Friday 18 October 2024

Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal (3)

Tura Wannan Zuwa Ga

Shawara


Domin fahimtar inda aka dosa dole sai mutum ya koma baya daga fitowa ta biyu (2). Latsa nan don komawa ga fitowar da ta gabata.


Sauya rayuwa a watanni 6
Hoto: Legends recovery

Kun san me yasa ne wai?


Ba damuwa take tsoro ba, kwanciyar hankali take tsoro.


Haka da yawa sai ka ga maƙasƙanci amma yana tsoron ɗaukaka.


Ka ga mara lafiya yana tsoron zuwa ganin likita.


Mai ƙaramar sana'a yana tsoron barin ta zuwa babba. Haka dai, haka dai.


3. Tsoron ra'ayin mutane


Ɗan Adam kenan, sau da dama ɗabi'arsa ce take cutar da shi saboda bai iya sarrafa zuciyarsa ba.


Yana rayuwa cikin ruɗani saboda yana tsoron tunkarar zahiri.


Kana tsoron mutane su ƙalubalance ka ko su yi mamakin ganin sauyi a cikin yanayin ka.


Babu abin da yake janyo haka face ruɗar kai da rayuwar ƙarya.


Kana tsoron ka koma makaranta saboda ana ganin ka a matsayin mai ilimi?


Kana tsoron ka fara neman kuɗi saboda abin da wasu za su yi tunani, amma fa ka san cewa kai talaka ne?


Kana tsoron rabuwa da su saboda kada su ga ka ɗauki hanyar ci-gaba a rayuwar ka?


To amma fa ka san ba ku ƙarar da juna wani abu mai amfani a rayuwa ba.


Mafita anan shi ne;


1. Ka fifita kanka a kansu. Idan abin da za ka yi zai taimaki rayuwar ka, ina ruwan ka da tunanin wani?


2. Ka yarda da gaskiya, ka bar ɓoye-ɓoye da ruɗar kanka.


Kai talaka ne, kai talaka ne.


Ba ka da ilimi, to ba ka da ilimi.


Ka yanke hukuncin ciyar da rayuwarka gaba. Don haka ba za ka iya mu'amala da su ba shikenan.


Shi sabo yana gwada juriyar ka ne da jumurin ka.


Mai jumurin yin haƙuri ne kawai zai iya rabuwa da wata ɗabi'a ko wani mutum da suka daɗe a tare da juna.


Shi kuma tsoro, yana gwada bajintar ka da ƙarfin halin ka da imanin ka.


Idan kana da bajinta da sadaukarwa, za ka ci galaba a kan dukkan wani tsoro da ya bijiro ga tafarkin ka.


Amma tsoron ra'ayin mutane, yana gwada son da kake yi wa kanka ne, da yarda da kanka da kuma damuwar ka a kan goben ka.


Idan kana son kanka, kuma ka damu da goben ka ta yi kyau, za ka daina damuwa da ra'ayoyin mutane game da rayuwarka.


Akwai wasu dodanni ban da waɗannan, amma guda ukun nan sun fi tsoratarwa da kawo cikas ga mutane.


Mun gama da bayanin Rusau saura na Ginau.


Mu haɗu a fitowa ta gaba da yardar Allah, inda za mu tattauna yadda ake gina sabon hali ko ɗabi'a da yadda mutum zai canza rayuwarsa da gaske ta hanyar aikinsa.


Babu rayuwar da za ta zo gare ka face rayuwar da ka ginawa kanka ita. Makomar ka a hannuwan ka take!


Turawa wani da ka san yana buƙatar wannan saƙon.


Da fatan kun ji daɗin wannan saƙon? 


Ku ci-gaba da bibiyar mu don samun saƙonni masu zaburarwa da za su inganta rayuwar ku a cikin harshen Hausa.


Za mu ci-gaba Insha Allah.


Tushe/Asali: Hausa Motivation 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user