Ibn Sina, wanda aka fi sani a Yamma da sunan Avicenna, masanin ilimin lissafi ne na Farisa wanda ake ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin manya-manyan likitoci, masana ilimin taurari, masana falsafa, kuma marubuta na Zamanin Zinare na Musulunci (Islamic Golden Age), kuma uban likitancin zamani na farko.
Marubuci: Saliadeen Sicey
Shi ne wanda ya fara bayyana kamuwa da cuta, da yadda ake yaɗa wasu cututtukan ƙananan yara da ƙyanda. Na farko da ya bayyana cututtuka na gynecological, irin su: rufewar farji, fibroids da zazzaɓin cizon sauro.
Wane ne uban magungunan zamani na farko?
Ibn Sina, fitaccen likitan musulmi, masanin falsafa, babban mai tunani kuma mai hazaƙa ana ɗaukarsa a matsayin "Uban Magungunan Farko" kuma a matsayin "Uban Likitan Magunguna".
An san shi musamman don gudummawar da ya bayar a fagen falsafar Aristotelian da likitanci. Ya haɗa Kitāb al-shifāʾ (Littafin Magani), ƙaƙƙarfan encyclopaedia na falsafa da na kimiyya, da Al-Qānūn fī al-ṭibb (The Canon of Medicine), wanda yana cikin shahararrun littattafai a tarihin likitanci.
Daga cikin manyan malaman ilimin likitanci na Musulunci, Ibn Sina shi ne wanda aka fi saninsa a ƙasashen yamma. Wanda aka yi la'akari da shi a matsayin magajin Galen, babban littafinsa na likitanci, Canon shi ne ma'auni na littafin likita a cikin Larabawa da Turai a ƙarni na 17. Ya kasance masanin falsafa, likita, likitan ƙwaƙwalwa.
Haihuwa
An haife shi ne a shekarar 370 hijiriyya wanda ya yi daidai da shekara ta 980 miladiyya a garin Balkh da wancan lokacin yake ƙarƙashin lardin Khorasan na ƙasar Iran.
Tun yana ƙarami ya fara koyon karatun Alkur'ani mai girma da adabi inda kafin ya cika shekaru goma a duniya sai da ya yi karatu mai zurfi na Alkur'ani Mai Girma da kuma fannoni daban-daban na adabi da ya janyo hankulan malamai da masanan zamaninsa. Ya fara karatun Alkur'ani mai girma, fikihu, adabi da lissafi ne a wajen mahaifinsa daga nan kuma sai ya koma wajen wani malami mai suna Abu Abdullah Natali inda ya karanci ilimin mandik, handasa da ilimin taurari.
Daga nan kuma lokacin da ya yi nisa sosai sai ya koma yana bincike da kansa kan ilmummukan ɗabi'a da likitanci. Ibn Sina dai bai cika shekaru 16 a duniya ba sai da ya yi fice a ɓangaren ilimin likitanci.
Labarin irin fice da shaharan da ya yi ne a ɓangaren ilimin likitanci da magunguna dai ya mamaye garuruwa daban-daban, hakan ne ma ya sanya Sarki Bukhara na lokacin Nuh bn Mansur Samani da yake fama da wata cuta da ta gagari likitoci gayyatarsa don ya gwada nasa sa'an. Bayan wani lokaci kuwa ya yi nasarar magance wa sarki cutar da yake fama da ita. Hakan dai ya sanya aka buɗe masa shahararren ɗakin karatun garin don ci gaba da bincikensa.
Bayan wani lokaci dai Ibn Sina ya yi hijira zuwa Turkeministan da Khorasan sakamakon nemansa da ake yi a kama shi saboda ƙin amincewar da ya yi na yin magani wa sarki Mahmud Gaznawi da ya yi.
Haka nan kuma ya zauna a garuruwan Iran irinsu Gorgan, Rey, Isfahan da sauransu inda ya ci gaba da ayyukansa na magani. Bayan wani lokaci kuma ya koma garin Hamedan shi ma dai na Iran ɗin inda ya kama aikin gwamnati don ya sami abin sa wa a bakin salati. A wannan lokaci ne ya rubuta wasu daga cikin littafansa musamman shahararren littafin nan nasa mai suna ‘Al-Shifa'
A taƙaice dai Ibn Sina ya gudanar da dukkanin rayuwansa ne wajen neman ilimi da rubuce-rubuce a ɓangarorin ilimi daban-daban da ya zamanto tilo a zamaninsa.
Irin wannan zurfi cikin ilimi da ya yi ne ya sanya wata rana yake ce wa ɗaya daga cikin ɗalibansa mai suna Abu Ubaid Juzjani cewa: "Lokacin da na kai shekaru sha takwa zuwa sha tara a duniya na samu nasarar samun ilmummuka irinsu mandik, lissafi, handasa, ilimin taurari, waƙe, likitanci da sauran ilmummuka masu yawa, kuma a lokacin babu wani sabon abu da aka fitar da shi, don haka tun daga lokacin na rasa samun wani da zan ɗauke shi a matsayin malami na".
Irin ƙarfin haddace abubuwa da Ibn Sina yake da shi ya ba wa kowa mamaki, ta yadda hatta lokacin da gobara ta cinye ɗakin karatun sarkin Bukhara, jama'a suna cewa ai littafan ne kawai aka rasa amma duk abin da ke ciki yana kan Sheik al-Ra'is (wato Ibn Sina). Don haka ne ma ake kiransa da sunan Kundin Fannonin Ilimi.
Irin ilimi da ya ke da shi na likitanci ne ya sanya a ƙasashen Turai daga an kira sunansa abin da ke fara zuwa tunanin mutane shi ne likitanci. Sanannen littafin nan nasa kan likitanci mai suna ‘Kanun' ya zamanto abin da ake darasinsa a manyan jami'oin Turai har zuwa ƙarni na 19. Ibn Sina dai ya rubuta wannan littafi ne a lokacin yana ɗan shekaru 35 a duniya kuma an raba shi ne zuwa kashi ko ɓangarori guda biyar.
Ɓangaren farko ya yi ishara ne da alamun cututtuka, ɓangare na biyu na littafi kuma ya yi ishara ne da yanayin magunguna inda ya kawo kimanin sunayen magunguna kimanin 800. Ɓangare na uku kuwa na littafin ya yi magana ne kan cututtukan da suka shafi gaɓoɓin jiki da suka haɗa da idanuwa, kunne da sauransu. A ɓangare na huɗu na littafin Kanun kuwa Ibn Sina ya yi ishara ne da nau'oin zazzaɓi da yadda ake gano su da kuma magungunansu, hakan ne ma ya sanya da dama daga cikin masana suke kiransa da ‘Baban Gano Cututtuka'. Sai kuma ɓangare na ƙarshe wato na biyar na littafin inda ya yi bayani kan yadda ake haɗa magunguna.
Ibn Sina ya koma ga Mahaliccinsa ne a shekara ta 428 hijira kamariyya yana ɗan shekaru 58 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya a garin Hamedan kuma a can ne aka binne shi.