Tuesday 22 October 2024

Tsantsar Sirrin Soyayya Da Ustaziyar Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Soyayya da Ustaziyar Asali sai an yi taka tsantsan na sosai, saboda abu kaɗan zai iya rikita tunaninta, ba komai ba ne face ta samu wani hali mummuna a tare da kai.


Sirrin Soyayya Da Ustaziyar Budurwa
Hoto: Amaani A/Pinterest

MarubuciyaFatima Zahra


Kar ka ce za ka dinga mata hirar abubuwan ƙyalƙyalin duniya, ko zancen kana da abin duniya, tunda dai ka san ita ba bin ka za ta yi ku je shaƙatawa ba, indai ba aurenta ka yi ba.


Wato soyayya da Ustaziyar Asali akwai wahala, saboda ita soyayya da ita ba kamar soyayya da 'yammata gama gari ba ne.


'Yammata gama gari za ka iya zuwa ka tsara su, har ka samu su shiga, su dinga washe maka baki, to ita kuma lamarin Ustaziyar Asali ba haka lamarin yake ba.


Kana fara magana kamar kana magana da Lauya ne, idan ba ka iya allonka ba a bugu ɗaya za ta ɓaro ka.


Ustaziyar Asali ba abin da ke kama zuciyarta sai gaskiyarka, tsoron Allahn ka, kyawun halinka, da kuma son ka da addini, sai kuma iya soyayya da kuma ƙwarewa wurin bayar da kulawa a aikace, da sauran ɗabi'u masu kyau, ba na tunanin bayan wannan Ustaziyar Asali za ta so ka don shi.


Na lura Ustaziya tana yin soyayya me tsafta idan ta samu wuri, kuma tana yin so me ƙarfi sosai, sai dai ba ta son namijin da ba irinta ba, duk namijin da ba irinta ba, da wuya ta so shi sai in ƙaddara, sai dai ta masa kara.


Idan tafiya ta yi tafiya, sai ta ji ba za ta iya kasancewa da kai ba, kuma tunda ba ta aure ka ba, gabaɗaya tanadinta ta fi son namijin da zai nuna mata hanyar Allah ko yaushe, wanda zai kula da ita, ya kula da 'ya'yanta, bayan hakan ba ta neman komai.


Allah yasa mu gama da duniya lafiya Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user