Saturday 12 October 2024

Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal (2)

Tura Wannan Zuwa Ga

Mun fara bayani a kan matakai goma da za su canza rayuwarka a cikin wata 6. Mun tattauna daga matakai na 1 zuwa na 3. Ya kamata mai karatu ya maida hankali a nan sosai, saboda a nan babban aiki yake.


Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal
Hoto: Protofuse

4. Ka canza wani abu da kake yi a kullum.


Masana suna cewa sirrin nasararka yana ɗauke a cikin tsarin yininka/wuninka (daily routine).


Bi ma'ana abin da kake yi kullum a rayuwarka daga safiya zuwa dare.


Ka tambayi kanka mana, ta yaya kake tafiyar da lokacinka, daga farkawarka daga barci har zuwa lokacin komawa shimfiɗarka?


Lokaci kam babu mai ja da muhimmancinsa saboda Allah da kanSa ya rantse da shi fiye da sau 10 a cikin Alƙur'ani Mai girma.


Allah ya rantse da Alfijir, Ya rantse da lokacin Asuba, Ya rantse da lokacin hantsi, Ya rantse da yini/wuni, da kuma dare, sannan Ya rantse da zamani gabaɗayansa.


To amma ta yaya za ka gano abin da za ka canza na tsarin yininka/wuninka?


Ka koma ka binciki waɗannan abubuwan:


1. Matsalolinka da ka zayyano a mataki na farko, da....


2. Manufofin da ka ayyana a mataki na biyu da kuma...


3. Abubuwan da suke shagaltar da kai da ka lissafa a mataki na uku (No.3).


Idan ka gano waɗanan gabaɗaya, to akwai wani GAGARUMIN AIKI a gabanka.


A nan ne za ka yi amfani da wani tsari na Rusau da Ginau mai muhimmanci.


RUSAU


1. Ka rusa, ka zare, ka goge, ka gusar, ka kawar da duk wata ɗabi'a, ko hali, ko shagala, ko yanayi, ko aiki, ko mutumin da ba ya ƙarfafa ka wurin isa ga burinka da ka ayyana a lamba ta 2.


A wannan matakin, za ka rabu da abokai da kuke zaman banza tare da su ba kwa tattauna wani abu na ci-gaba ko fa'ida a rayuwa.


Za ka rabu da budurwa/saurayi da kuke yaudarar juna, kuna ɓatawa juna lokaci da rayuwa alhali kun sani sarai ba auren juna za ku yi ba.


Za ka rabu da kallon fim, ko ka ba shi hutu, za ka rage hawa kan shafukan sada zumunta, idan so samu ne ma ka goge manhajojin (Apps) daga wayarka sai wanda ya zame maka tilas.


Idan ya zama dole sai ka hau shafukan sada zumunta don wani dalili, 


To ya zama dole ka yi;


- "unfollowing"


- ko "blocking"


- ko "unfriending" duk wani mutum ko shafi da ba ya bada gudunmawa wurin ci-gaban kanka da tunaninka, da sana'arka, ko iliminka, ko imaninka, ko auratayyarka da sauransu.


Dole ki yi blocking duk wani shashasha da bai san ciwon kansa ba yake zuwa inbox yana damunki da saƙonni na shiririta da shirme. Yin hakan taimakon kanki ne da ma shi kansa.


Dole ne ka rabu ka ja da baya da masu kashe maka gwiwa a kan manufofinka waɗanda komai ka ɗauko sai su ce maka ba zai yiwu ba.


Dole ki nisanta kanki daga duk wata ƙawa ko 'yan uwa masu kashe miki gwiwa akan sana'arki ko kasuwanciki ko aikin hannunki da kike rufawa kanki asiri a sanadinsa.


GINAU 


Idan ka kawar da dukkan waɗannan sai ka musanya su da ɗabi'u, da halaye, da ayyuka, da mutane masu taimakonka da ba ka ƙarfin gwiwa.


Amma kamar yadda na faɗa a baya, mutane da yawa ba za su iya wuce wannan matakin ba.


Sun gwammace su ci-gaba da wanzuwa a cikin yanayin da suke na rashin ma'ana, da salwantar da lokaci, da kasancewa tare da mutane masu hana su ci-gaba, da kuma riƙo da munanan ɗabi'unsu masu wuyar bari.


Idan ba za ka iya samar wa kanka da sauyin da rayuwarka take buƙata ba, za ka ci-gaba da rayuwa ne a cikin nadama.


Shi yasa muka yi alƙawarin yin bayani a kan wasu dodanni da dole mutum ya yaƙa domin wuce wannan matakin.


Su ne kamar haka:


1. Sabo


Na farkonsu kuma mafi illa a cikinsu shi ne sabo, wato abin da rai ko jiki ko zuciya ta saba da shi tsawon wata da watanni ko ma shekaru, rabuwa da shi ya kan yi mata matuƙar wahala.


Don haka dodo na farko kuma yaƙi na farko da za ka gwabza shi ne ka yaƙi kanka da kanka.


Ka ɗauka kamar mutum ne kai wanda ya daɗe yana cin wani abinci mai daɗin gaske amma kuma yana ɗauke da guba a ciki.


Shin daɗin wannan abincin da tsawon lokacin da ka ɗauka kana cin shi dalili ne da zai sa ka bar abincin ya kashe ka?


2. Tsoro


Dodo na biyu shi ne tsoro.


Shin hakan ma zai yiwu kuwa?


Shin zan iya yin nasara? Zan iya rayuwa idan babu wane da wance?


Akwai wani babban mutum da ya taɓa yin wata magana wacce har ila yau ta tsaya mini a rai. Yana cewa, "Mutane da yawa ba gazawa (failure) suke tsoro ba, nasara (success) suke tsoro."


Sai ka ga mutum cikin tsananin talauci ko sisi ba ya da shi, amma idan ka kawo masa wata dama ta aiki ko sana'a sai tsoro duk ya bi ya kame/kama shi.


Shin akwai wani abun tsoro ne dama da talauci, amma yin kuɗi yake tsoro ba talauci ba.


Mutum yana soyayya da wata tana matuƙar cutar da shi, ko yana wulaƙanta ta idan mace ce, amma yana ko tana tsoron rabuwa da su.


Za mu ci-gaba Insha Allah.


Tushe/Asali: Hausa Motivation 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user