Tuesday, 29 October 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Na Rubutu Masu Ratsa Ko'ina Na Cikin Jiki

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce macen da idan na tunata duk ƙuncina sai ya kwaranye, da hakan ne na ƙara tabbatar da cewan kin cancanci na kiraki da Autar Mata mai wuyar samu.


Kalaman Soyayya Na Rubutu Masu Ratsa Ko'ina Cikin Jiki
Hoto: Archmore business web

Marubuci:- Prince E


A duk lokacin da idanuwana suka yi arba da wannan kyakkyawar surar taki sai na dinga jin kaina tamkar ɗan sarkin da ya gaji sarautar mahaifinsa a daren farko.


Na kamu da matsananciyar ƙaunarki a zuciyata, gami da gagarumar gobarar son ki tamkar an jefa ma zuciyata bama-bamai.


Ke ce kaɗai za ki iya kashe mini wannan gobarar da ke ci a cikin kogon zuciyata.


Idan kika juya min baya to tabbas kuwa zuciyata za ta narke tamkar yadda kyandir/kendir ke narkewa yayinda aka saka masa wuta.


Dare da rana safe da yamma ke ce abar begena, ba ni da sukuni yayin da na tuna da kyakkyawar surarki da kyawawan ɗabi"unki.


Na kan kasance cikin farin ciki a duk lokacin da kunnuwana suke sauraron wannan tattausan lafuzan bakin naki.


Na kan ji tamkar a duk duniyar nan

babu wanda ya kai ni morewa rayuwar nan.


Kyawawan halayen ki da alkunyarki suke ƙara tunzura zuciyata zuwa farfajiyar daular fadar masarautar so da ƙaunarki.


Tabbas ki sani cewa kulawarki ita ce abar alfahari ga zuciyata tare da ruhina.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user