Sunan Jainism ya samo asali ne daga kalmar Sanskrit fi'ili ji, da ke ƙasar Indiya inda yake nufin "Don nasara." Yana nufin yaƙin da ake yi da zuciya don nasarar aikata kyawawan ayyuka, Jain (sufaye ) addinin yana koyar da mabiyansa cewa dole ne su yi yaƙi da sha'awa da ji na jiki don samun wayewa, ko samun tsarkin rai.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Mafi ilimin cikinsu da manyan malamansu ana kiransu Jina ( “Mai nasara”), masu bin wannan addini kuma ana kiransu Jain (“Mabiyan Masu Nasara”).
Jainism ya kasance addini a cikin ƙasar India kodayake ya ƙaura zuwa wasu ƙasashe, yawancin ƙasashen Commonwealth da kuma Amurka. Babu takamaiman ƙididdiga, amma an ƙiyasta cewa akwai Jain sama da miliyan shida, mafi yawansu suna zaune a Indiya.
Addinin yana koyar da tsarkin ruhi ta hanyar soyayya,tausayi, taimako ga dukkan abu mai motsi indai mutum yana kwatanta irin wannan shi ne suke kira wayayye.
Jains sun yi imanin cewa addininsu ba shi da wanda ya samar da shi ko ya kafa shi.
Mabiyin addinin Jainism na farko wanda akwai hujjojin tarihi shi ne Parshvanatha (ko Parshva), wanda wataƙila ya rayu a ƙarni na 7 KZ a ƙalla shekara dubu ashirin kafin haihuwar Annabi Isa, ya fara wannan addinin ne bisa ga watsi da ƙyaleƙyalen duniya.
Littattafan su masu tsarki na Jainism shi ne Agams ko Agam Sutras. Ya ƙunshi koyarwar Ubangiji Mahavir waɗanda almajiransa suka tsara ta hanyar Ilhama.
LAIFI
Manyan laifuffuka a addinin jainism su ne;
1. Ƙarya.
2. Sata.
3. Zinace-zinace.
4. Rashin cika alƙawari.
Da rashin kame kai.
Sannan sun yi imanin cewa duk wanda ya mutu ba ya aikata waɗancan ayyuka Ubangiji zai dawo da shi duniya a wani Basarake ko Mai Kuɗi ko wani Mai Cikakken Iko.
Idan kuma ka saɓawa hakan za ka iya dawowa duniya a matsayin Dabba ko Kare ko Jaki, ka yi ta shan wahala.
Sukan ajiye wani abu mai kama da ɗaki suna zagaya shi sanye da fararen kaya, duk shekara domin neman albarkar Ubangijinsu game da noma haihuwa, kiwo da sauran albarkatun yau da gobe.