Laaaaa!
Idan da rai da rabo na shaida ba za a hana mini ke ba, samun ki shi ne farin cikina ya sa ba zan bijire ba.
A! Idan da rai da rabo na shaida ba a hana mini kai ba, samun ka shi ne babban buri ya sa ba zan bijire ba.
So ya saka mini babbar sarƙa babu dare ba rana.
Ni ke nake so a zuciyata ɗan saurari batuna.
Duka jama'a na faman magana.
Na bar ki fannin ƙauna, faɗi suke yi hauka nake yi ba za a auran ke ba.
Aaa! A zuciyata babban buri ka zamo angona.
Dan Kai ne mai sharen kuka ba ka damuna.
Da ni da kai mun zamma guda ɓoye mini sirrina.
Kowa yana ƙaunar ka gidan mu Umma da Abbanaa!
Komai wuyar so ni zan jure kar da ki sa ni a rana.
Ni ke nake wa zallar ƙauna.
Taso mu je hubbina.
Duk lokacin da na gan ki a raina.
Sai na ji ina yin murna.
Indai da rai na zam miki gata ba za ki sha wahala ba.
A! Idan da rai da rabo na shaida ba a hana mini kai ba, samun ka shi ne babban buri ya sa ba zan bijire ba.
Idan da rai da rabo na shaida ba za a hana mini ke ba, samun ki shi ne farin cikina ya sa ba zan bijire ba.
Lala! Komai za a faɗa mai sona, ban juya maka baya.
Don ka riƙe Allah da Ma'aiki, kuma ba ka yin ƙarya.
In muka rayu a tare da juna za mu yo soyayya, wacce ba a yi kamar ta ba yanzu har ma da can baya.
Son ki ya sa min babbar sarƙa nake rubuta wasiƙa, na ji mutane suna ta cewa hauka nake fa a kanki.
Na ji waɗansu suna ta cewa shirme nake fa a kanki.
Ni kuma ke ce zaɓin raina son ki ba zan gajiya ba.
A! Idan da rai da rabo na shaida ba a hana mini kai ba, samun ka shi ne babban buri ya sa ba zan bijire ba.
Idan da rai da rabo na shaida ba za a hana mini ke ba, samun ki shi ne farin cikina ya sa ba zan bijire ba.
A! Idan da rai da rabo na shaida ba a hana mini kai ba.
Samun ki shi ne farin cikina ya sa ba zan bijire ba.
Jarumi kuma mawaƙi Isa A. Isa tare da mawaƙiya Murja Baba ne su rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi ku. Musamman masoya.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.