Thursday, 10 October 2024

Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal (1)

Tura Wannan Zuwa Ga

Dakata ɗan uwa! Kamar jiya muka shiga shekarar 2024 amma ga shi har mun cinye rabinta. Shin za ka iya bugun ƙirji ka ce ga wani buri da ka cimma tsakanin farkon wannan shekarar zuwa yanzu? Idan babu, to lallai ka zauna ka yi wa kanka faɗa.


Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal
Hoto: iStock Photo

Mutane da dama sun taɓa tsintar kansu a irin wannan yanayin amma suka cimma nasara. Don haka ruwa bai ƙare wa ɗan kada ba tukunna.


In dai ka shirya canza rayuwarka, akwai hanyoyi da za su taimake ka a kan yin hakan.


Waɗannan matakan guda goma da za mu kawo za su taimake ku wajen samun sauyi mai inganci a rayuwarku.


1. Ka fahimci rayuwarka (Clarity).


Hausawa suna cewa: " Mai ɗaki shi ya san inda ke masa yoyo."


Mataki na farko kuma mafi mahimmanci shi ne ka yi wa kanka da rayuwarka farin sani.


Matsalar mafi yawa daga cikin matasa ita ce ba su san kansu ba, don haka a kullum suke faɗawa cikin ruɗani da damuwa.


Dole ne ka gane wane ne kai, tare da manufofinka, ƙalubalenka da inda rayuwarka ta fuskanta.


Ka amsa waɗannan tambayoyin:


- Mene ne mafarkinka a rayuwa?


- A wasu ɓangarori kake da ƙarfi?


- A wasu ɓangarori kake da rauni?


- Wasu matsaloli kake da su?


- Wasu ƙalubalai kake fuskanta?


Ɗaya daga cikin sirrin mutane masu nasara shi ne sun fi sauran mutane fahimtar kawunansu, sun san abin da za su iya da wanda ba za su iya ba, da ƙalubalansu a rayuwa.


Ka tuna cewa in dai ba za ka iya amsa waɗannan tambayoyin ba, to duk abin da za ka karanta a shafuka na gaba ba zai amfane ka ba.


Sai an gano cuta ake iya maganinta.


2. Ka ayyana manufofinka.


Idan ka san kanka, to dole ka san abin da kake so a rayuwa.


Ina buƙatar ka ɗauki alƙalami da takarda ka rubuce dukkan wani abu da kake so ka samu ko zama a cikin wata 6 masu zuwa.


Idan ba za ka iya rubuta abin da kake so ba, to ba ka san abin da kake so ba.


Masana sun bayyana cewa rubuce manufa tana da matuƙar amfani wurin tattara hankalin mutum a wuri ɗaya tare da zaburar da shi don ƙoƙarin cika burinsa.


Shi yasa wasu suka bada shawarar ka rubuce manufofinka a takarda ko allo, sannan ka liƙe su a jikin bangon daƙinka ko wani wuri da za ka riƙa ganin su a kullum.


Mu ɗauka kai tela ne, manufarka sai ta zama ƙwarewa a kan sana'arka da kuma samun ƙarin kwastamomi nan da wata 6.


Ka koma lamba ta ɗaya ka duba matsalolin da ka rubuta, da su za ka gane manufofin da ya kamata ka ayyana don wata 6 na gaba.


Manufofinka za su iya zama:


1. Inganta alaƙarka da Ubangiji.


2. Ƙwarewa a kan baiwarka, misali rubutu, koyon kwamfuta, graphics design, content creation, da sauran su.


3. Neman ƙarin ilimi kamar haddan Alƙur'ani, karance wani adadi na littattafai, da sauran su.


4. Inganta zamantakewa da matarka ko mijinki.


5. Samun cikakken lafiya a jiki, da ruhi, da tunani, da sauransu.


3. Ka yi watsi da shagala


A wannan matakin, ina so ka lissafa duk wani abu da ke shagaltar da kai wanda ke hana ka cika wannan burin naka.


Shin Soyayya ce?


- Kana ko kina ɓata kuɗade wurin fira da saurayi ko budurwa a kullum.


- Ku ƙarar da awa 3 ko sama a rana tsakanin yin waya da chatting.


- Shiga damuwa saboda rigingimu na soyayya ko dan ba'a son ka/ki.


Shin wayarka ce?


- Kullum kana salwantar da rabin yini/wuni a kan waya ba tare da ka san abin da ka mora ba.


- Kai ne Facebook, Instagram, Tiktok, WhatsApp, kuma kowanne sai ka hau ka duba a kullum.


- Ka tambayi kanka, shin waɗannan kafafe akwai wata gudunmawar da suke bayar wa ga rayuwarka?


- Ta yaya za ka yi amfani da su domin kusantar burinka da ka lissafa a lamba ta biyu.


Shin miyagun abokai ne ko ƙawaye?


- Ko a makaranta, ko a gida, ko a kasuwa, ko a wani wurin, kana da abokai da kake tasirantuwa da su ta wata mummunar hanya?


- Shin suna ba ka shawara ne mara kyau ko kuma suna tunzura ka wurin aikata abin da babu amfani?


Ka zauna ka gano dukkan abin da ke hana ka dagewa da yin zuzzurfan aiki a kan burikanka.


Shagala ita ce halaka.


4. Ka canza wani abu da kake yi a kullum


To yanzu mun gama da ɓangaren fahimtar kai, da zayyano matsaloli da ƙalubalenka.


Idan ka iya kammala waɗancan matakan, daga na 1 zuwa na 3, to lokacin ɗaukar mataki ya yi.


Amma a nan ne, mutane da yawa suke gazawa.


Ai da ma magana ta fi komai sauƙi, aiki shi ke da wahala.


Idan ba za ka iya samar wa kanka da sauyin da rayuwarka take buƙata ba, za ka ci-gaba da rayuwa ne a cikin nadama.


DUBA WANNAN: Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal  (2)


Don haka ka shirya yaƙar dodanni da yawa idan kana son tsallake wannan matakin.


Amma waɗanne dodanni kenan?


Mu haɗu a fitowa ta biyu (2) da yardar Allah.


A karanta a yaɗa ga 'yan uwa.


Allah ya sa mu gudu tare mu tsira tare ɗan uwa.


Muna godiya da gudummawarku, Allah ya saka da alheri.


Da fatan za ku amfana da saƙonninmu a wannan shafin, ku ma ku gayyato abokanku don su ma su amfana.


Za mu ci-gaba Insha Allah.


Tushe/Asali: Hausa Motivation

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user