Monday, 28 October 2024

Karanta Tarihin Rayuwar Socrates A Takaice

Tura Wannan Zuwa Ga

Socrates tsohon masanin falsafa ne na Girka wanda ake ganin shi ne tushen tunanin Yammacin Turai. An yanke masa hukuncin kisa saboda salon aƙidarsa sa ta Socratic.


Tarihin Rayuwar Socrates A Takaice
Hoto: Humanidades

MarubuciSaliadeen Sicey


A cikin 399 kafin haihuwar Annabi isa (A.S), an zarge shi da rashin adalci da lalata matasa. Bayan shari’ar da aka shafe kwana guda ana yi masa an yanke masa hukuncin kisa. Ya yi ranarsa ta ƙarshe a gidan yari, ya ƙi tayin taimaka masa ya tsere.


Wane ne Socrates?


Socrates masani ne, malami kuma masanin falsafa da aka haife shi a tsohuwar Girka. Hanyarsa ta koyarwar Socratic ta kafa tushen tsarin dabaru da falsafar Yammacin Turai.


A lokacin da yanayin siyasa na Girka ya juya masa baya, an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar shayar dashi guba a shekara ta 399 kafin haihuwar Annabi isa (A.S). Ya yarda da a zartar masa da wannan hukuncin maimakon ya gudu zuwa gudun hijira.


Shekarun Farko


An haife shi kimanin Shekaru 470 Kafin Haihuwar Annabi isa (A S) a Birnin Athens, na ƙasar Girka, rayuwar Socrates ta kasance ta hanyar tattaunawa da Plato da Xenophon da kuma wasan kwaikwayo na Aristophanes (Wani Marubucin wasan kwaikwayo na Girka).


Waɗannan da rubuce-rubucen su ne aka fi sani a tarihin sa, wataƙila babu wani wanda ya ba da cikakken tarihinsa.


Rubuce-rubucensa suna bada labarin sa na musamman da haske na falsafar Socrates da halayensa.


Socrates ɗan Sophroniscus ne, wani mai sana’ar sassaƙar dutse a birnin Athens, mahaifiyarsa wata ma'aikaciyar jiyya/jinya ce mai suna Phaenarete. Domin shi ba ɗan sanannen gida ba ne wataƙila ya sami ilimin Firamare, Sakandare, tare da ƙarin matakin gaba da sakandare don koyon sana'a. Kuma ya koyi sana’ar mahaifinsa tun yana ƙarami.


An yi imani cewa Socrates ya yi aiki a matsayin mai buga bulon dutse a shekaru da yawa kafin ya sadaukar da rayuwarsa ga falsafa.


Masana tarihi sun yi saɓani akan ta yadda Socrates ya zama masanin falsafa. Masana falsafa irinsu Xenophon da Aristophanes da Plato sun biya kuɗi don a koyar da su, amma Socrates ya ƙi amincewa da ya biya kuɗin, yana mai nuni da talaucinsa a matsayin hujja.


Socrates ya auri wata ƙaramar yarinya mai suna Xanthippe, wadda ta haifa masa 'ya'ya uku: Lamprocles, Sophroniscus da Menexenus. Duk wasu majiyoyin tarihi sun ce bai cika son ta ba.


Na farko matar tasa Xanthippe ba ta farin ciki da sana'ar Socrates, na biyu kuma ba ta yi ƙorafin cewa ba ya kula iyali a matsayin masanin falsafa ba. Ta hanyar kalmominsa, Socrates ba shi da alaƙa da tarbiyyar 'ya'yansa maza sai dai kawai ya fi nuna sha'awar ci gaba da ilimantar da sauran yara maza a birnin Athens.


Rayuwa a Athens


Dokar Athens ta buƙaci duk mazan da ke da lafiya da su yi aiki a matsayin sojojin ƙasa, ana ɗaukar sojoji daga shekaru 18 zuwa 60. A cewar Plato, Socrates ya yi aiki a cikin sojojin da ke ɗauke da makamai - wanda aka fi sani da hoplite - masu ɗauke da garkuwa, da dogon mashi da abin rufe fuska.


Ya shiga yaƙe-yaƙe guda uku a lokacin yaƙin Peloponnesia, a Delium, Amphipolis da Potidaea, inda har ya ceci rayuwar Alcibiades, wani mashahurin janar na Athenia.


An san Socrates don ƙarfinsa a cikin yaƙi, da rashin tsoro, halin da ya kasance tare da shi a tsawon rayuwarsa. Bayan shari’ar da aka yi masa, ya kwatanta ƙin ja da baya daga hukuncin shari’a, da yadda soja ya ke ƙi ja da baya daga yaƙi, sa’ad da aka yi masa barazanar kisa.


Plato ya ba da cikakkun bayanai game da kamannin Socrates na zahiri. Inda ya ce Gajere ne mai hanci kodayaushe idan yana magana yana lumshe idanu.


Duk da haka, Plato ya nuna cewa a idanun ɗalibansa, Socrates mutum ne mai kwarjini, saboda kyakkyawar muhawararsa da tunani mai zurfi.


Socrates a koyaushe yana jaddada muhimmancin hankali akan mahimmancin jikin ɗan adam, cewa hankali ya fi jiki. Wannan ra'ayi ya zaburar da falsafar Plato na raba gaskiya zuwa sassa biyu daban-daban, duniyar hankali da duniyar tunani, yana bayyana cewa na ƙarshe shi ne kaɗai mai muhimmanci.


Falsafa


Socrates ya yi imanin cewa ya kamata falsafar ta sami sakamako mai amfani don jin daɗin rayuwar al'umma. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin ɗabi'a bisa ga tunanin ɗan adam maimakon koyarwar tauhidi.


Socrates ya nuna cewa sha'awar farin ciki ne ya motsa zaɓin ɗan adam. Hikima ta ƙarshe tana zuwa ne daga sanin kai. Da zarar mutum ya sani, hakan zai sa ya ƙara fahimtarsa ​​da yin zaɓin da zai kawo masa farin ciki na gaske.


Socrates ya yi imanin cewa a fassara wannan zuwa siyasa tare da mafi kyawun tsarin gwamnati, ba ta azzalumai ko dimokuraɗiyya ba. Maimakon haka, aikin gwamnati mai adalci shi ne bada ilimi da nagarta, kuma ta sanya talakawanta su mallaki cikakkiyar fahimtar kansu.


Hanyar Socratic


Ga Socrates, Athens ta kasance aji kuma ya ci gaba da yin tambayoyi ga manyan mutane da talakawa, yana neman gaskiyar siyasa da ɗabi'a. Socrates baya yin lacca game da abin da bai sani ba. Hasali ma ya yi iƙirarin cewa shi jahili ne mai hikima, domin ya san jahilcinsa.


Ya na yin tambayoyi ga ’yan uwansa mutanen Athens ta hanyar Hanyar Socratic - Wani lokaci suna ba shi amsa daidai, hakan ya sa abokan hamayyar Socrates suke matsa wauta. tsarinsa na Socratic wasu sun yaba da shi, wasu kuma suka rinƙa yi masa ba'a.


A lokacin rayuwar Socrates, Athens ta sami canji mai ban mamaki saboda mulkin mallaka ta canja daga yadda take a gargajiyance zuwa tsarin mulkin Sparta da ta yi a yaƙin Peloponnesia. Mutanen Atina sun shiga wani lokaci na rashin kwanciyar hankali da shakku game da ainihin matsayinsu a duniya.


A sakamakon haka, sun koma son ɗaukaka da son dukiya, Socrates bai yadda da waɗannan ɗabi'un ba, tare da nacewa da jaddada mahimmancin hankali.


Shari'ar Socrates


A cikin 399 kafin haihuwar Annabi isa, an zargi Socrates da lalata matasan Athens da rashin kunya, ko kuma bidi'ar zuhudu. Duk da haka Ya zaɓi ya kare kansa a kotu. 


Maimakon kare kansa a matsayin wanda ake tuhuma da aikata ba daidai ba, Socrates ya bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa a matsayin mutumin da ya shahara wajen ɓata wa wasu rai, wanda ke da muhimmanci ga al'ummarsa ta hanyar ci gaba da yin tambayoyi da ƙalubalantar matsayi da masu kare shi.


Kariyar Socrates ba ta gamsar da alƙalan kotun ba kuma sun yanke masa hukunci ta hanyar kada kuri'u 221 a cikin 280.


Mai yiwuwa ne rashin kariyar da ya ƙi baiwa kansa ya taimaka wajen yanke masa hukuncin, kuma ya ƙara dagula al'amura yayin da ake tattaunawa kan yanke hukuncin.


Dokar Athens ta ba wa ɗan ƙasa da aka yanke wa hukunci damar gabatar da wani hukunci na daban ga masu gabatar da ƙara, su kuma su yi kira ga alƙalan da za su yanke hukunci da su canja. Maimakon ya ba da shawarar a fitar da shi zuwa gudun hijira, Socrates ya ba da shawarar a girmama shi a birnin saboda gudunmawar da ya bayar don wayar da kan su, kuma a girmama shi don ayyukansa.


Alkalin kotun ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar shayar dashi guba.


Tasiri


Socrates ya yi tasiri mai ƙarfi a kan masana falsafa a zamanin dā kuma ya ci gaba da yin hakan a zamanin yau. Malaman addinin musulunci na zamanin da, sun yi nazari akansa, sun jinjina masa akan rawar da ya taka a juyin juya halin Girka, musamman a cikin rayuwarsa ta gudun duniya, da ƙoƙarin sa na ganin an rage rayuwar ƙasaita ta almubazzaranci, da kuma wadatuwa da abinda ya samu.


Shin Socrates Ya Gaskata Ubangiji?


Socrates ya gaskanta da Allah, kuma tunaninsa ya bambanta da na Athens. Socrates ya gaskanta cewa Allah ya kasance mai kyau da hikima. Abin bautarsa ​​yana da kyawawan halaye. Ubangijinsa kuma yana da manufa. kyau da hikima. Abin bautarsa ​​yana da kyawawan halaye. Ubangijinsa kuma yana da manufa.


Mutuwar Socrates


Kafin a kashe Socrates, abokai sun ba wa masu gadi cin hanci don su cece shi ya gudu zuwa gudun hijira.


Ya ƙi, yana mai cewa ba ya tsoron mutuwa, yana jin ba zai fi jin daɗi ba idan ya tafi gudun hijira, kuma ya ce har yanzu shi ɗan ƙasar Atina ne mai aminci, yana son ya bi dokokinta, har ma da dokar waɗanda suka yanke masa hukuncin kisa.


Yayinda ya amince da shan guba a maimakon tsira
Hoto: VCG WILSON, CORBIS/GETTY

Plato ya bayyana hukuncin kisa na Socrates a cikin tattaunawarsa ta Phaedo : Socrates ya sha gubar da aka cakuɗa, ba tare da wani jinkiri ba, a hankali ta ratsa jikinsa har ta kai zuciyarsa. Jim kaɗan kafin numfashinsa na ƙarshe, Socrates ya kwatanta mutuwarsa a matsayin fitar rai daga jiki.


Ya mutu Shekara 399 Kafin Haihuwar Annabi Isa (A.S) yana da shekaru 71.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user