Assalamu alaiki ya ke wannar kyakkyawar da zuciyata ke bugawa da haruffan sunanta, kamar yadda kika sani cewa daidaiton kowacce gangar jiki a haɗa ta da ruhin ta to haka ni ma mahaɗin nawa farin cikin shi ne jin kyakkyawar amsar da za ta sanya annuri a cikin zuciyata saboda ke.
Marubuci:- Yaron MLM KD
Idan har yaƙinina ya zamto gaskiya a gare ki cewa kin tashi lafiya kamar yadda ni ma na tashi lafiya. To zan kasance mai matuƙar farin ciki da shauƙi na musamman.
Karɓuwar saƙona a gare ki shi ne karsashin da zuciyata za ta samu kamar yadda nake ji a sanadin ƙaunarki.
BARKA DA SAFIYA masoyiyata, abar ƙauna, shalelena, hubbina, sahibata, nurul ƙalbina, matata, farin cikina da annashuwata da shauƙina.