Tuesday, 22 October 2024

Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal (4)

Tura Wannan Zuwa Ga

Canji abu ne mai sauƙin faɗa, sai dai samar da shi yana da matuƙar wahala, amma kuma sakamakonsa akwai daɗi ƙwarai da gaske. Domin fahimtar inda aka dosa dole sai mutum ya koma baya daga fitowa ta farko (1). Latsa nan don komawa ga fitowar farko.


Ka fita daga sabgar mata
Hoto: Damir Khabirov/iStock photo 

5. Ka tarbiyantar da kanka akan tashi barci da wuri.


Wannan ɗabi'a ce mai ƙololuwar tasiri sannan mafi yawancin manya-manyan mutane suna siffantuwa da ita.


Ka daidaita yininka/wuninka ta yadda za ka kammala duk wani aiki naka ka kwanta kafin 10:00 PM na dare, sannan ka tashi ƙarfe 4:00 AM na safe.


Hakan zai ba ka ƙarin awanni guda 2 zuwa 4 kafin yinin /wunin wasu ya fara. Wannan lokacin zai ba ka damar shiryawa yininka/wuninka da kyau, yin karatu, motsa jiki, ko ibada da addu'o'i.


Duk rintsi kada ka bari ƙarfe 5:00 AM ta asuba ta wuce kana kwance. Rayuwa guda ɗaya kake da ita, ta yaya za ka yi barcin sama da ɗaya bisa ukunta (1/3)?


6. Ka yi watsi da shagala.


Na yi bayani game da shagala a gaɓa ta uku. Maganar gaskiya ita shagala tana da nau'o'i daban-daban masu wuyar lissafawa.


Amma ina so ka gane cewa duk lokacin da ka fuskanci manufarka kake ƙoƙarin hawa tafarkin nasara, akwai wasu ƙugiyoyi da za su riƙe ka su ƙanƙame ka.


Duk wani abu da zai tauye ko ya salwantar maka da ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da zan lissafa, to ba za ka isa ga manufarka ba sai ka yi watsi da shi:


- Lokaci (Time).

- Tunani (Attention).

- Kuɗi (Money).

- Sha'awa (Lust).

- Lafiyar Jiki (Health).


To ka matso kusa ka ji ɗan uwa.


Idan har ka damu da daidaita al'amuran rayuwarka, to dole ne;


- Ka fita daga sabgar mata, soyayya ba taka ba ce.


- Rayuwar ƙarya da ƙoƙarin burge mutane ba naka ba ne.


- Kalle-kallen TV da yawan hawa shafukan sada zumunta ba naka ba ne.


- Al'amurra masu tashe ko yayi (trends) su bar ɗaukar hankalinka.


- Bibiyar labaran yau da kullum da al'amuran siyasa bai da amfani gare ka.


- Shaye-shaye zai sa ka yi baƙin jini a cikin mutane, ka mutu a wulaƙance sannan ka haɗu da fushin Ubangiji.


Waɗannan abubuwan dukkaninsu guba ne da suke cutar da kai. Ka gaya min mene ne amfanin karantawa ko kallon labarai a rayuwarka?


A yau dai kam mai karatu na ƙalubalance ka, ka cire dukan waɗancan abubuwan da na lissafa daga rayuwarka.


A cikin wata 6 masu zuwa, kawai ka maida hankali akan gina kanka ta kowacce fuska.


Ka gina jikinka ta hanyar kula da lafiyar jikinka.


Ka gina ilimi da basira ta hanyar koyo, bincike, da karatu.


Ka gina alaƙa mai kyau da mutane masu himma da za ka amfana da su.


Ka gina aljihunka da asusun bankinka domin ganin ka fi ƙarfin buƙatun yau-da-kullum.


Ka samu gogewa da ƙwarewa ta hanyar maida hankali akan abu guda 1 tsawon watanni 6.


Idan ka ɗauki waɗannan abubuwa da muhimmanci, tabbas rayuwarka za ta canza na har abada.


7. Ka gina jiki mai ƙarfi.


Dole ne kana buƙatar ka zama mai cikakkiyar lafiya da ƙarfi na gangar jiki domin ka iya aiki da gaske don cikar burinka.


Nawā, kasala, gajiya, ragwanci, da son jiki, duk waɗannan ba abin da ke janyo su face raunin jiki.


Idan kana so ka ci nasara a gwagwarmayar rayuwa, dole sai ka zama jarumi. Shi kuma jarumi ba'a samun sa da rauni a ko'ina.


Zuciyarsa tana da ƙwari kamar yadda gangar jikinsa take da ƙarfi.


Don haka bayan ka gina jarumtaka ta zuciya ta hanyar yarda da kanka, neman ilimi, rashin tsoro da sauran hanyoyi da muka ambata, dole kuma ka gina gangar jiki mai ƙarfi don zama cikakken jarumi.


A kullum, ka ware aƙalla minti 30 zuwa awa ɗaya domin motsa jiki da aikata ayyukan da za su ƙarfafa gangar jikinka.


8. Ka doge/dage da koyo da neman ilimi.


Abokina ka nemi ilimi, ba za ka taɓa zama sama da abin da ka sani ba a rayuwa.


A kullum ka ware a mafi ƙaranci, minti 30 zuwa awa 1 domin karanta aƙalla shafi 10 zuwa 20, da za su gina maka ƙwaƙwalwa sannan su haɓaka tunaninka da basirarka.


Karatu ne kaɗai zai ba ka damar koyon tajriba/ƙwarewa da gogewar da mutane suka samu a tsawon rayuwarsu cikin yini/wuni ɗaya ko 'yan kwanaki.


Daga ranar da ka daina neman ƙarin ilimi, rayuwarka za ta fara daskarewa ta daina ci-gaba.


Ina so ka amsa wa kanka waɗannan tambayoyin;


1. Littafai nawa ka karanta daga farkon shekarar nan zuwa yanzu?


2. Sau nawa kake zuwa majalisi a mako ko kake sauraren karatuttukan malamai?


3. Yaushe ne ƙarshen lokacin da ka halarci wani taro na ganawa da musayar ra'ayi tsakanin masana?


4. Kwasa-kwasai nawa ka koya daga yanar gizo domin gina kanka a wannan shekarar?


5. Akwai bambanci a iliminka da ƙwarewarka da gogewarka tsakanin shekaru 3 baya zuwa yanzu?


Daga sanda ka zama mai ƙoƙarin karance-karance, rayuwarka za ta fara bambanta da ta sauran jama'a.


Babban ƙalubalen da ke hana mu samun ci-gaba a rayuwa ba komai ba ne face jahilci.


Akwai ƙwarewa da dabarun kasuwanci na zamani da hanyoyin neman kuɗi da yawa da za su inganta rayuwarka, amma ta yaya za ka san su idan ba ka neman ilimi?


Ina so ka nutsu ka zaɓi wata ƙwarewa (skill) ko fage guda 1, ka tattara hankalinka akan sa tsawon watanni 6.


Idan kai ɗan kasuwa ne, ka dage da koyon ilimin kasuwancin zamani, ka san kasuwancin da kake yi a ilimance, sannan ka nemi ilimin haɓaka kasuwanci (business development).


Ko ka yarda ko ba ka yarda ba, ilimi shi ne zai iya magance maka duk wani talauci da ke damun ka.


Talauci sakamako ne na ƙaramin tunani da jahiltar hanyoyin neman kuɗi, shi yasa wasu masana suke cewa, "Iya yawan saninka, iya yawan samunka.".


DUBA NA GABA: Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal  (5)


Ilimi shi ne zai wayar maka da kai ya buɗe idanunka ga abin da ba ka sani ba, sanann ya nuna maka hanyoyin aikata abin da mara wannan ilimin bai isa ya yi ba.


Ku biyo mu  a fitowa ta gaba domin karanta  mataki na 9 zuwa na 11. Kuma na ƙarshe a cikin jerin matakan sauya rayuwa a wata 6 kacal.


Ku ci-gaba da bibiyar shafin nan namu domin ci-gaba da samun saƙonnin da za su taimaki rayuwar ku tare da  taimaka muku ga cimma burin ku da muradin ku cikin sauƙi duk a kyauta. Za ku iya sanar da sauran mutane sunan wannan shafin domin su ma su shigo su amfana kamar yadda ku ma kuke amfana.


Tushe/Asali: Hausa Motivation

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user