Thursday, 24 October 2024

Muhimmancin Bambance Sana'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Sana’o’i kaɗan ne suke tunƙaho da rashin kishiya a ɓangaren da suke. Mafi yawancin sana’o’i yanzu sun zagaye duniya, kuma kullum jama’a ƙara shiga suke, saboda haka gasa na ƙaruwa. Domin samun nasara, dole mai sana’a ya kawo wani abu daban wanda babu irin shi, kamar yadda wani gawartaccen ɗan kasuwar ƙasar Girka mai suna Aristotle Onassis ya ce “ya kamata ka san abin da babu wanda ya sani a kasuwa” domin yin fice da tserewa kishiyoyi.".


Sirrin nasara a kasuwanci shi ne ka san abin da babu wanda ya sani, ka yi fice a kasuwa
Hoto: Max4e/Freepik

MarubuciBello Galadanchi



KAWO SABON ABU CIKIN KASUWA IRIN WANDA BABU KAMAR SHI


A duk lokacin da mai sana’a yake fuskantar gasa, to dabarar da aka fi yi shi ne a yi ƙoƙarin bambance sana’ar daga ta abokan gasa. Wannan ya ƙunshi gabatarwa kwastomomi abin da ragowar abokan gasa ba su gabatar ba, ko kuma ba za su iya gabatar wa ba. A shekara ta 1940 ne wani fitaccen ɗan talla mai suna Rosser Reeves a Amurka ya ƙirƙiro wannan tsari domin nuna dalilin da yasa ake iya sayar da wasu hajoji da tsada idan aka kwatanta da kishiyoyinsu. Sabon abu irin wanda babu shi kuma wanda ya bambanta da ragowa na da wahalar ƙirƙirowa, kuma yana da wahalar kwafa – wannan shi ne dalilin da ke sa sana’ar ta yi fice. 


Dole sai mai sana’a ya bambance hajar sa daga ta kishiyoyi, kama daga kayan da ake haɗa hajar da su ko wajen da ake samo hajar, zuwa dabarun haɗa hajar da ma kula da jin daɗin kwastoma bayan ya sayi wannan haja. Kamfanoni kamar Nespresso da ke yin garin shayin kofi da Crocs masu yin takalman roba da ma sana’ar gidan cin abincin nahiyar Asiya mai suna Tune hotels sun bambanta kansu sosai daga kishiyoyin su kuma hakan ya ba su tagomashi mai ƙarfi a kasuwa. 


Babban alfanun bambance sana’a shi ne samun kwastomomin da ba za su je ko'ina ba, da kuma ikon sauya farashi a duk lokacin da ake so.


Bambance sana’a na kare sana’a daga kishiyoyi masu ƙaramin farashi; saboda bambancin na saka kwastoma ya amince da farashi na daban kuma hakan yana tabbatar da an samu riba a kowane lokaci, sannan hakan na bai wa sana’a tagomashin yin fice a kasuwa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user