Malamai sun yi saɓani game da sharuɗɗan Zakkar amfanin gona. Imamu Abu Hanifa cewa ya yi, duk abin da ake shukawa a ƙasa don amfan da shi to akwai Zakka a kansa. In ban da itatuwa da ciyayi da karmami.
Shi kuwa Imam Ahmad sai ya ce, Zakka tana wajaba ne a kan duk abin da akan auna shi kuma ya kan bushe ya daɗe. Su kuwa Imamu Malik da Imamu Shafi’i, sai suka ce, zakka ba ta wajaba a kan amfanin gona sai wanda ake amfani da shi a matsayin abinci, kuma za a ajiye shi ya daɗe bai lalace ba.
Dangane da nisabi kuwa shi amfanin gona nisabinsa shi ne ya kai ‘wusuki biyar. Shi ‘wusuki’ ma’auni ne wanda kowanne ɗaya ya ke cin kwano sittin. Amma fa kwanon mai daidai da mudannabi huɗu. Watau a taƙaice dai idan aka ƙiyasta abin da aka noma aka ga zai kai kwano ɗari uku to ya wajaba a fitar masa da Zakka.
Game da abin da za a fitar kuwa, wannan ya danganta da irin ruwan da ya tsirar da amfanin. Idan da ruwan sama ya tsira, to sai a fitar da kashi ɗaya cikin goma. Idan kuwa ban ruwa aka yi, to sai a fitar da kashi ɗaya a cikin ashirin. Saboda faɗin Manzon Allah (S.A.W):
"فيما سقت السماء والعيون أو كان عثريا، العشر. وفيما سقي بالنضح نصف العشر".
“Abin da sama ta shayar, ko idanun ruwa, ko ya kasance mai jan ruwa ta jijiyarsa, to za a fitar da ɗaya cikin goma. Idan kuwa ban ruwa aka yi, sai a fitar da ɗaya cikin ashirin”. (Bukhari da Muslim suka rawaito.).