Monday, 25 November 2024

Abubuwa 3 Masu Cutar Da Sana'a Da Hana Ta Ci-gaba

Tura Wannan Zuwa Ga

Abubuwa uku da idan ba ka daina yin su ba, sana'arka ba za ta ci gaba ba.


Ga su kamar haka:


1. Raina riba


Idan kana raina ribar da kake samu a cikin sana'arka hakan zai shafi mu'amalarka da masu maka ciniki, za su dinga ji kamar su kake rainawa, maimakon mu'amalantar abokin ciniki daidai da ribar da ya kawo, ka mu'amalance shi daidai da ribar da zai ci-gaba da kawowa nan gaba.


Abubuwa 3 Masu Cutar Da Sana'a Da Hana Ta Ci-gaba
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abubakar S. Wali


3. Raina abokin ciniki


Ka daina mu'amalantar mai ciniki kamar ba zai ba ka yanke talauci ba. Ka dinga ɗauka duk wani mai ciniki guda ɗaya kamar yana wakiltar sauran mutanen da suke maka ciniki ne ko za su maka a nan gaba, duk yadda mai ciniki yake da buƙatar abin da kake sayarwa matuƙar yana da zaɓin saya a wani waje ya cancanci ka girmama shi ka mutunta shi.


Kai koda ba shi da zaɓi ya cancanci a mutunta shi, saboda ya zaɓi ya mallaki abun nan ta kyakkyawar hanya (saya ba sata ba).


3. Raina sana'a


Daga lokacin da ka ji a ran ka ba za ka yi arziki a cikin sana'arka ba, ka kashe wannan sana'ar. Kuma ba za ka yi arzikin da ita ba saboda za ka fara tunani da aiwatar da sana'ar a tsiya ce. 


Idan sana'a ba ta bada abin da ake so, canjata ake ko a ɓullo mata ta wata hanyar amma ba a ci-gaba a sana'ar da aka yarda ba za a ci-gaba ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user