Friday 11 October 2024

Sirrin Yadda Ake Kirkirar Sana'o'i Masu Kawo Riba Sosai

Tura Wannan Zuwa Ga

Ina da shawara ta ƙirƙirar sabuwar sana'a, yaya zan fara? Ka daidaita wannan shawara da kadarorin da kake da su a ƙasa. Misali, idan ka san yadda ake ɗinki, to sai ka yi tunanin wani sabon salo da tsarin ɗinka kaya ta yin amfani da shago da kuma keken ɗinkin wani wanda kake mutunci da shi, ko ya ba ka haya, har sai ka samu ƙwarewa, da fahimtar kasuwa da kuɗaɗen da za su ishe ka sayo naka keken. Kar ka yi garajen kama ƙaton shago da sayo kayan aiki nan take. 


Sirrin Yadda Ake Kirkirar Sana'o'i Masu Kawo Riba Sosai
Hoto: Getty Images

MarubuciBello Galadanchi


Ka fara da 'yar ƙaramar sana’a, sai ka girma a tsanake. Ka kashe kuɗaɗen da ba za ka gurgunce ba idan sana’ar ta karye, ko kuma albashin da kake samu na watanni uku a shekara.


Hakan zai ba ka damar gwada wannan sabuwar sana’a, ta yadda idan ka samu akasi, to ba za ka karye baki ɗaya ba, kuma za ka iya yin nazarin kuskuren da ka yi, sai ka sake gwadawa. 


Idan kana da fasaha, to kar ka ƙirƙiri abu daga farko, idan har akwai irin shi a kasuwa. Ka sayo na kasuwar, sannan ka nazarce shi, kuma ka yi tunanin yadda za ka inganta shi. Idan ka yi sa’a kuma ka samu alheri bayan inganta na kasuwa, to daga nan kuma za ka iya zuba jari mai tsoka domin ƙirƙirar naka sabon salon, a dai-dai lokacin da kake ci-gaba da samun kuɗaɗen shiga daga tsohon salon.


Ka zama kana da tarko mai inganci, yadda idan tsuntsun ya ƙwace, to ba zai gudu da tarkonka ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user