Na ɗauki shekaru 10 kafin na koyi waɗannan darussan amma zan karantar da kai su cikin minti 1 kacal.
Ga darussa guda 10 da na koya a cikin rayuwa:
1. Rayuwa ba ta jiran kowa. Kullum ka wayi gari ka tabbatar ka ribaci wannan yinin/wunin ta hanyar yin abin da zai ciyar da rayuwarka gaba.
2. Ka kula sosai da kanka. Idan wani abu ya same ka, duniya za ta ci-gaba kai ko za'a bar ka a baya.
3. Idan ba ka yi aiki don gina rayuwar da kake so ba, wani zai ɗauke ka ƙwadago ka gina masa tasa.
4. Ka yi aiki cikin sirri sannan ka ɓoye nasararka daga idanun mutane. Ba kowa yake maka fatan alheri ba, wasu jira suke su ga faɗuwarka.
5. Ka bar ɓata lokaci saboda baƙin ciki akan abin da ya riga ya wuce. Amma ka ɗau darasi a cikinsa domin gyara gaba.
6. Babu wanda ya damu da kai. Kullum ka wayi gari, ka yi aiki fiye da na jiya domin inganta rayuwarka.
7. Ka bar karɓar shawara daga mutanen da ba su taka matakin da kake son takawa a rayuwa ba.
8. Dole ka fi ƙarfin motsin zuciyarka. Saurin fushi yana ba maƙiyanka damar yin galaba a kanka cikin ruwan sanyi.
9. Idan ka haɗu da wanda ya fi ka a rayuwa, kada ka yi masa baƙin ciki. Kai ƙanƙan da kanka ka koya daga gare shi.
10. Babu abin da zai haifar maka da kwanciyar hankali a rayuwa kamar barin abin da babu ruwanka.
Barkanmu da safiya!
Tushe/Asali: Hausa Motivation