A rayuwa babu abin da ke tafiya kara zube dole ne ka yi amfani da tsare-tsare masu kyau da kuma hangen nesa domin ribatar damarmakin rayuwa ta yadda ya dace.
Abubuwa guda uku suna da matuƙar muhimmanci a cikin duk abin da mutum zai yi a rayuwa.
Idan ka yi riƙo da su za su taimake ka ƙwarai wajen samun ci-gaba da cimma manufofinka.
Hanyar tabbatar da tsari mai kyau shi ne ka rarraba burikan ka zuwa ƙananan taku, hakan zai taimake ka wurin ajiye kowanne abu a bigiren shi tare da samun ci gaba mai ɗorewa.
Ga su kamar haka:
1. Tsari da hangen nesa.
Duk abin da za ka yi ko za ka fara, ko ka daɗe kana yi, ana so ka zauna ka yi dogon tunani akai.
Ka yi tunani akan manufarka ta fara wannan abin, wasu damarmaki ne a ciki, kuma wasu haɗurra ne, sannan ta yaya za ka ribaci waɗannan damarmakin kuma ka ƙauracewa haɗurran da ke ciki.
Hakan shi zai ba ka damar aiki bisa ilimi da basira da hankali.
2. Neman shawara.
Abu na gaba shi ne neman ƙarin haske da shawarwari amma daga mutanen da suka cancanta.
Masu ilimi da shekaru da basira da sanin-ya-kamata, da kuma waɗanda suke da ƙwarewa da gogewa akan abin da kake yi.
Masu hikimar magana suna cewa Ɗan Adam tara yake bai cika goma ba. Kuma hakan ne.
Daɗin shawara shi ne ba'a yin sa a yi hasara/asara ko nadama. Idan ka yi shawara da mutane, ko dai su gaya maka abin da ba ka sani ba, su nuna maka abin da ba ka hango ba ko kuma su tabbatar maka da abin da ka riga ka sani.
3. Koyo daga Jagora.
Wannan shi ne na uku kuma shi ne mafi muhimmanci duk a cikinsu.
Jagora (wato Mentor) shi ne wanda zai nuna maka hanyar da ya kamata ka bi kuma ya tsamo ka a lokacin da ka shiga duhu.
Kana da damar tambayar sa idan ba ka gane ba ko ka nemi ƙarin bayani game da abin da ka shiga ruɗani akai.
Jagora shi ne Masani kuma Ƙwararren mai ilimi da gogewa akan abin da kake koyo.
Ana buƙatar jagora a kasuwanci, da noma da karatu, da siyasa, da Addini da dukkan al'amuran rayuwa.
Kuma a zamanin yau, jagoranka ba dole sai ya zamo wanda kuka san juna ko kuke a gari ɗaya ba.
Za ka iya samun jagora da bai taɓa sanin ka ba bare ma ku haɗu, albarkacin yanar gizo-gizo da shafukan sada zumunta kuka san juna.
Mabuɗin ilimi shi ne tambaya, don haka duk abin da za ka yi ka tabbatar ka tambayi masana su nuna maka hanya.
Sakamako mai kyau yana samuwa ne ta dalilin tsarawa cikin dabara da zartarwa cikin shiri. Duk abin da kake yi ka bada muhimmanci ga waɗannan biyun, dabaru suna taka rawa mai muhimmanci ga nasara.
Tushe/Asali: Hausa Motivation