Friday 1 November 2024

Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (5)

Tura Wannan Zuwa Ga

Tamkar mai hauka haka Laila ta koma bayan da ta yi duk abin da za ta iya don ganin masoyin nata a farke, idanuwan Laila tuni sun ƙanƙance saboda tsabar kukan da ta ke yi.


Labarin Soyayyar Majnun Da Laila
Hoto: Kekisruhan

Marubuci:- Auwal Ilyas Adam


Cikin wata murya wadda kunne ba zai iya tantancewa ba ta fara rera wasu baitoci kamar haka:


Wanzuwata da numfashi na na gan ka a damana.


In ka bar ni anan duniyar ga wane ne gatana?


Yaka taso zo, ni ganin ka shi ne fatana.


Tana kaiwa ƙarshen baitocin sai ta ƙwala masa kira da ƙarfin gaske "Majnun!"


Can kuma a mahaɗar nan wadda daga nan ne za ka yi shirin shiga Habasha, wato inda iyayen Laila suka yada zango kenan, bayan iyayenta sun gama shiryawa tsaf sai mahaifiyarta ta duba ba ta gan taba, nan da nan ta sanarwa da mahaifinta halin da ake ciki, neman duniyar nan sun yi a wannan mahaɗar wadda take tamkar wani ɗan ƙaramin gari ne amma ba Laila ba alamarta, hankalin iyayenta ya tashi, anan wasu suka ba wa iyayen shawara akan su ƙarasa cikin Habashan ko wataƙila ta bi ayarin wasu gungun fataken ne.


Hakan kuwa akai wato iyayen Lailar suka amince da hakan, isar su Habashan keda wuya ba su zame ko ina ba sai fadar sarkin, a matsayinsu na su ma masu ƙaramar sarauta a masarautarsu, yayinda iyayen Laila suka labartawa sarkin Habasha labarin ɓatan 'yarsu da ma cikakken labarin Laila da Majnun ɗin, sai sarki da muƙarrabansa suka cika da mamaki yayin da wasu da yawansu suka ringa kuka saboda tausayin waɗannan masoyan, sarki ya haɗa wata tawaga ta mahaya ɗari ya ce su nufi can nahiyar da aka baro Majnun ɗin ko wata ƙila za'a gan ta a can wajensa, kuma ya ce musu idan sun gan su to su taho dasu gabaɗayansu zuwa fadarsa.


Gwauron numfashin da ya ja ne ya sa Laila ta karkato da hankalinta zuwa gare shi, tabbas Majnun ɗinta ne yake numfasawa, sannu a hankali ya buɗe idanunsa waɗanda ba sa iya buɗewa gabaɗaya saboda tsabar wahalar da Majnun ɗin ya sha, Laila ta dube shi cikin shashsheƙar kuka haɗe da dariya ta ce, "Majnun ni ce Lailarka, gani a tare da kai na dawo Majnun... Ba zan iya rayuwa ba ba tare da Majnun ɗina ba..." 


Duk da halin da yake ciki hakan bai hana bayyanar wani tattausan murmushi ba akan kumatunsa, cikin sanyin jiki ya lalubo hannun Laila ya matse shi gam a hannunsa tamkar yana tsoron kada wani abin ya zo ya kuma raba shi da Lailarsa.


DUBA WANNAN: KARANTA CIKAKKEN LABARIN SOYAYYAR LAILA MAJNUN 


Wata rana Majnun ya zo ya wuce ta gaban mai sallah yana begen Laila bayan mai sallah ya gama sai ya yi sauri ya sha gaban Majnun don ya ji dalilin da ya sa ya tsallaka mashi sallah?

 

Majnun ya dubi mai sallah ya ce


"Yaushe ka gan ni"


Mai sallah ya ce "Lokacin da nake sallah".


Majnunin Laila ya ce "Wallahi ina cikin begen Laila har na wuce ban gan ka ba, kuma Wallahi da soyayyar ka ga Allah ta kai kwatankwacin yadda nake son Laila to na tabbatar kai ma ba za ka gan ni ba.".


Ina jin anan zan tsaya da ba ku wannan ƙayataccen labarin.


Ku ci-gaba da kasancewa da ni domin jin wasu daɗaɗan labaran.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user