Wednesday 30 October 2024

Saurin Yarda Da Jama'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk wanda muka haɗu da shi a rayuwata, ina yarda da shi 100%. Ina mutunta shi 100%, koda kuwa bai cancanci samun hakan ba. Ina ba shi amana 100%.


Saurin Yarda Da Jama'a
Hoto: Vmove 

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Ina gasgata furucinsa, koda kuwa ba gaskiya ba ne 100%.


Ina yi masa biyayya, koda kuwa na girme shi 100%.


Ina ba shi lokaci na 100%, koda kuwa bai dace da samun hakan ba.


Ina yin iyakar bakin ƙoƙarina a kan duk abin da muke yi tare da shi don ganin ba a samu matsala ba, sai dai da sannu zai sauya yardar da na yi masa, idan da ma can tun farko ba halinsa ba ne.


A hankali zai fara sa wa na yarda da cewa, shi maƙaryaci ne.


A kwana a tashi zai sa amintar da na yi masa tun farko ta kuɓuce masa, zai sa na dinga kallon sa a matsayin maci amana.


Girman da nake ba shi na yi masa biyayya ba don komai ba sai dai saboda girmama mutane ɗabi'a ce ta masu hankali, amma watarana da kanshi zai sa na daina girmama shi, idan har da ma can tun farko ba halin sa ba ne.


Mutunta shi da nake yi, a kwana a tashi, zai sa na daina mutunta shi yadda ya kamata, idan da ma can bai cancanci samun hakan ba.


Lokacin da nake ba shi, bisa tunanin cewa, yana da muhimmanci, kasancewar shi mutum, da sannu zai sa na daina ba shi lokutana, idan da ma can bai ɗauki lokaci a matsayin abu mafi muhimmanci a cikin rayuwar shi ba.


Da akwai abubuwa masu yawa idan na ce zan yi muku bayanin su.


Da yawan mu mu ne muke sa wa a daina aminta da mu, shi ya sa idan ka ga mutum yana tantama a kanka to kai ne ka sa hakan, haka kuma idan ka ga yana gasgata ka kai ne ka sa hakan, sai dai ba kowa ba ne mutumin kirki haka kuma ba kowa ba ne mutumin banza.


Allah yasa mu da ce, ya kuma zaɓa mana mafi alkhairi a cikin dukkan al'amuran mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user