoyi kafin wakilan Bilkisu su kammala isowa. Da wakilan suka iso suka ga tarin runduna da dukiyoyi, sai suka gane cewa dukiyoyinsu ba komai ba ne kwatankwacin na daular fadar Suleman, wanda aka yi da itacen sandal da zinariya.


Sun lura Sulemanu ya leƙo asirin zuwansu sai suka yi mamakin yawan sojoji iri-iri, da suka gani, waɗanda suka haɗa da zakuna, damisa, da tsuntsaye. 


Sai manzannin suka tsaya cak a cikin mamaki, sun gane cewa suna gaban wata runduna ce da ba za ta iya tunkara ba.


Wakilan sun yi mamakin irin kayan ƙawan da ke kewaye da su. Suna ɗokin ba da kyauta da sarauniyarsu ta aiko su da ita kuma suka gaya wa Sulemanu cewa sarauniyar tana so ya karɓe su a matsayin sulhu. Abin da ya yi ya ba su mamaki: ko da yake bai nemi buɗe kyautar ba! Ya ce da su: "Allah ya ba ni dukiya mai yawa, da mulki mai girma, da Annabci. Don haka ni na wuce karɓar cin hanci, kawai burina shi ne in yaɗa imani da Tauhidi, da kaɗaita Allah."


Ya kuma umarce su da su mayar wa sarauniyar kyaututtukan kuma su gaya mata cewa idan ba ta daina irin ibadar da take yi ba zai tumɓuke mulkinta ya kori al’ummarta daga ƙasar.


Wakilan sarauniya sun dawo da kyaututtukan suka isar da saƙon. Sun kuma gaya mata abubuwan ban mamaki da suka gani. Maimakon ta yi fushi, ta yanke shawarar ziyartar Annabi Sulemanu da kanta. Sarauniya Bilkis ta bar Sheba tare da fādawanta da barorinta, ta aiki manzo ya faɗa wa Sulemanu tana kan hanyarta ya tarye/tarbe ta.


Annabi Suleman ya tambayi aljanu da ke masa aiki ko wani a cikinsu zai iya kawo masa gadon mulki kafin ta iso. Sai wani Aljani ɗaya daga cikinsu ya ce; "Zan kawo maka kafin a gama zaman nan."


Annabi Sulemanu bai mayar da martani ga wannan tayin nasa ba; ya bayyana cewa yana son akawo masa shi cikin sauri. Aljanu sun yi ta gwabzawa gasa da juna don faranta masa rai, wannan ya ce zai kawo nan da lokaci kaza, wannan ma ya faɗa. Can sai wani daga cikinsu mai suna Ifrit Ya miƙe tsaye ya ce: "Zan kawo muku shi a cikin ƙiftawar ido!"


Sai Ifrit Ya ce da Annabi Sulaiman ɗaga kanka sama sai ya ɗaga sai Ifrit ya ce sauke, Yana saukewa sai ga gadon Bilqis a gabansa Sulemanu lallai an kammala aikin kawo shi a cikin ƙiftawar ido. Kujerar Mulkin Annabi Suleman tana cikin Falasɗinu, ita kuma masarautar Bilqis ta kasance a Yemen, tafiyar mil dubu biyu. Wannan babbar mu'ujiza ce da ɗaya daga cikin waɗanda suke zaune tare da Annabi Sulemanu ya yi.


Lokacin da Bilqis ta isa fadar Annabi Sulaiman, an tarbe ta cikin fara'a da mutuntawa. 


Sai Sulemanu ya yi nuni ga gadon da aka ɗauko na Bilqis ya tambaye ta ko gadon ta da ta baro a Yaman ya yi kama da wannan? Ya kalleta, a ranta ta tabbata cewa lalle gadon nata ba za ta iya zama wadda take kallo ba, kasancewar nata yana cikin fadarta; da, ta gano kamanni mai ban mamaki kuma ta amsa: Sai tace "Kamar shi ne, kuma ya yi kama da nawa ta kowace fuska." Annabi Sulemanu ya tabbatar da cewa lallai Bilqis ta kasance mai hankali da iya diflomasiya.


Alkur'ani Ya ce:


TO A YAYIN DA TA ZO (FADAR ANNABI SULAIMAN ) SAI AKA TAMBAYE TA : KAMAR HAKA GADONKI YAKE? SAI TA CE ”YANA KAMA DA SHI”. TO ILIMIN DA AKA BA MU YA ƊARA HAKA, KUMA DUK MUN MIƘA WUYA GA ALLAH HAƘIƘANIN MIƘAWA”.


(Kur’ani sura ta 27 aya ta 42 ). 


Bayan ta gane cewa gadonta ne na mulki, sannan ta fahimci baiwar da Annabi Sulaiman ke da ita, sai ta shiga cikin ƙasaitacciyar fadar tasa. 


Daga nan ya gayyace ta zuwa cikin babban falo wanda aka shimfiɗa tiles da aka yi da gilas mai ƙyalli a zatonta ruwa ne, za ta shiga don haka ta ɗaga siket ɗinta sama saboda tsoron kar ta jiƙe kawai sai ta ji Annabi Sulaiman ya ce da ita: 


WANNAN AI FADA CE DA AKA GINA HANYOYIN TA DA GILASHIN KARAU “. 


(Kur’ani sura ta 27 aya ta 44) 


Alkur'ani ya ba mu labari cewa:


“ta dauka wani ruwa ne sai ta ɗage halliyarta [don ta ratsa ta]. Ya ce: "Lalle ne shi, gini ne mai santsi da gilashi." Ta ce: "Ubangijina! ( 27:44 ).


Ta yi mamaki, ba ta taɓa ganin irin waɗannan abubuwan ba. Bilqis ta fahimci cewa tana tare da wani mutum mai ilimi sosai wanda ba wai kawai mai mulkin babbar daula ba ne, shi ma manzon Allah ne. Ta tuba, ta bar bautar rana, ta yarda da imani da Allah, kuma ta nemi mutanenta su yi haka.


Bayan sun yi an gama ganawa: Bilƙis ta ga aƙidar mutanenta ta sauya a gaban Sulaiman. Sai ta gane cewa rana da mutanenta suke bautawa ba komai ba ce face ɗaya daga cikin halittun Allah.


A ranar hasken imani ya lulluɓe cikin zuciyarta da haskawa da hasken da ba ya gushewa, shi ne hasken Musulunci. 


Bilkis ta gane ashe masarautar Sulaiman ba kamar fadar da ta taɓa gani ba ce. Ta shaida hikimarsa da ƙasƙantar da kai tare da ƙarfin ikonsa kuma ta yarda da shi a matsayin manzon Allah. Ta tuba ta musulunta tare da al'ummarta.


Tarihin ziyarar sarauniya Bilkisu zuwa gurin Annabi Sulaiman, tarihi ne da ƙarshen sa ya zamo mai ban kaye sosai, inda a ƙarshe sarauniya Bilkisu ta ayyana da kanta cewa: 


” YA UBANGIJI NA LALLAI NA TAFKA KUSKURE (A BAYA) YANZU NA MIƘA WUYA GA ALLAH UBANGIJIN KOWA-DA-KOMAI, TA HANYAR ANNABI SULAIMAN”.


Kur’ani sura ta 27 aya ta 44.


A wata ruwayar an ce ta Aure Ta.


WAFATIN ANNABI SULAIMAN


Annabi Sulaiman ya rayu kuma ya yi mulki cikin ɗaukaka. Yawancin aikinsa na jama'a aljanu ne suka yi shi a matsayin hukunci don sanya mutane gaskata cewa aljanu ba su da ilimin gaibi. Sulaiman ya koya wa mutanensa cewa Allah ne kaɗai ya san irin wannan ilimin. Hatta wafatin Annabi Sulaiman ya zama darasi akan haka.


Aljanu ko annabawa ba su san makomar gaba ba, sai ga Allah shi kaɗai.


Sulaiman yana zaune riƙe da sandar sa, yayin da yake kula da wasu aljanu da ke aiki a cikin mahaƙar ma'adinai. Aljannun da suke tsoron Annabi sulaiman, sun mayar da hankali sosai kan ginin a lokacin da Allah ya yi niyyar ɗauke ran Annabi Sulaiman.


Ba wanda ya san mutuwarsa, sai bayan kwanaki, wata tururuwa mai yunwa ta fara lallasar/lasae sandarsa ta katako. Tana cikin ci sai sandar ta karye, gawar Annabi Sulaiman da ke jingine a kanta ta faɗi ƙasa. 


Mutane suka ruga wurin Annabinsu, nan da nan suka gane cewa ya rasu tun da daɗewa. Don haka kowa ya gane cewa da aljanu sun mallaki ilimin gaibi, da ba za su azabtar da kansu suna aiki tuƙuru ba, suna tunanin Sulaiman yana kallonsu. 


Rayuwa da mutuwar Sulaiman lallai suna cike da abubuwan al'ajabi waɗanda ɗan adam zai iya samun darussa masu ban mamaki daga gare su.


“Kuma a lokacin da muka wajabta wa Sulaiman mutuwa, babu abin da ya nuna wa aljani mutuwarsa face wata ƙwaro daga ƙasa tana cin sandarsa. To, a lõkacin da ya faɗi, ya bayyana ga aljannu cẽwa lalle ne dã sun san gaibi, dã ba su zauna a cikin azãba mai wulãƙantãwa ba. (Alkur'ani suratul Saba'i sura ta 34 aya ta 14 ).


Ya rasu a dhekara ta 931 kafin Haihuwar Annabi Isa (A.S) yana da shekaru 53 a duniya. 


MANAZARTA


Story of Prophet Sulaiman/Solomon (Pbuh) Na Ibn Kathir.


Don neman ƙarin bayani ku tuntuɓi IslamAwareness@gmail.com domin faɗaɗa bayani ko bincike.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user