Ki sani cewa ni masoyinki ne, ina ƙaunarki sosai ba zan iya misalta miki ɗaukakar matsayinki a raina ba. Ina son ki har cikin zuciyata.
Marubuci:- Sadeeq
Soyayyarki a daskare take cikin jinin jikina, a kodayaushe bugun zuciyata yana tafiya ne da mizanin adadin son da nake miki. Ina son ki har cikin raina.
A kodayaushe da shauƙin son ki da ƙaunarki nake kwana nake tashi.
Adadin fitar numfashina yana fitowa ne da furucin kalmar ina son ki.
Ina son ki yarda da cewa a rayuwata ba zan taɓa mantawa da ke ba koda mun rabu.
Gangar jikina za ta tafi da ƙwayar sonki da ƙaunarki.
Ina ƙaunarki ba zan so na ga ɓacin ran ki ba a rayuwata, ke kaɗai na ji ina so.
Tunaninki nake a kodayaushe, begen ki ne ya cika min zuciyata ko cikin barcina hoton fuskarki nake gani.