Siddhartha Gautama, wanda ya kafa addinin Buddhism ya rayu a cikin ƙarni na 5 BC.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
An haifi Gautama a cikin dangi masu arziki a matsayin basarake a ƙasar (Nepal ) ta yau amma daga baya ya yi watsi da dukiya da sarautar da yake ciki yayin da ya keɓe kansa tare da shiga duniya dan neman gaskiya.
Addinin Buddhism ya kasu gida huɗu amma duk tsarinsu da imaninsu ɗaya ne sai ɗan bambanci kaɗan.
Ɓangarorin da ya rabu su ne:
Buddha Theravada: a ƙasar Thailand, Sri Lanka, Cambodia, Laos da Burma.
Mahayana Buddhism: a China, Japan, Taiwan, Korea, Singapore da Vietnam.
Addinin Buddah na Tibet: Ya yaɗu a Tibet, Nepal, Mongoliya, Bhutan, da wasu sassan Rasha da arewacin Indiya.
BUDDAH-bangaskiya ne (imani) (faith) da Siddhartha Gautama ("Buda") ya kafa fiye da shekaru 2,500 da suka wuce a Indiya.
Mabiya
Ƙididdigar 2019 ta tabbatar addinin yana da mabiya kusan miliyan 470, masana sun rubuta addinin Buddah ɗaya daga cikin manyan addinan duniya. Ayyukansa a tarihi sun kasance mafi shahara a Gabas da Kudu maso Gabashin Asiya, amma yana ƙara girma a yammancin asiya.
Mabiyan addinin Buddha ba su yarda da wani Allah ko abin bautawa ba, a maimakon haka sun maida hankali ga samun wayewa, kwanciyar hankali da hikima.
Wanda ya kafa addinin, Buddha, ana ɗaukarsa wani halitta mai daraja da ƙima, amma ba Allah ba ko abun bauta.
Wasu masana suna bayyana Buddhism da cewa ba addini ba ne face wani tsari ne na tsara ingantacciyar rayuwa da kwanciyar hankali ga duniya baki ɗaya.
Manyan malamai (sufaye) na addinin Buddhism wanda ake kira da (Buddhist monks, or bhikkhus,) ƙarfafa al'adar nan ta rashin yin aure a kansu da kuma gudun duniya daga abubuwan ƙyale-ƙyale da sha'awa-shawan kayayyakin duniya.
Mabiya addinin Buddhism sun yi imani da zagayen haihuwa wato (Karma ko reincarnation) wato sake haifar mutum bayan ya rasu ta yadda zai dawo duniya a wani attajiri ko waliyyi ko wani babban shugaba ko attajiri idan ya yi aiki nagari zai iya dawowa kuma a matsiyaci ko wani masaki ko a dabba ma idan ya yi mummunan aiki ya dawo ya yi ta shan wahala a duniya gwargwadon zunubin da ya aikata.
Akwai adadi da yawa na hotuna da su ke nuna alamar wakiltar imanin Buddha, gami da furen (lotus,) (dharma ) mai magana takwas, bishiyar (Bodhi) da (swastika ) alamomi ne wanda sunan su ke nufin "lafiya" ko "Sa'a" a (Sanskrit).
Mene ne abinda addinin Buddhism ke umarnin aikatawa?
Zuzzurfan tunani, tsarkake ruhi da zahiri, da kyawawan halaye su ne hanyoyin samun wayewa, wato (nirvana).
Mene ne abin da addinin Buddhism ya haramtawa mabiyansa shi?
Ƙaurace wa kashe abu mai rai, sata, lalata (zinace-zinace), ƙarya da shan kayan maye.
Mai son ƙarin bayani ya nemi littafin Dhammapada na Eaknath Easwaran.