Friday, 25 October 2024

Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal (5)

Tura Wannan Zuwa Ga

9. Ka bar Jinkirtar da mafarkanka.


A duk lokacin da ka jinkirtar da wani mafarki naka, kana jinkirtar da damarka ne da nasararka, da rayuwarka gaba-ɗaya.


Tafiyar mil dubu tana farawa ne da taku ɗaya
Hoto: Liubomyr Vorona/iStock photo


Ita ɗabi'ar jinkiri kamar maƙabarta ce ga mafarkan mutum. Tana binne burikanka ne ta bar ka da nadama a gaba.


Duk abin da za ka aikata to ka aikata shi a yau kuma a yanzu, kada ka tsaya jiran gobe ko jibi.


Ina so na yi maka wata tambaya kamar haka:


Daga lokacin da ka fara karanta wannan rubutun tun fitowa ta ɗaya zuwa yanzu wasu matakai ka ɗauka?


Na san ƙila wannan rubutun ya ƙayatar da kai, ya ratsa ka sosai, ƙila ma ka adana shi don son karantawa a gaba.


To amma fa ina so in tunatar da kai cewa hakan bai da amfani idan ba za ka ɗau mataki ba. Don haka ka fara ɗaukar mataki domin aiwatar da duk wani abu da ka karanta a cikin wannan saƙon.


Shekara ɗaya daga yanzu za ka so ina ma ka fara aiki don cikar burinka a yau.


Wasu da dama ba rashin ilimi ko ƙwarewa ba ce matsalarsu, kawai ba za su iya ɗaukar mataki ba ne don samar da ci-gaba a rayuwarsu.


Illar jinkiri ita ce duk abin da kake jinkirtar da shi za ka ci-gaba da ganin wahalarsa ne shi kuma yana ƙara yi maka nesa yana ƙara ba ka tsoro.


Jinkiri yana sa abubuwa masu sauƙi su zama masu wahala, kuma abubuwa masu wahala su zama marasa yiwuwa. Ɓoyayyen maƙiyi ne ga nasara.


10. Ka gina kyawawan ɗabi'u.


Farawa ya fi komai wuya, amma hakan ba ya nufin da ka fara shikenan ka haye.


Wasu da yawa sun fara amma daga baya suka sare, sun ɗauko tafarkin cim ma nasara amma daga ƙarshe suka watsar suka koma gidan jiya.


Ya kamata ka gane cewa fafutukar canza rayuwarka wata gwagwarmaya ce da dole za ka yi ta kai kaɗai, babu wanda zai iya shigewa gaba ya tare maka wannan faɗan.


A don haka ne kake buƙatar wasu ɗabi'u da za su zamanto abokan tafiyarka kuma domin su isa ga manufarka.


Waɗannan ɗabi'u su ne kamar haka:


A. Maida Hankali (Focus).


Kada ka ce za ka zamo komai da ruwanka, ita rayuwa ba haka tsarinta yake ba.


Kowane gwani yana da fagen gwanintarsa, kuma ba za ka iya samun wanda yake gwani a komai ba.


Don haka kada ka raba hankalinka tsakanin abubuwa guda biyu, ka dage akan abu guda ɗaya tukuna har ka samu ƙwarewa a cikinsa.


Ka yi watsi da duk wata shagala ka maida hankali akan manufarka.


B. Haƙuri da dagiya (Patience and Endurance).


Ka fito ka yi gwagwarmaya kuma a fafata da kai. Duk wani abin da kake so a rayuwa dole sai ka yi aiki za ka same shi.


Babu wanda zai ɗauko ya ba ka. Don haka kana buƙatar ka sadaukar domin cimma burinka.


Ba lallai ka samu lokacin fira da nishaɗi kamar sauran jama'a ba.


Za ka yi jinkirin barci amma za ka riga kowa tashi. Wannan ba sabon abu ba ne, ka saba da hakan.


C. Sarrafa kai (Self-discipline).


Dole ka ladabtar da kanka, kuma ka tarbiyantar da zuciyarka akan yin abin da ya dace a kowanne irin yanayi.


Ko kana so ko ba ka so, ka koyi aikata abin da ya dace a lokacin da ya kamata.


Watarana za ka ji ka babu kuzari, babu karsashi, ko ƙyuya da kasala su kama ka.


Idan ba ka da kanka akan jajircewa ba, zuciyarka sai ta rinjaye ka a irin wannan yanayin.


D. Maimaici (Consistency).


Hausawa suna cewa, zara ba ta barin dami kamar yadda sannu-sannu ba ya hana zuwa.


Da kaɗan da kaɗan ruwa ke cika tulu, kamar yadda da kaɗan da kaɗan ake samun nasara.


Don haka, sakamakon da kake fata zai samu ne kawai bayan tsawon lokaci.


Kana buƙatar gina ɗabi'a ta maimaici, ka zamo mai yin abu yau-da-kullum kafin nasara ta samu gare ka. Ginin yini/wuni ɗaya ba ya yin ɗaki.


Amma kuma duk garin da ruwa ke zuba, sai ya zama daji. Don haka daga nan har watanni 6 masu zuwa, ka yi wa kanka alƙawarin a kullum za ka aikata koda abu ɗaya da zai kusantar da kai ga burinka.


11. Ka kewaye kanka da masu ƙarfafa ka.


Zuwa yanzu ya kamata ka fahimci cewa muhallin da kake rayuwa a cikinsa da irin mutanen da kake ta’ammuli da su suna da gagarumin tasiri akan tunaninka da kuzarinka da aikin da za ka yi.


Don hakan idan kana so ka cimma manufarka, dole na farko, ka nisanta kanka da mutanen da suke kashe maka gwiwa akan mafarkanka da abokai waɗanda za su iya maida kai rijiya.


Sannan sai ka ƙulla alaƙa da mutane masu manufa irin naka don ku ƙarfafi junanku har ku yi nasara a tare.


Ka yi ƙoƙarin samun jagora (mentor) wanda zai riƙe hannuwanka ya nuna maka hanya sannan ya ba ka gudunmawa wurin cimma burinka.


Ka kasance a shirye don biyan kuɗi domin ka yi koyi daga ilimi da gogewar irin waɗannan mutanen da sun riga sun yi nasara kuma sun taki irin matakin da kake so ka taka a rayuwa. 


Wannan shi ne mataki na 11 kuma na ƙarshe cikin ƙa’idojin da zan kawo. Daga nan ka gama rusa duk wasu munanan halaye, da ɗabi’u da alaƙoƙi da ba sa taimakon ka akan burinka kuma ka iya gina sabbin halaye, ɗabi’u da alaƙoƙi masu matuƙar amfani da tasiri ga manufofinka da rayuwarka.


Wannan shi ne tsari na Rusau da Ginau da na ambata a baya.


Shawara ta ƙarshe


A nan zan so in rufe da maganar shahararren marubucin nan na ƙasar Masar wanda ya lashe kyautar Nobel, wato Najib Mahfuz.


Yana cewa: “Na koya daga rayuwa cewa burin mutum ba ya zuwa gare shi a kan farantin zinariya, amma yana samuwa ne tare da dogon yunƙuri da kuma kyakkyawan haƙuri.”


Wannan maganar tasa tana da zurfin ma'ana sosai. Abubuwa biyu take yi mana nuni akai, su ne muhimmancin yunƙuri da kuma haƙuri.


Wato duk abin da kake so a rayuwa, sai ka tashi tsaye ka yi fafutuka za ka same shi.


Idan ka zauna zaman jira babu wanda zai ɗauko wannan abin ya ba ka.


Sannan nasarar da kake nema ba za ta zo gare ka a dare ɗaya ba, dole sai ka ɗauki tsawon lokaci kana mai yunƙurawa tare da yin haƙuri.


A yayin da mafi akasarin jama'a suka kamu da son yin abubuwa a cikin gaggawa, ka tuna cewa haƙiƙanin ci-gaba yana faruwa ne bayan tsawon lokaci.


Ka yarda da nasara mai ɗorewa bisa neman sakamakon yanzu-yanzu ko aiki da gaggawa.


Kana buƙatar tazarar lokaci kafin ka iya aikata duk wani abu da na ambata a cikin wannan saƙon


Kana buƙatar tsawon lokaci da haƙuri kafin;


- Ka samu ilimi ko ƙwarewa akan wani abu.


- Ka iya haɓaka sana'arka ko kamfaninka.


- Ka tara dukiya ko ka bunƙasa kasuwancinka.


- Ka iya gina jikinka, da zuciyarka da tunaninka, da kuma aljihunka.


Duk wani abu mai ƙima a rayuwa ba ya samuwa sai da haƙuri, don haka ka tarbiyantar da zuciyarka akan haƙuri.


Duk mutumin da ya yi haƙuri to da sannu zai samu sakamakonsa koda ya yi jinkirin zuwa gare sa.


Duk wani abu mai kima a rayuwa ba ya samuwa sai da haƙuri, don haka ka tarbiyantar da zuciyarka akan haƙuri.


Duk mutumin da ya yi haƙuri to da sannu zai samu sakamakonsa koda ya yi jinkirin zuwa gare sa.


Ka tuna cewa tafiyar mil dubu tana farawa ne da taku ɗaya. Don haka ka ɗauki mataki na farko a yau, kuma nan da watanni 6 za ka gode wa kanka.


ƘARSHE 


Ga waɗanda ba su samu damar karantawa ba tun daga farko ba, to su kwantar da hankalin su, su latsa nan don komawa ga shafin farko na Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal  ko kuma nan....



Da wannan ne, muka kawo ƙarshen wannan muhimmin saƙon mai taken, "Yadda Za Ku Sauya Rayuwar Ku A Rabin Shekara Kacal.".


Ku kasance tare da mu a kullum don samun saƙonni da za su inganta rayuwarku a cikin harshen Hausa.


A ci-gaba da yaɗawa tare da ba mu gudummawa a wannan shafin. Muna matuƙar godiya.


Ku ci-gaba da bibiyar shafin nan namu domin ci-gaba da samun saƙonnin da za su taimaki rayuwar ku tare da  taimaka muku ga cimma burin ku da muradin ku cikin sauƙi duk a kyauta. Za ku iya sanar da sauran mutane sunan wannan shafin domin su ma su shigo su amfana kamar yadda ku ma kuke amfana.


Tushe/Asali:  Hausa Motivation

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user