Friday, 29 November 2024

Babban Abin Da Ya Bambanta Ka Da Sauran Jama'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Mu 'yan adam an halicce mu da abin da Bature yake kira Uniqueness, ma'ana kowa yana da wani abu na musamman da ya bambanta shi da sauran mutane, hatta DNA da ake haifarmu da shi kowa yana zuwa da irin nasa shi kaɗai wanda ba a taɓa yin irinsa a baya ba kuma har duniya ta tashi ba za a sake maimaita irin sa ba.


Babban Abin Da Ya Bambanta Ka Da Sauran Jama'a
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abubakar S. Wali


A ɓangaren rayuwa kuma babu wanda yake da haƙiƙanin irin iyayen da kake da su, idan an samu wanda yake da iyaye irin naka kamar misali abokin haihuwa (ɗan uwa) za ka samu kuna da bambancin yadda kuka gudanar da rayuwarku a matakai daban-daban na girman ku.


Irin ƙuruciyar da ka yi ba irin ta wani ya yi ba, ko a lokacin da aka haifeka akwai bambanci da lokacin da aka haifi wani, da sauran abubuwa da yawa da za su iya bambanta yadda kuke kallon rayuwa da yadda wani yake kallon ta.


Manufar ita ce ka fahimci cewa ba kowacce rayuwa ba ce za ta iya zama rayuwarka, idan kana rayuwa da ɗabi'ar kwafi ko kwaikwayon rayuwar wasu ba za ka ci ribar wannan abu na musamman ɗin da Ubangiji ya halicce ka da shi ba tun farko.


Fahimtar abin da ya bambanta ka da mutane zai ba ka damar kai wa ƙololuwa akan duk abun da kake yi, babu wanda zai iya yin gasa da kai a cikin yin wannan abun, saboda babu wani irin ka sak, kai ɗaya ne an riga da an yi kuma ba za a sake maimaita wani kamar kai ba.


DUBA WANNANKaranta Ire-iren Baiwar Ɗan Adam 14 Masu Ban Mamaki


Mafi yawan lokaci dalilin da ya sa muke kasa kai wa labari a wani fanni na rayuwa saboda mun rasa fahimtar wannan abu na musamman ɗin da Allah ya mana ne, mu kan shafe rabin rayuwar mu cikin ƙoƙarin kwaikwayon wasu mutanen da ba za mu taɓa zama su ba har abada.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user