Monday, 28 October 2024

Tafiya Daidai Da Ra'ayin Kowa

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk irin yanayin yadda ka kai ga kyautata wa mutane, akwai dubban zukatan da sam ba sa yin farin ciki da kai, koda kuwa za ka zama jagora wajen cimma dukkan muradan rayuwarsu, haka kuma a ƙarƙashin zukatansu sam ba sa yi maka fatan alkhairi a iya tsawon rayuwarka.


Tafiya Daidai Da Ra'ayin Kowa
Hoto: Real people group/iStock photo

Marubuci:- M. Kabiru Muhammad


Haka ma duk yadda ka kai ga ƙuntata wa mutane, akwai ɗaruruwan zukatan bayin Allah waɗanda suke yin farin ciki da kai, kuma sam ba sa son ɓacin ranka, sannan kuma ba za su gushe ba face sun kasance suna masu yi maka kyakkyawan fata gami da kyautata maka zato, koda kuwa ka fi kowa hatsari a cikin rayuwar al'umma baki-ɗaya.


Shawara ta a gare ka: Kai dai komai za kai, ka yi shi da kyakkyawar manufa da zuciya ɗaya, don neman yardar mahaliccin ka, ba neman yardar wasu ƙatti ba. 


Sannan ka sa wa ranka cewa, ba za ka iya farantawa kowa rai ba, haka kuma ba za ka iya burge kowa ba.


Amma muddin ka ɗauki aniyar tafiya daidai da ra'ayin kowa, ba shakka ka ɗauki aikin da sam ba a iya kammala shi har abada, koda kuwa a tsakanin 'yan uwan ka ne ko kuma iyalanka.


Kai dai kawai, ka yi iyakar abun da za ka iya yi, wanda ba zai takura ka ba. Ka manta da irin yanayin zantuttukan da mutane za su yi a game da hakan. 


Watarana komai zai zama tarihi a cikin rayuwarka gaba-ɗaya!


Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sa dukkan Ibadun mu karɓaɓɓu ne, Ya kuma yi mana katangar ƙarfe da gurɓatattun mutanen cikin mu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user